< 2 Timoti 3 >
1 Amma ka san da wannan: a cikin kwanakin karshe za a yi lokuta masu matsananciyar wahala.
2 Gama mutane za su zama masu son kansu, masu son kudi, masu Kumburi, da girman kai, masu sabo, marasa biyayya ga iyaye, marasa godiya, da kuma marasa tsarki.
3 Za su kasance marasa dabi'a, wadanda basu son jituwa da kowa, masu tsegumi, marasa kamun kai, 'yan tawaye, marasa kaunar nagarta.
4 Za su zama masu zagon kasa, taurin kai, masu takama, da masu kaunar anishuwa fiye da kaunar Allah.
5 Za su kasance da siffar ibada amma za su musunci ikonta. Ka juya daga wadannan mutanen.
6 A cikinsu akwai wadanda suke shiga gidaje suna yaudarar mataye marasa hikima. Wadannan ne mataye wadanda suke cike da zunubi, kuma sun kauce hanya sabili da sha'awoyi dabam daban.
7 Wadannan matayen suna ta koyo, amma ba za su taba kai wa ga sanin gaskiya ba.
8 Kamar yadda Yannisu da Yambrisu suka yi jayayya da Musa. Haka nan wadannan malaman karya kuma suke yin tsayayya da gaskiya. Mutane ne lalatattu a zuciya, marasa sahihiyar bangaskiya.
9 Amma ba za su yi nisa ba. Domin wautarsu za ta bayyana a fili ga kowa, kamar wadannan mutane.
10 Amma kai, ka bi koyarwata, da dabi'ata, nufe nufena, da bangaskiyata, da jimriyata, da kaunata, da hakurina,
11 da yawan kuncina, da wahalolina, da duk abubuwan da suka faru da ni a Antakiya, da Ikoniya da kuma Listra. Na jure a cikin kuncina. Amma a cikinsu dukka, Ubangiji ya cece ni.
12 Duk wadanda su ke so su yi rayuwa ta ibada a cikin Almasihu Yesu za su sha tsanani.
13 Miyagun mutane da masu hila za su yi ta kara lalacewa. Za su badda wasu. Su da kansu ma sun bijire.
14 Amma kai, ka ci gaba da abubuwan da ka koya kuma ka gaskata da zuciya daya. Ka san daga wurin wanda ka koya.
15 Ka san da cewa, tun kana dan karamin yaro ka san wadannan littattafai masu tsarki. Wadannan suna iya mai da kai mai hikima domin ceto ta wurin bangaskiya a cikin Almasihu Yesu.
16 Dukkan Nassi hurarre ne daga Allah. Yana da amfani domin koyarwa, domin tsautawa, domin gyara, kuma domin horarwa cikin adalci.
17 Wannan domin mutumin Allah ya zama cikakke ne, shiryayye domin dukkan ayyukan nagarta.