< 3 Yohanna 1 >
1 Daga dattijon zuwa ga Gayus, wanda nake kauna da gaske.
Starší Gáiovi milému, kteréhož já miluji v pravdě.
2 Ya kaunatace na, ina addu'a domin ka samu albarka cikin kowanne al'amari, da kuma koshin lafiya, kamar yadda ruhun ka yake lafiya.
Nejmilejší, žádámť obzvláštně, abys se dobře měl a zdráv byl, tak jako duše tvá dobře se má.
3 Na yi farin ciki kwarai sa'adda wadansu 'yan'uwa suka zo suka ba da shaida a kan bangaskiyar ka, kamar yadda ka ke bin gaskiya.
Zradovalť jsem se zajisté velice, když přišli bratří a svědectví vydávali o tvé upřímnosti, vypravujíce, kterak ty v upřímnosti chodíš.
4 Ba abin da ya fi faranta mani rai kamar in ji yayana suna tafiya cikin gaskiya.
Nemámť větší radosti, nežli abych slyšel, že synové moji chodí v upřímnosti.
5 Ya kaunatace na, kana aiki da aminci zuwa ga 'yan'uwa da baki,
Nejmilejší, věrně děláš, cožkoli činíš bratřím a hostem,
6 wadanda suka shaida kaunar ka a gaban ikilisiya. Zai yi kyau ka yi masu taimako da kyakkyawar salama, ta hanyar da ta dace da masu ibada,
Kteřížto svědectví vydali o lásce tvé před církví. Kteréžto vyprovodíš-li, tak jakž sluší na Boha, dobře učiníš.
7 domin sabili da sunan nan ne suka fito, ba su kuma karbar kome a hannun al'ummai.
Neboť jsou pro jméno jeho vyšli, a nic nevzali od pohanů.
8 Don haka ya kamata mu karbi irin wadannan mutane, domin mu zama abokan aiki tare da su a kan gaskiya.
Mámeť tedy my takové přijímati, abychom byli pomocníci pravdy.
9 Na rubuta wasika zuwa ga ikilisiya, amma Diyotariffis, wanda ya fi kowa son girma a cikinsu, bai karbe mu ba.
Psal jsem sboru vašemu, ale Diotrefes, kterýž stojí o prvotnost mezi nimi, nepřijímá nás.
10 Saboda haka, idan na zo, zan tuna masa da irin ayukkan sa, da kuma yadda yake babbata sunayen mu a wurin jama'a da miyagun kalmomi. Wannan ma bai ishe shi ba, har ma yana kin karbar 'yan'uwa. Ya kuma hana wadanda suke son su yin hakan, harma ya kan kore su daga ikilisiya.
Protož přijdu-liť tam, připomenuť skutky jeho, kteréž činí, mluvě proti nám zlé řeči. A nemaje dosti na tom, i sám bratří nepřijímá, i těm, kteříž by přijímati chtěli, nedopouští, a ze sboru je vylučuje.
11 Ya kaunatace na, kada ka yi koyi da mugun abu, sai dai abu mai kyau. Dukan wanda yake yin abu mai kyau na Allah ne; mai aikata mugunta kuma bai san Allah ba.
Nejmilejší, nenásledujž zlého, ale dobrého. Kdož dobře činí, z Boha jest; ale kdož zle činí, nevidí Boha.
12 Dimitiriyas yana da kyakkyawar shaida a gun kowa har a wurin gaskiyar da kanta. Mu ma mun shaida shi, ka kuma san shaidar mu gaskiya ce.
Demetriovi svědectví vydáno jest ode všech, i od samé pravdy; ano i my svědectví o něm vydáváme, a víte, že svědectví naše pravé jest.
13 Ina da abubuwa dayawa da zan rubuta maka, amma ban so in rubuta maka su da alkalami da tawada ba.
Mnohoť jsem měl psáti, ale nechci psáti černidlem a pérem.
14 Ina sa zuciya mu sadu ba da dadewa ba, sa'annan mu yi magana ido da ido. Bari salama ta kasance tare da kai. Abokanmu suna gaishe ka, kuma ka isadda sakon gaisuwar mu ga sauran abokai da sunayen su.
Nebo mám naději, že tě tudíž uzřím, a ústy k ústům mluviti budeme. Pokoj budiž tobě. Pozdravují tě přátelé. Pozdraviž i ty dobrých přátel ze jména.