< 2 Korintiyawa 4 >

1 Don haka, domin muna da wannan hidima, da kuma yadda muka karbi jinkai, ba mu karaya ba.
Зато имајући ову службу као што бисмо помиловани, не досађује нам се;
2 Maimakon haka, sai muka rabu da dukan hanyoyin da ke na kunya, kuma na boye. Ba mu rayuwar makirci, kuma bamu yiwa maganar Allah rikon sakaci. Ta wurin gabatar da gaskiya, muna mika kanmu ga lamirin kowa a gaban Allah.
Него се одрекосмо тајног срама да не живимо у лукавству, нити да изврћемо реч Божију, него јављањем истине да се покажемо свакој савести човечијој пред Богом.
3 Amma, idan bishararmu a rufe take, tana rufe ne ga wadanda ke hallaka.
Ако ли је пак покривено јеванђеље наше у онима је покривено који гину,
4 A al'amarinsu, allahn wannan duniya ya makantar da zukatansu marasa bada gaskiya. A sakamakon haka, ba su iya ganin hasken bisharar daukakar Almasihu ba, wanda shine surar Allah. (aiōn g165)
У којима бог света овог ослепи разуме неверника, да им не засветли видело јеванђеља славе Христове, који је обличје Бога, који се не види. (aiōn g165)
5 Gama ba mu yin shelar kanmu, amma Almasihu Yesu a matsayin Ubangiji, mu kuma bayinku saboda Yesu.
Јер себе не проповедамо него Христа Исуса Господа, а себе саме ваше слуге Исуса Господа ради.
6 Gama Allah shine wanda ya ce, “Haske zai haskaka daga cikin duhu.” Ya haskaka cikin zukatanmu don ya bada hasken sanin daukakar Allah a gaban Yesu Almasihu.
Јер Бог који рече да из таме засветли видело, засветли у срцима нашим на светлост познања славе Божије у лицу Исуса Христа.
7 Amma muna da wannan dukiya a randunan yunbu, yadda zai zama a bayyane cewa mafi girman iko na Allah ne ba namu ba.
Али ово благо имамо у земљаним судовима, да премноштво силе буде од Бога, а не од нас.
8 Muna shan tsanani ta kowace hanya, ba a ci mu dungum ba. Mun rikice amma ba mu karaya ba, an tsananta mana amma ba a watsar da mu ba.
У свему имамо невоље, али нам се не досађује; збуњени смо, али не губимо наду;
9 Ana tsananta mana amma ba a yashe mu ba. Aka doddoke mu amma ba mu lalace ba.
Прогоне нас, али нисмо остављени; обаљују нас, али не гинемо.
10 Mu dai a kullayaumin muna dauke da mutuwar Yesu a jikkunanmu, saboda a bayyana rayuwar Yesu a jikkunanmu kuma.
И једнако носимо на телу смрт Господа Исуса, да се и живот Исусов на телу нашем покаже.
11 Mu da muke a raye kuwa a kulluyaumin ana mika mu ga mutuwa saboda Yesu, domin rayuwar Yesu ta zama a bayyane a jikunanmu na mutuntaka.
Јер ми живи једнако се предајемо на смрт за Исуса, да се и живот Исусов јави на смртном телу нашем.
12 Saboda haka, mutuwa tana aiki a cikinmu, amma rai na aiki a cikinku.
Зато дакле смрт влада у нама, а живот у вама.
13 Amma dai muna da wannan Ruhu na bangaskiya kammar yadda aka rubuta: “Na gaskata, saboda haka na furta.” Mu ma mun gaskata, haka kuwa muke fada.
Имајући пак онај исти дух вере као што је написано: веровах, зато говорих; ми верујемо, зато и говоримо.
14 Mun sani cewa wanda ya tada Ubangiji Yesu daga matattu za ya sake tada mu tare da Yesu. Mun san cewa zai gabatar da mu tare da ku a gabansa.
Знајући да ће Онај који подиже Исуса, и нас подигнути с Исусом, и поставити с вама.
15 Dukan abubuwa sabili da ku suke domin, yayin da aka baza alheri ga mutane dayawa, bada godiya ta karu ga daukakar Allah.
Јер је све вас ради, да благодат умножена изобилује хвалама на славу Божију.
16 Don haka ba mu karaya ba. Kodashike daga waje muna lalacewa, daga ciki ana sabunta mu kulluyaumin.
Зато нам се не досађује; но ако се наш спољашњи човек и распада, али се унутрашњи обнавља сваки дан.
17 Domin wannan 'yar wahala ta dan lokaci tana shirya mu zuwa ga nauyin madauwamiyar daukaka wadda ta wuce gaban aunawa. (aiōnios g166)
Јер наша лака садашња брига доноси нам вечну и од свега претежнију славу. (aiōnios g166)
18 Domin ba muna kallon abubuwan da ake gani bane, amma abubuwan da ba a gani. Abubuwan da muke iya gani ba masu dawwama ba ne, amma abubuwan da ba a gani madawwama ne. (aiōnios g166)
Нама који не гледамо на ово што се види, него на оно што се не види; јер је ово што се види, за време, а оно што се не види, вечно. (aiōnios g166)

< 2 Korintiyawa 4 >