< 2 Timoti 2 >
1 Domin wannan kai, dana, ka karfafa cikin alherin da ke cikin Almasihu Yesu.
2 Abubuwan da ka ji daga gare ni a bainar jama'a masu yawa, ka danka su ga mutane masu aminci da za su iya koya wa wadansu kuma.
3 Ka daure shan tsanani tare da ni, kamar amintaccen sojan Almasihu Yesu.
4 Ba bu sojan da zai yi bauta yayin da ya nannade kansa da al'amuran wannan rayuwar, domin ya gamshi shugabansa.
5 Hakanan, idan wani yana gasa a matsayin dan wasa, ba zai sami rawani ba tukuna har sai in ya karasa tseren bisa ga ka'idodin gasar.
6 Wajibi ne manomi mai kwazon aiki ya fara karbar amfanin gonarsa.
7 Ka yi tunani game da abin da na ke gaya maka, gama Ubangiji zai ba ka ganewa a cikin komai.
8 Ka tuna da Yesu Almasihu, daga zuriyar Dauda, wanda a ka tayar daga matattu. Bisa ga wa'azin bisharata,
9 wanda na ke shan wahala har ya kai ga dauri kamar mai laifi. Amma maganar Allah ba a daure ta ba.
10 Saboda haka na jure wa dukkan abubuwa domin wadanda aka zaba, saboda su ma su sami ceton da ke cikin Almasihu Yesu, da daukaka madawwamiya. (aiōnios )
11 Wannan magana tabbatacciya ce: “Idan mun mutu tare da shi, za mu kuma rayu tare da shi.
12 Idan mun jure, zamu kuma yi mulki tare da shi. Idan mun yi musun sa, shi ma zai yi musun mu.
13 Idan mun zama marasa aminci, shi mai aminci ne koyaushe, domin shi ba zai yiwu ya musunta kansa ba.”
14 Ka yi ta tuna masu da wadannan abubuwan. Ka yi masu kashedi a gaban Allah kada su yi ta dauki ba dadi game da kalmomi. Saboda wannan bai da wani amfani. Domin wannan zai halakar da ma su sauraro.
15 Ka yi iyakacin kokarika domin ka mika kanka ma'aikacin Allah wanda aka tabbatar, wanda babu dalilin kunya a gareshi. Wanda ya ke koyar da kalmar gaskiya daidai.
16 Ka guje wa masu maganar sabo, wanda ya kan kara kaiwa ga rashin bin Allah.
17 Maganarsu za ta yadu kamar ciwon daji. Daga cikinsu akwai Himinayus da Filitus.
18 Wadannan mutanen sun kauce wa gaskiya. Sun fadi cewa an rigaya an yi tashin matattu. Suka birkitar da bangaskiyar wadansu.
19 Duk da haka, ginshikin Allah ya tabbata. Ya na da wannan hatimi: “Ubangiji ya san wadanda ke nasa,” Kuma “Duk mai kira bisa ga sunan Ubangiji dole ya rabu da rashin adalci.”
20 A gida mai wadata, ba kayayyaki na zinariya da azurfa ba ne kawai. Haka kuma akwai kayayyaki na itace da yunbu. Wadansu domin aikin mai daraja, wadansu kuma ga aiki mara daraja.
21 Idan wani ya tsarkake kansa daga rashin daraja, shi kayan aiki ne mai daraja. An kebe shi, abin aiki domin mai gidan, kuma a shirye domin kowanne aiki mai kyau.
22 Ka guje wa sha'awoyi na kuruciya, ka nemi adalci, bangaskiya, kauna da salama da wadanda suke kira ga sunan Ubangiji daga zuciya mai tsabta.
23 Amma ka ki tambayoyi na wauta da jahilci. Ka sani sukan haifar da gardandami.
24 Tilas bawan Ubangiji ya guje wa jayayya. A maimakon haka dole ya zama mai tawali'u ga kowa, mai iya koyarwa, kuma mai hakuri.
25 Dole ne ya koyarwa mutane da su ke jayayya da shi a cikin tawali'u. Watakila Allah ya ba su ikon tuba domin sanin gaskiyar.
26 Suna iya sake dawowa cikin hankalinsu kuma su bar tarkon Ibilis, bayan da ya cafke su domin nufinsa.