< 2 Korintiyawa 12 >

1 Dole ne in yi fahariya, ko dashike bata da ribar komai. Amma zan ci gaba da wahayoyi da ruyoyi daga Ubangiji.
Jeg må rose mig skjønt det ikke er gagnlig; men jeg kommer nu til syner og åpenbarelser av Herren.
2 Na san wani mutum cikin Almasihu, wanda shekaru goma sha hudu da suka wuce-ko a cikin jiki ne ko ba a jiki ba, ban sani ba, Allah ya sani-an dauke shi zuwa sama ta uku.
Jeg kjenner et menneske i Kristus - om han var i legemet, vet jeg ikke, eller utenfor legemet, vet jeg ikke; Gud vet det - en som for fjorten år siden blev rykket like inn i den tredje himmel.
3 Kuma na san wannan mutumin-ko cikin jiki ko kuma ba cikin jiki ba, ban sani ba, Allah ya sani-
Og jeg kjenner dette menneske - om han var i legemet eller utenfor legemet, vet jeg ikke; Gud vet det -
4 an dauke shi zuwa Firdausi ya kuma ji madaukakan al'amura wadanda ba mai iya fadi.
han blev rykket inn i Paradis og hørte usigelige ord, som det ikke er et menneske tillatt å tale.
5 A madadin irin wannan mutumin zan yi fahariya. Amma a madadin kaina ba zan yi fahariya ba, sai dai game da kumamancina.
Av dette vil jeg rose mig; men av mig selv vil jeg ikke rose mig, uten av min skrøpelighet.
6 Idan ina so inyi takama, ba zai zama wauta ba, domin gaskiya zan rika fada. Amma zan guje wa fahariya, domin kada wani ya dauke ni fiye da abinda ya gani ko ya ji daga gare ni.
For om jeg vil rose mig, blir jeg ikke en dåre; for det er sannhet jeg vil tale; men jeg lar det være, forat ingen skal tenke større om mig enn som han ser mig eller hører av mig.
7 Zan kuma gujewa fahariya saboda irin wadannan gagaruman ruyoyi. Domin kada in cika da girman kai, an ba ni kaya cikin jikina, manzon shaidan ya wahalshe ni, domin kada in yi girman kai dayawa.
Og forat jeg ikke skal ophøie mig av de høie åpenbarelser, er det gitt mig en torn i kjødet, en Satans engel, forat han skal slå mig, så jeg ikke skal ophøie mig.
8 Na roki Ubangiji har sau uku domin ya kawar mini da wannan.
Om denne bad jeg Herren tre ganger at han måtte vike fra mig;
9 Amma ya ce mani, “Alherina isasshe yake a gare ka, domin ta wurin kumamanci karfi yake cika.” Don haka zan gwammace takama a akan kasawata, domin ikon Almasihu ya zauna a ciki na.
og han sa til mig: Min nåde er dig nok; for min kraft fullendes i skrøpelighet. Derfor vil jeg helst rose mig av min skrøpelighet, forat Kristi kraft kan bo i mig.
10 Sabili da haka a gamshe nake ta dalilin Almasihu, cikin kumamanci, ko raini, ko matsaloli, ko jarabobi, ko kuma nawaya. Don ko dayaushe na raunana, ina da karfi kuma.
Derfor er jeg vel til mote i skrøpelighet, i mishandling, i nød, i forfølgelser, i trengsler for Kristi skyld; for når jeg er skrøpelig, da er jeg sterk.
11 Na zama wawa! Amma ku ne kuka tilasta mani haka, ya kamata ku yabe ni, domin ban kasa ga wadan da ake kira manyan manzanni ba, ko da shike ni ba komai ba ne.
Jeg er blitt en dåre; I har tvunget mig til det. For jeg burde få ros av eder; jeg stod jo ikke i noget tilbake for de såre store apostler, om jeg enn er intet.
12 Cikakkun alamun mazanni sun faru a tsakanin ku, da cikakken hakuri, alamu da abubuwan ban mamaki da manyan ayyuka.
En apostels tegn blev iallfall gjort blandt eder med all utholdenhet, både med tegn og under og kraftige gjerninger.
13 Ta yaya kuka zama da rashin muhimmanci akan sauran Ikkilisiyoyin, sai dai don ban zama matsala a gare ku ba? Ku gafarce ni a kan wannan laifin.
For hvad var det I blev tilsidesatt i for de andre menigheter uten i det at jeg ikke falt eder til byrde? Tilgi mig denne urett!
14 Duba! A shirye nake domin in zo gare ku karo na uku. Ba zan so in zamar maku nawaya ba, domin ba kayanku nake so ba. Amma ku nake so. Domin ba 'ya'ya ne ya kamata su yi wa iyaye tanadi ba. Amma iyaye ne ya kamata su yi wa 'ya'ya tanadi.
Se, for tredje gang er jeg nu rede til å komme til eder, og jeg vil ikke falle eder til byrde; for jeg søker ikke det som eders er, men eder selv. Barna er jo ikke skyldige å samle til foreldrene, men foreldrene til barna.
15 Zan yi murnar biyan bukatunku, ko ya kai ga in bada rai na. Idan ni na kaunace ku, sosai, sai ni za a kaunata kadan?
Men jeg vil med glede ofre, ja bli ofret for eders sjeler, om jeg enn elskes dess mindre av eder jo mere jeg elsker eder.
16 Amma kamar yadda yake, ban nawaita maku ba. Amma, da shike ni mai dabara ne, Ni ne na kama ku da yaudara.
Men la så være at jeg ikke var eder til byrde, men jeg var listig og fanget eder med svik!
17 Ko na cutar da ku ta wurin wadanda na turo maku?
Søkte jeg vel vinning av eder ved nogen av dem som jeg sendte til eder?
18 Rokar Titus na yi domin ya zo gare ku, sa'an nan na turo shi da wani dan'uwa. Ko da na turo Titus, ya cutar da ku ne, ba cikin hanya daya muka yi tafiya ba? Ba a sawu daya muka yi tafiya ba?
Jeg tilskyndte Titus og sendte vår bror med ham; mon vel Titus søkte vinning av eder? vandret vi ikke i den samme ånd? ikke i de samme spor?
19 Kuna tsammanin a dukan wannan lokaci muna kare kan mu a gaban ku ne? A gaban Allah, a cikin Almasihu muke fadin komai domin ku sami karfi.
Alt lenge har I tenkt at det er eder vi forsvarer oss for. Nei, det er for Guds åsyn vi taler i Kristus; men alt er til eders opbyggelse, mine elskede!
20 Ina tsoro domin idan na zo ba zan same ku yadda nake zato ba. Ina tsoro kuma ba za ku same ni kamar yadda ku ke zato ba. Ina tsoron cewa za a sami gardandami, kishi, barkewar fushi, buri na son kai, gulma, girman kai da yamutsi.
For jeg frykter for at når jeg kommer, skal jeg ikke finne eder slik som jeg ønsker, og at jeg skal finnes av eder slik som I ikke ønsker - at det skal være kiv, avind, vrede, stridigheter, baktalelse, sladder, opblåsthet, uorden -
21 Ina tsoron cewa bayan na dawo, Allahna zai iya kaskantar da ni a gaban ku. Ina tsoron cewa zan yi bakinciki domin mutane dayawa da suka yi zunubi kafin yanzu, wadanda kuma ba su tuba daga rashin tsarki da zina da fasikanci da ayyukan sha'awa da suka aikata ba.
at når jeg kommer, skal min Gud atter ydmyke mig hos eder, og jeg skal komme til å sørge over mange av dem som før har syndet og ikke har omvendt sig fra den urenhet og utukt og skamløshet som de har drevet.

< 2 Korintiyawa 12 >