< Ayyukan Manzanni 11 >

1 Yanzu Manzani da 'yan'uwa wadanda suke cikin Yahudiya suka ji cewa al'ummai ma sun karbi maganar Allah
E ouviram os apóstolos, e os irmãos que estavam na Judeia, que também os gentios receberam a palavra de Deus.
2 Lokacin da Bitrus ya je Urushalima, wadanda suke na kaciya suka zarge shi;
E, subindo Pedro a Jerusalém, disputavam com ele os que eram da circuncisão,
3 suka ce, “Ka hada kai tare da mutane marasa kaciya kana ci tare da su!”
Dizendo: Entraste em casa de varões incircuncisos, e comeste com eles.
4 Amma Bitrus ya fara bayyana masu dalla-dalla; ya ce,
Mas Pedro começou a contar-lhes tudo por ordem, dizendo:
5 Ina addu'a a cikin birnin Yafa, sai na ga wahayi game da taska yana saukowa, kamar babban mayafi da aka saukar daga sama ta kusurwan nan hudu. Ya sauko gabana.
Estando eu orando na cidade de Joppe, vi, arrebatado dos sentidos, uma visão, um certo vaso, como um grande lençol que descia do céu e, baixado, vinha até junto de mim
6 Na zura masa ido kuma na yi tunani a kansa, na ga dabbobi masu kafa hudu na duniya, miyagun dabbobi, da masu rarrafe, da tsuntsayen sama.
No qual, pondo eu os olhos, considerei, e vi animais da terra, quadrúpedes, e feras, e réptis, e aves do céu.
7 Sai na ji murya tana ce da ni, “Tashi, Bitrus, yanka ka ci.”
E ouvi uma voz que me dizia: Levanta-te, Pedro; mata e come.
8 Na ce, “Ba haka ba, Ubangiji: gama babu abu mara tsarki ko mai kazanta da ya taba shiga bakina.”
Porém eu disse: De maneira nenhuma, Senhor; pois nunca em minha boca entrou coisa alguma comum ou imunda.
9 Amma murya ta amsa kuma daga sama cewa, “Abin da Allah ya kira mai tsarki, kada ka kira shi mara tsarki.”
Mas a voz respondeu-me do céu segunda vez: Não chames tu comum ao que Deus purificou.
10 Wannan ya faru sau uku, sai dukan komai ya koma sama.
E sucedeu isto por três vezes; e tudo tornou a recolher-se no céu.
11 Nan da nan sai ga mutane uku tsaye a gaban gidan da muke; an aike su daga Kaisariya zuwa gare ni.
E eis que, na mesma hora, pararam junto da casa em que eu estava três varões que me foram enviados de Cesareia.
12 Ruhun ya umurce ni in tafi tare da su, ba tare da nuna banbanci game da su ba. Yan'uwan nan shida sun tafi tare da ni, sai muka shiga gidan mutumin.
E disse-me o espírito que fosse com eles, não duvidando; e também estes seis irmãos foram comigo, e entramos em casa daquele varão;
13 Ya fada mana yadda ya ga mala'ika tsaye a cikin gidansa yana cewa “Aiki mutane zuwa Yafa, su kirawo Saminu wanda ake kira Bitrus.
E contou-nos como vira estar um anjo em sua casa, e lhe dissera: Envia varões a Joppe, e manda chamar a Simão, que tem por sobrenome Pedro,
14 Zai gaya maku sakon da za ku sami ceto kai da dukan gidanka.”
O qual te dirá palavras com que te salves, tu e toda a tua casa.
15 Da na fara magana da su, Ruhu Mai Tsarki ya sauko akansu kamar yadda ya sauko mana tun da farko.
E, quando comecei a falar, caiu sobre eles o Espírito Santo como também sobre nós ao princípio.
16 Sai na tuna da maganar Ubangiji, yadda ya ce,”Hakika Yahaya ya yi baptisma da ruwa, amma ku za a yi maku baptisma da Ruhu Mai Tsarki.”
E lembrei-me do dito do Senhor, quando disse: João certamente batizou com água: mas vós sereis batizados com o Espírito Santo.
17 To, idan Allah ya yi masu baiwa kamar yadda ya yi mana yayin da muka bada gaskiya ga Ubangiji Yesu Almasihu, wane ni da zan yi jayayya da Allah?
Portanto, se Deus lhes deu o mesmo dom que a nós, que também já havemos crido no Senhor Jesus Cristo, quem era então eu, para que pudesse estorvar a Deus?
18 Da suka ji wadannan abubuwa, suka rasa ta cewa, amma suka daukaka Allah suka ce “Ga al'ummai ma Allah ya basu tuba zuwa rai.”
E, ouvindo estas coisas, apaziguaram-se, e glorificaram a Deus, dizendo: De maneira que até aos gentios deu Deus o arrependimento para a vida.
19 Sai wadanda suka warwatsu saboda tsananin da ya bi bayan mutuwan Istifanas, suka yadu har zuwa Finikiya, Kuburus da Antakiya, amma suka yi wa'azin Yesu ga Yahudawa kadai.
E os que foram dispersos pela perseguição que sucedeu por causa de Estevão caminharam até à Fenícia, Chypre e Antiochia, não anunciando a ninguém a palavra, senão só aos judeus.
20 Amma wadan sunsu, mutane daga Kuburus da Kurane, suka zo Antakiya suka yi magana da hellenawa, suna yi masu wa'azin Ubangiji Yesu.
E havia entre eles alguns varões chyprios e cyrenenses, os quais, entrando em Antiochia, falaram aos gregos, anunciando o Senhor Jesus.
21 Kuma ikon Ubangiji yana tare da su, har mutane da yawa suka gaskata kuma suka juyo wurin Ubangiji.
E a mão do Senhor era com eles; e grande número creu e se converteu ao Senhor.
22 Labari game da su ya iso kunnen ikilisiya da ke Urushalima: sai suka aika da Barnaba zuwa can Antakiya.
E chegou a fama disto aos ouvidos da igreja que estava em Jerusalém; e enviaram Barnabé à Antiochia.
23 Da ya iso kuma ya ga kyautar Allah, sai ya yi farinciki; ya karfafa su dukka su kafu cikin Ubangiji da dukan zuciyar su.
O qual, quando chegou, e viu a graça de Deus, se alegrou, e exortou a todos a que permanecessem no Senhor com propósito do coração.
24 Domin shi mutumin kirki ne, cike kuma da Ruhu Mai Tsarki da bangaskiya, sai mutane da yawa suka karu ga Ubangiji.
Porque era homem de bem, e cheio do Espírito Santo e de fé. E muita gente se uniu ao Senhor.
25 Sai Barnaba ya tafi Tarsus domin ya nemi Shawulu.
E partiu Barnabé para Tarso, a buscar Saulo; e, achando-o, o conduziu para Antiochia.
26 Da ya same shi, ya kawo shi Antakiya. Ya kasance, shekara guda suna taruwa tare da ikilisiya suka koyar da mutane da yawa. A Antakiya ne aka fara kiran almajiran Krista.
E sucedeu que todo um ano se congregaram naquela igreja, e ensinaram muita gente; e em Antiochia foram os discípulos, pela primeira vez, chamados cristãos.
27 A cikin kwanakin nan wadansu annabawa daga Urushalima suka zo Antakiya.
E naqueles dias desceram profetas de Jerusalém para Antiochia.
28 Daya daga cikinsu, mai suna Agabas ya mike tsaye yayi magana da ikon Ruhu cewa za a yi tsanani fari ko'ina a duniya. Wannan ya faru ne a zamanin Kalaudiya.
E, levantando-se um deles, por nome Agabo, dava a entender, pelo espírito, que haveria uma grande fome em todo o mundo, a qual aconteceu no tempo de Claudio Cesar.
29 Sai, almajiran, suka dau niyya kowa gwargwadon karfinsa, su aika wa 'yan'uwa da ke Yahudiya da taimako.
E os discípulos determinaram mandar, cada um conforme o que pudesse, socorro para serviço dos irmãos que habitavam na Judeia.
30 Suka yi haka; sun aika wa dattawa da kudi ta hanun Barnaba da Shawulu.
O que eles com efeito fizeram, enviando-o aos anciãos por mão de Barnabé e de Saulo.

< Ayyukan Manzanni 11 >