< 2 Bitrus 2 >

1 Annabawan karya sun zo ga mutane, hakannan kuma malaman karya suma sun zo. A asirce za su zo maku da karkatacciyar koyarwa mai hallakarwa, su kuma yi musun sanin Ubangiji da ya fanshe su. Su na jawowa kansu hallaka da sauri.
But there were false prophets also among the people, even as there will be false teachers among you, who will privately bring in damnable heresies, even denying the Lord that bought them, and bring upon themselves swift destruction.
2 Da yawa za su bi gurbinsu, kuma ta wurinsu za a sabawa sahihiyar gaskiya.
And many will follow their pernicious ways; by reason of whom the way of truth will be evil spoken of.
3 Ta wurin hadama za su ribace ku ta wurin maganganunsu na yaudara. Hallakarsu ba za ta yi jinkiri ba; hukuncinsu na nan tafe.
And through covetousness they will with feigned words make merchandise of you: whose judgment now of a long time lingereth not, and their damnation slumbereth not.
4 Allah bai kebe mala'ikkun da suka yi zunubi ba. Maimakon haka ya tura su a cikin bakin duhun jahannama daure da sarkoki, har ya zuwa ranar shari'a. (Tartaroō g5020)
For if God spared not the angels that sinned, but cast [them] down to hell, and delivered [them] into chains of darkness, to be reserved to judgment; (Tartaroō g5020)
5 Hakan nan kuma bai kebe duniya ta zamanin da ba. Maimakon haka, ya kebe Nuhu, wanda yake wa'azin adalci, tare da mutane bakwai, lokacin da ya kawo ambaliyar ruwan Tsufana a fuskar duniyar marasa bin Allah.
And spared not the old world, but saved Noah the eighth [person], a preacher of righteousness, bringing the flood upon the world of the ungodly;
6 Sa'annan Allah ya kone biranen Sadoma da Gomrata da wuta ya maishe su toka, wannan ya zama misalin abin da zai faru da marasa ibada.
And turning the cities of Sodom and Gomorrah into ashes, condemned [them] with an overthrow, making [them] an example to those that afterwards should live ungodly lives.
7 Amma ga adalinnan Lutu, wanda ya zaku a ransa ta wurin miyagun halayen mutanen, Ubangiji kuwa ya cece shi.
And delivered just Lot, grieved with the habitual lewdness of the wicked:
8 Ga wannan mutum mai adalci, wanda yayi zama a cikinsu kowace rana ransa na baci, domin abin da yake gani yake kuma ji.
(For that righteous man dwelling among them, in seeing and hearing, grieved [his] righteous soul from day to day with [their] unlawful deeds; )
9 Saboda haka Allah ya san yadda zai ceci masu adalci daga gwaji, da yadda kuma zai kama masu rashin adalci da hukunci a ranar shari'a.
The Lord knoweth how to deliver the godly out of temptations, and to reserve the unjust to the day of judgment to be punished:
10 Wannan kuwa musamman gaskiya ce ga wadanda suka ci gaba da ayyuka na jiki suka kuma raina masu mulki. Suna da taurin kai da kuma yin ganin dama. Ba sa tsoron sabo ga wadanda aka daukaka.
But chiefly them that walk after the flesh in the lust of uncleanness, and despise government. Presumptuous [are they], self-willed; they are not afraid to speak evil of dignities.
11 Ko da shike mala'iku suna da karfi da iko fiye da su, amma basu kawo karar batanci a kansu a gaban Ubangiji ba.
Whereas angels, who are greater in power and might, bring not railing accusation against them before the Lord.
12 Amma wadannan dabbobi marassa tunani an yi su ne musamman domin a kama a yanka. Suna sabawa abin da ba su sani ba. Zasu halaka.
But these, as natural brute beasts, made to be taken and destroyed, speak evil of the things that they understand not; and shall utterly perish in their own corruption:
13 Za su sami sakamakon mugun aikinsu. Suna tunanin yin nishadi da rana abin annashuwa ne. Su kan su tababbu ne. Suna jin dadin ayyukansu na yaudara yayin da suke liyafa tare da ku.
And shall receive the reward of unrighteousness, [as] they that count it pleasure to riot in the day-time. Spots [they are] and blemishes, sporting themselves with their own deceivings while they feast with you;
14 Suna da idanun sha'awace sha'awacen mata mazinata; ba sa koshi da aikata zunubi. Suna rinjayar wandanda ba su da tsayayyan hankali zuwa ga munanan ayyuka, kuma sun kafa zukatansu ga hadama, su 'ya'yan la'ana ne!
Having eyes full of adultery, and that cannot cease from sin; beguiling unstable souls: they have a heart exercised with covetous practices; cursed children:
15 Sun bar bin hanyar gaskiya. Sun bijire kuma sun bi hanyar Bal'amu dan Be'or wanda yake kaunar ribar rashin adalci.
Who have forsaken the right way, and gone astray, following the way of Balaam [the son] of Bosor, who loved the wages of unrighteousness;
16 Amma ya karbi tsautawa domin zunubinsa. Jaki ma da baya magana ya tsauta wa haukan annabin da muryar dan adam.
But was rebuked for his iniquity: the dumb ass speaking with man's voice, forbad the madness of the prophet.
17 Wadannan mutane suna kamar mabulbullai da babu ruwa. suna nan kamar gizagizai da iska ke korawa. Duhu mai tsanani yana jiransu.
These are wells without water, clouds that are carried with a tempest; to whom the mist of darkness is reserved for ever. (questioned)
18 Su masu babatu ne da girman kai. suna yadaurar mutane ta wurin sha'awowin jiki. Suna yaudarar mutane da suke kokarin su tsere daga wadanda suke rayuwa cikin kuskure.
For when they speak great swelling [words] of vanity, they allure through the lusts of the flesh, [through much] wantonness, those that had quite escaped from them who live in error.
19 Suna masu alkawarin yanci, amma su da kan su bayi ne ga zunubi. Domin mutum bawa ne ga duk abinda ya rinjaye shi.
While they promise them liberty, they themselves are the servants of corruption: for by whom a man is overcome, by the same is he brought into bondage.
20 Duk wanda ya kubuta daga shashanci na duniya ta wurin sanin Ubangiji da mai Ceto Yesu Almasihu, sa'annan ya koma cikin shashaci, yanayinsu na karshe ya zama da muni fiye da na farkon.
For if after they have escaped the pollutions of the world through the knowledge of the Lord and Savior Jesus Christ, they are again entangled in them, and overcome, the latter end is worse with them than the beginning.
21 Da ma zai fi masu kada su san hanyar adalci da su san ta amma sa'annan su juya daga ka'ida mai tsarki wanda aka damka masu.
For it had been better for them not to have known the way of righteousness, than, after they have known [it], to turn from the holy commandment delivered to them.
22 Wannan karin magana ya zama gaskiya a kan su: “Kare ya dawo yana lashe amansa. Aladen da akayi masa wanka ya koma cikin tabo.”
But it hath happened to them according to the true proverb, The dog [is] turned to his own vomit again; and, The sow that was washed, to her wallowing in the mire.

< 2 Bitrus 2 >