< 2 Tessalonikawa 2 >

1 Yanzu game da zuwan Ubangijinmu Yesu Almasihu da taruwarmu domin kasancewa tare da shi; muna rokonku yan'uwa,
Pour ce qui regarde l'avènement de notre Seigneur Jésus-Christ, et notre réunion avec lui,
2 kada kuyi saurin damuwa ko ku gigice saboda wani ruhu ko kuma sako ko kuma wasika da ta yi kamar daga wurin mu, da ke cewa ranar zuwan Ubangiji ta rigaya ta zo.
Nous vous prions, frères, de ne pas vous laisser ébranler facilement dans vos pensées, et de ne pas vous laisser troubler par quelque inspiration, ou par quelque parole, ou quelque lettre qu'on dirait venir de nous, comme si le jour de Christ était proche.
3 Kada wani ya yaudare ku ta kowace hanya. Domin wannan rana baza ta zo ba sai fandarewar nan ta zo kuma an bayyana mutumin tawayen nan wato dan hallaka.
Que personne ne vous séduise en aucune manière; car il faut que la révolte soit arrivée auparavant, et qu'on ait vu paraître l'homme du péché, le fils de la perdition,
4 Wannan shi ne wanda ya ke gaba, yana kuma daukaka kansa fiye da duk abin da ake kira Allah ko kuma ake bautawa. Sakamakon haka yana zama a kursiyin Allah har ma yana cewa shine Allah.
L'adversaire et celui qui s'élève au-dessus de tout ce qu'on appelle Dieu, ou qu'on adore, jusqu'à s'asseoir comme dieu dans le temple de Dieu, se proclamant lui-même dieu.
5 Baku tuna ba lokacin da nake tare daku na gaya maku wadannan abubuwa?
Ne vous souvient-il pas que je vous disais ces choses, lorsque j'étais encore avec vous?
6 Yanzu kun san abinda ke tsaida shi, domin a bayyana shi a lokacin da ya dace.
Et maintenant vous savez ce qui le retient, afin qu'il ne soit manifesté que dans son temps.
7 Ko yanzu asirin take shari'a ya na aiki, sai dai a kwai wanda ke tsaida shi yanzu har sai an dauke shi.
Car le mystère d'iniquité opère déjà; attendant seulement que celui qui le retient maintenant, soit enlevé.
8 Sa'anan za'a bayyana dan tawayen, wanda Ubangiji Yesu zai hallaka shi da numfashin bakinsa. Ubangiji zai mayar da shi ba kome ba ta wurin bayyanuwar zuwansa.
Et alors paraîtra l'impie, que le Seigneur détruira par le souffle de sa bouche, et qu'il anéantira par l'éclat de son avènement.
9 Mai tawayen nan kuwa, zai zo ne bisa ga aikin shaidan da dukan iko, alamu, da al'ajiban karya,
L'apparition de cet impie aura lieu avec la force de Satan, avec toute puissance, avec des prodiges et de faux miracles,
10 da kuma dukan yaudara ta rashin adalci. Wadannan abubuwa za su zama ga wadanda suke hallaka, saboda ba su karbi kaunar gaskiya ba domin su sami ceto.
Et avec toutes les séductions de l'iniquité parmi ceux qui se perdent, parce qu'ils n'ont point reçu l'amour de la vérité, pour être sauvés.
11 Saboda wannan dalilin Allah ya aiko masu da sabani, saboda su yarda da karya.
C'est pourquoi Dieu leur enverra un esprit efficace d'égarement, pour qu'ils croient au mensonge;
12 Sakamakon shine dukkan su za'a yi masu shari'a, wato wadanda ba su yarda da gaskiya ba suna kuma jin dadin rashin adalci.
Afin que tous ceux qui n'ont pas cru à la vérité, mais qui ont pris plaisir dans l'injustice, soient condamnés.
13 Amma muna masu godiya kulluyaumin ga Allah domin ku, yan'uwa wadanda Ubangiji yake kauna. Ubangiji ya zabe ku a matsayin yayan fari don ceto cikin tsarkakewar Ruhu da gaskatawa da gaskiya.
Mais pour nous, frères bien-aimés du Seigneur, nous devons rendre de continuelles actions de grâces à Dieu à cause de vous, de ce qu'il vous a choisis, dès le commencement, pour le salut, dans la sanctification de l'Esprit, et dans la foi en la vérité;
14 Wannan shine abinda ya kira ku gare shi ta wurin bishararmu domin ku sami daukakar Ubangijinmu Yesu Almasihu.
Il vous a appelés à cela par notre Évangile, pour que vous possédiez la gloire de notre Seigneur Jésus-Christ.
15 Saboda haka yan'uwa, ku tsaya da gaske. Ku rike al'adun da aka koya maku, ko ta kalma ko kuma ta wasikarmu.
C'est pourquoi, frères, demeurez fermes et retenez les enseignements que nous vous avons donnés, soit de vive voix, soit par notre lettre.
16 Yanzu bari Ubangiji Yesu Almasihu da kansa, da Allah Ubanmu wanda ya kaunace mu ya ba mu madawwamiyar ta'aziya da gabagadi mai kyau domin gaba ta wurin alheri, (aiōnios g166)
Or, que notre Seigneur Jésus-Christ lui-même, et Dieu notre Père, qui nous a aimés, et qui nous a donné dans sa grâce une consolation éternelle, et une bonne espérance, console vos cœurs, (aiōnios g166)
17 ya ta'azantar da ku ya kuma gina zuciyarku cikin kowane aiki mai kyau da kalma.
et vous affermisse en toute bonne doctrine et en toute bonne œuvre.

< 2 Tessalonikawa 2 >