< 2 Korintiyawa 7 >
1 Kaunatattu, da shike muna da wadannan alkawura, bari mu tsaftace kanmu, daga dukan abubuwan da ke kazantar da jikinmu da ruhunmu. Bari mu bidi tsarki cikin tsoron Allah.
ταύτας οὖν ἔχοντες τὰς ἐπαγγελίας, ἀγαπητοί, καθαρίσωμεν ἑαυτοὺς ἀπὸ παντὸς μολυσμοῦ σαρκὸς καὶ πνεύματος, ἐπιτελοῦντες ἁγιωσύνην ἐν φόβῳ θεοῦ.
2 Ku ba mu dama! Bamu bata wa kowa rai ba. Ba mu cutar da kowa ko mu zambaci kowa ba.
Χωρήσατε ἡμᾶς· οὐδένα ἠδικήσαμεν, οὐδένα ἐφθείραμεν, οὐδένα ἐπλεονεκτήσαμεν.
3 Ba domin in kayar da ku na fadi haka ba. Domin kuwa na riga na fada muku, cewa kuna zuciyar mu, domin mu mutu tare mu kuma rayu tare.
⸂πρὸς κατάκρισιν οὐ λέγω, προείρηκα γὰρ ὅτι ἐν ταῖς καρδίαις ἡμῶν ἐστε εἰς τὸ συναποθανεῖν καὶ συζῆν.
4 Ina da muhimmin gabagadi a cikin ku, Ina fahariya da ku. Ina cike da ta'aziya. Farincikina ya cika makil duk da wahalhalunmu.
πολλή μοι παρρησία πρὸς ὑμᾶς, πολλή μοι καύχησις ὑπὲρ ὑμῶν· πεπλήρωμαι τῇ παρακλήσει, ὑπερπερισσεύομαι τῇ χαρᾷ ἐπὶ πάσῃ τῇ θλίψει ἡμῶν.
5 Yayin da muka zo Makidoniya, jikinmu bai samu hutu ba. A maimakon haka, mun shiga matsaloli ta ko wace hanya ta wurin tashin hankali a waje tsoro kuma a ciki.
Καὶ γὰρ ἐλθόντων ἡμῶν εἰς Μακεδονίαν οὐδεμίαν ⸀ἔσχηκενἄνεσιν ἡ σὰρξ ἡμῶν, ἀλλʼ ἐν παντὶ θλιβόμενοι— ἔξωθεν μάχαι, ἔσωθεν φόβοι—
6 Amma Allah, mai ta'azantar da raunana, ya ta'azantar da mu ta wurin zuwan Titus.
ἀλλʼ ὁ παρακαλῶν τοὺς ταπεινοὺς παρεκάλεσεν ἡμᾶς ὁ θεὸς ἐν τῇ παρουσίᾳ Τίτου·
7 Ba ta wurin isowar sa kadai Allah ya yi mana ta'aziyya ba. Amma kuma ta wurin ta'aziyyar da Titus ya samu daga wurin ku. Ya gaya mana irin matsananciyar kaunarku, bakincikinku, da zurfin kulawarku a kaina. Na kuwa yi farinciki sosai.
οὐ μόνον δὲ ἐν τῇ παρουσίᾳ αὐτοῦ, ἀλλὰ καὶ ἐν τῇ παρακλήσει ᾗ παρεκλήθη ἐφʼ ὑμῖν, ἀναγγέλλων ἡμῖν τὴν ὑμῶν ἐπιπόθησιν, τὸν ὑμῶν ὀδυρμόν, τὸν ὑμῶν ζῆλον ὑπὲρ ἐμοῦ, ὥστε με μᾶλλον χαρῆναι.
8 Kodashike wasikata, ta bata maku rai, ban yi da na sanin haka ba. Amma sa'adda na ga wasika ta ta bata maku rai, na yi da na sani. Sai dai bacin ranku, na dan lokaci ne.
ὅτι εἰ καὶ ἐλύπησα ὑμᾶς ἐν τῇ ἐπιστολῇ, οὐ μεταμέλομαι· εἰ καὶ μετεμελόμην (⸀βλέπωὅτι ἡ ἐπιστολὴ ἐκείνη εἰ καὶ πρὸς ὥραν ἐλύπησεν ὑμᾶς),
9 Yanzu kuwa, ina farinciki, ba domin bacin ranku ba, amma domin bacin ranku ya kawo ku ga tuba, kun fuskanci bakinciki na ibada, donhaka ba ku yi rashi ba sabili da mu.
νῦν χαίρω, οὐχ ὅτι ἐλυπήθητε, ἀλλʼ ὅτι ἐλυπήθητε εἰς μετάνοιαν, ἐλυπήθητε γὰρ κατὰ θεόν, ἵνα ἐν μηδενὶ ζημιωθῆτε ἐξ ἡμῶν.
10 Domin bakinciki daga Allah ya kan kai ga tuba da ke kammala ceto ba tare da-da na sani ba. Bakinciki na duniya kuwa ya kan kai ga mutuwa.
ἡ γὰρ κατὰ θεὸν λύπη μετάνοιαν εἰς σωτηρίαν ἀμεταμέλητον ⸀ἐργάζεται ἡ δὲ τοῦ κόσμου λύπη θάνατον κατεργάζεται.
11 Ku dubi irin kyakkyawar niyya da bakincikin nan daga Allah ya haifar a cikin ku. Ina misalin girman niyyar nan taku ta nuna cewa baku da laifi. Ina misalin girman fushinku, tsoronku, da sa zuciyarku, himmar ku, da marmarin ku na ganin cewa an yi adalci! A cikin komai, kun nuna kanku marasa laifi a cikin wannan al'amari.
ἰδοὺ γὰρ αὐτὸ τοῦτο τὸ κατὰ θεὸν ⸀λυπηθῆναιπόσην κατειργάσατο ὑμῖν σπουδήν, ἀλλὰ ἀπολογίαν, ἀλλὰ ἀγανάκτησιν, ἀλλὰ φόβον, ἀλλὰ ἐπιπόθησιν, ἀλλὰ ζῆλον, ἀλλὰ ἐκδίκησιν· ἐν παντὶ συνεστήσατε ἑαυτοὺς ἁγνοὺς ⸀εἶναιτῷ πράγματι.
12 Kodayake na rubuto maku, ban rubuto saboda mai laifin ba, ko kuma saboda wanda aka yi wa laifin. Na rubuto ne domin himmarku gare mu ta sanu gare ku a gaban Allah.
ἄρα εἰ καὶ ἔγραψα ὑμῖν, οὐχ ⸀ἕνεκεντοῦ ἀδικήσαντος, ⸀οὐδὲ⸁ἕνεκεντοῦ ἀδικηθέντος, ἀλλʼ ⸀1ἕνεκεντοῦ φανερωθῆναι τὴν σπουδὴν ὑμῶν τὴν ὑπὲρ ἡμῶν πρὸς ὑμᾶς ἐνώπιον τοῦ θεοῦ.
13 Dalilin haka ne muka samu karfafawa. Baya ga ta'aziyyar mu, mun kuma yi murna sosai saboda farin cikin Titus, domin ruhunsa ya wartsake ta wurin ku duka.
διὰ τοῦτο παρακεκλήμεθα. Ἐπὶ δὲ τῇ παρακλήσει ⸀ἡμῶν περισσοτέρως μᾶλλον ἐχάρημεν ἐπὶ τῇ χαρᾷ Τίτου, ὅτι ἀναπέπαυται τὸ πνεῦμα αὐτοῦ ἀπὸ πάντων ὑμῶν·
14 Domin kuwa idan na yi fahariya da ku a gaban sa, ban ji kunya ba. A sabanin haka, kamar yadda kowane abu da muka fada maku gaskiya ne, fahariyarmu a kan ku ga Titus ta zama gaskiya.
ὅτι εἴ τι αὐτῷ ὑπὲρ ὑμῶν κεκαύχημαι, οὐ κατῃσχύνθην, ἀλλʼ ὡς πάντα ἐν ἀληθείᾳ ἐλαλήσαμεν ὑμῖν, οὕτως καὶ ἡ καύχησις ἡμῶν ⸀ἡ ἐπὶ Τίτου ἀλήθεια ἐγενήθη.
15 Kaunarsa a gare ku tana da girma, kamar yadda ya rika tunawa da biyayyarku duka, yadda kuka karbe shi da tsoro da rawar jiki.
καὶ τὰ σπλάγχνα αὐτοῦ περισσοτέρως εἰς ὑμᾶς ἐστιν ἀναμιμνῃσκομένου τὴν πάντων ὑμῶν ὑπακοήν, ὡς μετὰ φόβου καὶ τρόμου ἐδέξασθε αὐτόν.
16 Ina farinciki matuka domin ina da cikakken gabagadi a cikin ku.
χαίρω ὅτι ἐν παντὶ θαρρῶ ἐν ὑμῖν.