< 2 Bitrus 1 >
1 Siman Bitrus, bawa da manzon Almasihu Yesu, zuwa ga wadanda suka karbi bangaskiya mai daraja kamar yadda muka karba, bangaskiya cikin adalcin Allahnmu da Yesu Almasihu.
Συμεὼν Πέτρος, δοῦλος καὶ ἀπόστολος Ἰησοῦ Χριστοῦ, τοῖς ἰσότιμον ἡμῖν λαχοῦσι πίστιν ἐν δικαιοσύνῃ τοῦ Θεοῦ ἡμῶν καὶ σωτῆρος Ἰησοῦ Χριστοῦ·
2 Bari alheri ya kasance tare da ku; bari salama ta karu ta wurin sanin Allah da na Yesu Ubangijinmu.
χάρις ὑμῖν καὶ εἰρήνη πληθυνθείη ἐν ἐπιγνώσει τοῦ Θεοῦ καὶ Ἰησοῦ τοῦ Κυρίου ἡμῶν.
3 Dukkan abubuwan ikon Allah na rayuwa da Allahntaka an bamu su ta wurin sanin Allah, wanda ya kira mu ta wurin daukakarsa da nagarta.
Ὡς πάντα ἡμῖν τῆς θείας δυνάμεως αὐτοῦ τὰ πρὸς ζωὴν καὶ εὐσέβειαν δεδωρημένης διὰ τῆς ἐπιγνώσεως τοῦ καλέσαντος ἡμᾶς διὰ δόξης καὶ ἀρετῆς,
4 Ta wurin wanan, ya bamu babban alkawari mai daraja. Yayi wanan ne saboda ku zama masu rabo cikin Allahntaka, yayin da ku ka kubuta daga lalacewa da ke cikin duniya saboda mugayen sha'awace sha, awace.
δι᾽ ὧν τὰ τίμια ἡμῖν καὶ μέγιστα ἐπαγγέλματα δεδώρηται, ἵνα διὰ τούτων γένησθε θείας κοινωνοὶ φύσεως ἀποφυγόντες τῆς ἐν κόσμῳ ἐν ἐπιθυμίᾳ φθορᾶς.
5 Saboda wanan dalilin kuyi iyakacin kokarinku ku kara nagarta ta wurin bangaskiyarku, kuma ta wurin adalci, sani.
καὶ αὐτὸ τοῦτο δὲ σπουδὴν πᾶσαν παρεισενέγκαντες ἐπιχορηγήσατε ἐν τῇ πίστει ὑμῶν τὴν ἀρετήν, ἐν δὲ τῇ ἀρετῇ τὴν γνῶσιν,
6 Ta wurin sani ku kara da kamun kai, kuma ta wurin kamun kanku, ku kara da jimrewa, ta wurin jimrewarku, ku kara da bin Allah.
ἐν δὲ τῇ γνώσει τὴν ἐγκράτειαν, ἐν δὲ τῇ ἐγκρατείᾳ τὴν ὑπομονήν, ἐν δὲ τῇ ὑπομονῇ τὴν εὐσέβειαν,
7 Ta wurin bin Allah, ku kara da kauna irin ta 'yan'uwa, ta wurin kauna irin ta 'yan'uwa, ku kara kauna.
ἐν δὲ τῇ εὐσεβείᾳ τὴν φιλαδελφίαν, ἐν δὲ τῇ φιλαδελφίᾳ τὴν ἀγάπην.
8 Idan wadannan abubuwan suna cikinku, kuma suka yi girma a cikinku, baza a sami bakarare ko rashin 'ya'ya cikin sanin Ubangijinmu Yesu Almasihu ba.
ταῦτα γὰρ ὑμῖν ὑπάρχοντα καὶ πλεονάζοντα οὐκ ἀργοὺς οὐδὲ ἀκάρπους καθίστησιν εἰς τὴν τοῦ Κυρίου ἡμῶν Ἰησοῦ Χριστοῦ ἐπίγνωσιν·
9 Amma duk wanda ya rasa wadannan abubuwan yana kallon abin da ke kusa ne kawai; ya makance. Ya manta da cewa an wake shi daga tsofaffin zunubansa.
ᾧ γὰρ μὴ πάρεστι ταῦτα, τυφλός ἐστι, μυωπάζων, λήθην λαβὼν τοῦ καθαρισμοῦ τῶν πάλαι αὐτοῦ ἁμαρτιῶν.
10 Saboda haka, 'yan'uwa, kuyi iyakacin kokari ku tabbatar da kiranku da zabenku. Idan kun yi wadannan abubuwan, baza ku yi tuntube ba.
διὸ μᾶλλον, ἀδελφοί, σπουδάσατε βεβαίαν ὑμῶν τὴν κλῆσιν καὶ ἐκλογὴν ποιεῖσθαι· ταῦτα γὰρ ποιοῦντες οὐ μὴ πταίσητέ ποτε.
11 Ta haka zaku sami shiga cikin mulki na har'abada na Ubangijinmu da Maicetonmu Yesu Almasihu. (aiōnios )
οὕτω γὰρ πλουσίως ἐπιχορηγηθήσεται ὑμῖν ἡ εἴσοδος εἰς τὴν αἰώνιον βασιλείαν τοῦ Κυρίου ἡμῶν καὶ σωτῆρος Ἰησοῦ Χριστοῦ. (aiōnios )
12 Saboda haka a shirye nake kulayomi in tunashe ku game da wadannan abubuwan, ko da yake kun san su, kuma kun yi karfi cikin gaskiya yanzu.
Διὸ οὐκ ἀμελήσω ἀεὶ ὑμᾶς ὑπομιμνήσκειν περὶ τούτων, καίπερ εἰδότας καὶ ἐστηριγμένους ἐν τῇ παρούσῃ ἀληθείᾳ.
13 Ina tunani daidai ne in zuga ku da tuni game da wadannan abubuwan, tun ina cikin wannan jiki.
δίκαιον δὲ ἡγοῦμαι, ἐφ᾽ ὅσον εἰμὶ ἐν τούτῳ τῷ σκηνώματι, διεγείρειν ὑμᾶς ἐν ὑπομνήσει,
14 Domin na sani jim kadan zan bar wannan jiki, kamar yadda Yesu Almasihu ya nuna mani.
εἰδὼς ὅτι ταχινή ἐστιν ἡ ἀπόθεσις τοῦ σκηνώματός μου, καθὼς καὶ ὁ Κύριος ἡμῶν Ἰησοῦς Χριστὸς ἐδήλωσέ μοι.
15 Zan yi iyakancin kokarina kulayomi domin ku rika tunawa da abubuwan, bayan kaurata.
σπουδάσω δὲ καὶ ἑκάστοτε ἔχειν ὑμᾶς μετὰ τὴν ἐμὴν ἔξοδον τὴν τούτων μνήμην ποιεῖσθαι.
16 Domin bamu bi labaru da aka kago na nuna wayo cikinsu ba, da muka fada maku game da iko da bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Almasihu, amma mu shaidu ne na ikonsa.
Οὐ γὰρ σεσοφισμένοις μύθοις ἐξακολουθήσαντες ἐγνωρίσαμεν ὑμῖν τὴν τοῦ Κυρίου ἡμῶν Ἰησοῦ Χριστοῦ δύναμιν καὶ παρουσίαν, ἀλλ᾽ ἐπόπται γενηθέντες τῆς ἐκείνου μεγαλειότητος.
17 Gama ya karbi daukaka da daraja daga wurin Allah Uba lokacin da murya ta zo daga ikon mai daukaka cewa, “Wannan shine dana, kaunataccena, wanda nake jin dadinsa kwarai.”
λαβὼν γὰρ παρὰ Θεοῦ πατρὸς τιμὴν καὶ δόξαν φωνῆς ἐνεχθείσης αὐτῷ τοιᾶσδε ὑπὸ τῆς μεγαλοπρεποῦς δόξης, οὗτός ἐστιν ὁ υἱός μου ὁ ἀγαπητός, εἰς ὃν ἐγὼ εὐδόκησα, —
18 Mun ji muryar nan da ta zo daga sama, lokacin da mu ke tare da shi a dutse mai tsarki.
καὶ ταύτην τὴν φωνὴν ἡμεῖς ἠκούσαμεν ἐξ οὐρανοῦ ἐνεχθεῖσαν, σὺν αὐτῷ ὄντες ἐν τῷ ὄρει τῷ ἁγίῳ.
19 Muna da wannan kalmar annabci wanda akwai tabbaci sosai, kun yi daidai idan kun mayar da hankali a kansu. Yana nan kamar fitillar da take walkiya a wuri mai duhu kafin asubahi ya zo, kuma tauraron asubahi ya tashi cikin zukatanku.
καὶ ἔχομεν βεβαιότερον τὸν προφητικὸν λόγον, ᾧ καλῶς ποιεῖτε προσέχοντες ὡς λύχνῳ φαίνοντι ἐν αὐχμηρῷ τόπῳ, ἕως οὗ ἡμέρα διαυγάσῃ καὶ φωσφόρος ἀνατείλῃ ἐν ταῖς καρδίαις ὑμῶν,
20 Ku san da wannan tun da farko, cewa babu annabci da ke bisa ga fasarar mutum.
τοῦτο πρῶτον γινώσκοντες, ὅτι πᾶσα προφητεία γραφῆς ἰδίας ἐπιλύσεως οὐ γίνεται.
21 Domin babu annabcin da ya taba zuwa ta wurin nufin mutum. Maimakon haka, Ruhu Mai Tsarki ne ke iza su, su fadi maganar Allah.
οὐ γὰρ θελήματι ἀνθρώπου ἠνέχθη ποτὲ προφητεία, ἀλλ᾽ ὑπὸ Πνεύματος Ἁγίου φερόμενοι ἐλάλησαν ἅγιοι Θεοῦ ἄνθρωποι.