< 1 Timoti 6 >

1 Bari duk wadanda ke bayi a karkashin karkiya su ga iyayengijinsu sun cancanci dukan daraja. Su yi haka domin kada a sabawa sunan Allah da koyarwarsa.
Alle de, som ere Trælle under Åg, skulle holde deres egne Herrer al Ære værd, for at ikke Guds Navn og Læren skal bespottes.
2 Bayin da suke da iyayengiji da ke masu ba da gaskiya kada su rena su saboda su 'yan'uwa ne. A maimakon haka, su yi masu hidima da kwazo. Gama iyayengijin da suke cin ribar aikinsu masu bi ne, kaunattatu kuma. Ka koyar ka kuma bayyana wadannan abubuwa.
Men de, der have troende Herrer, må ikke ringeagte dem, fordi de ere Brødre, men tjene dem desto hellere, fordi de, som nyde godt af deres gode Gerning, ere troende og elskede. Lær dette, og forman dertil!
3 Idan ya kasance wani na koyar da wani abu dabam bai kuma yarda da amintaciyar koyarwa ba, wato maganar Ubangijinmu Yesu Almasihu. Alal misali ba su amince da koyarwa da ke kai ga Allahntaka ba.
Dersom nogen fører fremmed Lære og ikke holder sig til vor Herres Jesu Kristi sunde Ord og til den Lære, som stemmer med Gudsfrygt.
4 Wannan mutum mai girman kai ne, kuma bai san komai ba. A maimakon haka, yana da matukar jayayya da gardama game da kalmomi. Wadannan kalmomi na kawo kishi, da husuma, da zage-zage, da miyagun zace-zace, da
han er opblæst, skønt han intet ved, men er syg for Stridigheder og Ordkampe, hvoraf kommer Avind, Kiv, Forhånelser, ond Mistanke
5 yawan rashin jituwa tsakanin mutane masu rubabbun hankula. Sun bijire wa gaskiya. Suna tunani cewa ibada hanya ce ta yin arziki.” Ka zame daga wadannan abubuwa.
og idelige Rivninger hos Mennesker, som ere fordærvede i Sindet og berøvede Sandheden, idet de mene, at Gudsfrygten er en Vinding.
6 Yanzu bin Allah tare da dangana babbar riba ce.
Vist nok er Gudsfrygten sammen med Nøjsomhed en stor Vinding.
7 Gama ba mu kawo komai a duniya ba, ba zamu iya fita cikinta da komai ba.
Thi vi have intet bragt ind i Verden, det er da åbenbart, at vi ej heller kunne bringe noget ud derfra.
8 A maimakon haka, mu dangana da abinci da kuma sutura.
Men når vi have Føde og Klæder, ville vi dermed lade os nøje.
9 To wadanda ke son zama mawadata su kan fada cikin jaraba, cikin tarko. Suna fadawa cikin abubuwan wauta da sha'awoyi masu illa da kowanne abu da ke sa mutane su dulmaya cikin lallacewa da hallaka.
Men de, som ville være rige, falde i Fristelse og Snare og mange ufornuftige og skadelige Begæringer, som nedsænke Menneskene i Undergang og Fortabelse;
10 Gama son kudi shine tushen kowacce irin mugunta. Wadansu mutane garin neman kudi sun kauce daga bangaskiya, sun kuma jawowa kansu bakin ciki mai yawa.
thi Pengegridskheden er en Rod til alt ondt; og ved at hige derefter ere nogle farne vild fra Troen og have gennemstunget sig selv med mange Smerter.
11 Amma kai, mutumin Allah, ka guji wadannan abubuwa, ka bi adalci, ibada, aminci, kauna, jimiri, da tawali'u.
Men du, o Guds Menneske! fly disse Ting; jag derimod efter Retfærdighed, Gudsfrygt, Tro, Kærlighed, Udholdenhed, Sagtmodighed;
12 Ka yi fama, fama mai kyau na bangaskiya. Ka kama rai madawami da aka kira ka gare shi. A kan wannan ne ka ba da shaida a gaban shaidu masu yawa game da abin da ke da kyau. (aiōnios g166)
strid Troens gode Strid, grib det evige Liv, til hvilket du er bleven kaldet og har aflagt den gode Bekendelse for mange Vidner. (aiōnios g166)
13 Ina ba ka wannan umarni a gaban Allah wanda ke rayar da dukan abubuwa, da gaban Almasihu Yesu, wanda ya fadi abin da ke gaskiya ga Bilatus Babunti.
Jeg byder dig for Guds Åsyn, som holder alle Ting i Live, og for Kristus Jesus, som vidnede den gode Bekendelse for Pontius Pilatus,
14 Ka bi doka daidai, babu abin zargi har bayanuwar Ubangijinmu Yesu Almasihu.
at du holder Budet uplettet, ulasteligt indtil vor Herres Jesu Kristi Åbenbarelse,
15 Allah zai nuna bayyanuwarsa a daidai lokaci- Allah, mai albarka, Makadaicin iko, Sarkin da ke sarauta, Ubangiji mai mulki.
hvilken den salige og alene mægtige, Kongernes Konge og Herrernes Herre skal lade til Syne i sin Tid;
16 Shine kadai marar mutuwa, mai zama cikin hasken da ba ya kusantuwa. Ba wanda ke ganinsa, ko ya iya hango shi. Girma ya tabbata a gare shi da kuma madawwamin iko. Amin. (aiōnios g166)
han, som alene har Udødelighed, som bor i et utilgængeligt Lys, hvem intet Menneske har set, ikke heller kan se; ham være Ære og evig Magt! Amen! (aiōnios g166)
17 Ka gaya wa masu dukiya a cikin wannan duniya kada su daga kai, kada su sa bege ga arziki mara dawwama. Maimamakon haka, su sa begensu ga Allah wanda ke ba mu wadatar gaske domin jin dadin mu. (aiōn g165)
Byd dem, som ere rige i den nærværende Verden, at de ikke hovmode sig, ej heller sætte Håb til den usikre Rigdom, men til Gud, som giver os rigeligt alle Ting at nyde; (aiōn g165)
18 Gaya masu su yi nagarta su arzurta a ayyuka nagari, su zama masu bayarwa hannu sake.
at de gøre godt, ere rige på gode Gerninger, gerne give, meddele
19 Ta haka za su ajiye wa kansu harsashi mai kyau kan abin da ke zuwa domin su amshi rayuwa ta kwarai.
og således, opsamle sig selv en god Grundvold for den kommende Tid, for at de kunne gribe det sande Liv.
20 Timoti, ka kare abin da aka ba ka. Ka nisanci maganar wauta da gardamomin da ke sabawa juna wanda ake kira ilimi a karyace.
O Timotheus! vogt på den betroede Skat, idet du vender dig bort fra den vanhellige, tomme Snak og Indvendingerne fra den falskelig såkaldte Erkendelse,
21 Wadansu mutane suna shelar wadannan abubuwa, don haka sun kauce wa bangaskiyar. Bari alheri ya kasance tare da kai.
hvilken nogle have bekendt sig til og ere afvegne fra Troen. Nåden være med dig!

< 1 Timoti 6 >