< 2 Korintiyawa 2 >

1 Don haka na yanke shawara daga bangarena, ba zan sake zuwa wurin ku cikin yanayi mai tsanani ba.
Men jeg beslutte dette hos mig selv, at jeg vilde ikke atter komme til eder med Bedrøvelse.
2 Idan na bata maku rai, wa zai karfafa ni, in ba shi wanda na bata wa rai ba?
Thi dersom jeg bedrøver eder, hvem er da den, som gør mig glad, uden den, som bedrøves af mig?
3 Na rubuto maku kamar yadda na yi domin idan na zo gareku kada in sami bacin rai a wurin wadanda ya kamata su faranta mani rai. Ina da gabagadi game da dukan ku, cewa farincikin da nake da shi, shine kuke da shi duka.
Og jeg skrev netop derfor, for at jeg ikke, når jeg kom, skulde have Bedrøvelse af dem, som jeg burde have Glæde af, idet jeg havde den Tillid til eder alle, at min Glæde deles af eder alle.
4 Domin kuwa na rubuto maku cikin kunci da bacin rai da kuma hawaye mai yawa. Ba zan so in sake bata maku rai ba. Maimakon haka, na so ku san zurfin kaunar da nake da ita domin ku.
Thi ud af stor Hjertets Trængsel og Beklemthed skrev jeg eder til, under mange Tårer, ikke for at I skulde blive bedrøvede, men for at I skulde kende den Kærlighed, som jeg har særlig til eder.
5 Idan wani ya kawo sanadin bacin rai, ba ni kadai ya kawo wa wannan abin ba, amma ta wani fannin- domin kada a tsananta- har a gare ku duka.
Men dersom nogen har voldt Bedrøvelse, har han ikke bedrøvet mig, men til Dels, for ikke at sige det hårdere, eder alle.
6 Hukuncin nan da galibinku kuka yi wa mutumin nan ya isa.
Det er nok for ham med denne Straf, som han har fået af de fleste,
7 Don haka, yanzu a maimakon hukunci, ku gafarta masa, ku kuma ta'azantar da shi. Ku yi haka domin kada bakinciki mai yawa ya danne shi.
så at I tværtimod snarere skulle tilgive og trøste ham, for at han ikke skal drukne i den alt for store Bedrøvelse.
8 Don haka ina karfafa ku da ku nuna irin kaunar da kuke yi masa a fili.
Derfor formaner jeg eder til at vedtage at vise ham Kærlighed.
9 Wannan shine dalilin da ya sa na rubuto maku, domin in gwada ku, ko kuna biyayya cikin komai.
Det var nemlig også derfor, at jeg skrev, for at erfare, hvor vidt I stå Prøve, om I ere lydige i alt.
10 Duk mutumin da kuka gafarta wa, ni ma na gafarta masa. Abin da na gafarta-idan na gafarta wani abu-an gafarta ne domin ku a gaban Almasihu.
Men hvem I tilgive noget, ham tilgiver også jeg; thi også hvad jeg selv har tilgivet, om jeg har tilgivet noget, det har jeg gjort for eders Skyld, for Kristi Åsyn,
11 Wannan ya zama haka ne domin kada shaidan ya yaudare mu. Don ba mu jahilci irin makircinsa ba.
for at vi ikke skulle bedrages af Satan; thi hans Anslag ere os ikke ubekendte.
12 Na samu budaddiyar kofa daga wurin Ubangiji yayin da nazo birnin Tarwasa, in yi wa'azin bisharar Almasihu a can.
Da jeg kom til Troas for at prædike Kristi Evangelium, og der var åbnet mig en Dør i Herren,
13 Duk da haka, raina bai kwanta ba, domin ban ga dan'uwana Titus a can ba. Sai na bar su a can, na dawo Makidoniya.
da havde jeg ingen Ro i min Ånd, fordi jeg ikke fandt Titus, min Broder; men jeg tog Afsked med dem og drog til Makedonien.
14 Amma godiya ta tabbata ga Allah, wanda cikin Almasihu yake kai mu ga nasara a koyaushe. Ta wurin mu ya baza kamshi mai dadi na saninsa ko'ina.
Men Gud ske Tak, som altid fører os i Sejrstog i Kristus og lader sin Kundskabs Duft blive kendelig ved os på ethvert Sted.
15 Gama mu, kamshi ne mai dadi na Almasihu ga Allah, a tsakanin wadanda ake ceton su, da kuma tsakanin wadanda suke hallaka.
Thi en Kristi Vellugt ere vi for Gud, iblandt dem, som frelses, og iblandt dem, som fortabes,
16 Ga mutanen da suke hallaka, kamshi ne daga mutuwa zuwa mutuwa. Ga wadanda suke samun ceto kuma kamshi ne daga rai zuwa rai. Wanene ya cancanci wadannan abubuwan?
for disse en Duft af Død til Død, for hine en Duft af Liv til Liv. Og hvem er dygtig dertil?
17 Gama mu ba kamar sauran mutane muke ba, masu sayar da maganar Allah domin samun riba. Maimakon haka, da tsarkakkiyar manufa, muke magana cikin Almasihu, kamar yadda Allah ya aiko mu, a gaban Allah.
Thi vi ere ikke som de mange, at vi gøre en Forretning af Guds Ord, men som af Renhed, som af Gud tale vi for Guds Åsyn i Kristus.

< 2 Korintiyawa 2 >