< 1 Timoti 5 >

1 Kada ka tsauta wa dattijo. Sai dai ka gargade shi kamar mahaifi. Ka gargadi samari kamar 'yan'uwa.
En gammel Mand maa du ikke skælde paa, men forman ham som en Fader, unge Mænd som Brødre,
2 Gargadi dattawa mata kamar iyaye mata, 'yan mata kamar 'yan'uwa mata cikin dukkan tsarki.
gamle Kvinder som Mødre, unge som Søstre, i al Renhed.
3 Ka girmama gwamraye, gwamraye na gaske.
Ær Enker, dem, som virkelig ere Enker;
4 Amma gwamruwar da take da 'ya'ya ko jikoki, bari su fara nuna bangirma cikin danginsu. Bari su sakawa iya-yensu, domin Allah yana jin dadin haka.
men om en Enke har Børn eller Børnebørn, da lad dem først lære at vise deres eget Hus skyldig Kærlighed og gøre Gengæld imod Forældrene; thi dette er velbehageligt for Gud.
5 Amma gwamruwa ta gaske da ke ita kadai, ta kafa begenta ga Allah. Kullum tana tsananta yin roke-roke da addu'o'i dare da rana.
Men den, som virkelig er Enke og staar ene, har sat sit Haab til Gud og bliver ved med sine Bønner og Paakaldelser Nat og Dag;
6 Amma, mace mai son zaman annashuwa ta riga ta mutu, ko da shike tana raye.
men den, som lever efter sine Lyster, er levende død.
7 Kuma ka yi wa'azin wadannan al'amura donsu zama marasa abin zargi.
Forehold dem ogsaa dette, for at de maa være ulastelige.
8 Amma idan mutum bai iya biyan bukatun 'yan'uwansa ba, musamman iyalin gidansa, ya musunci bangaskiya, kuma gara marar bi da shi.
Men dersom nogen ikke har Omsorg for sine egne og især for sine Husfæller, han har fornægtet Troen og er værre end en vantro.
9 Bari a lisafta mace gwamruwa idan ba ta kasa shekara sittin ba, matar miji daya.
En Enke kan udnævnes, naar hun er ikke yngre end tresindstyve Aar, har været een Mands Hustru,
10 A san ta da kyawawan ayyuka, ko ta kula da 'ya'yanta, ko tana mai karbar baki, ko mai wanke kafafun masubi, ko mai taimakon wadanda ake tsanantawa, mai naciya ga kowanne kyakkyawan aiki.
har Vidnesbyrd for gode Gerninger, har opfostret Børn, har vist Gæstfrihed, har toet helliges Fødder, har hjulpet nødlidende, har lagt sig efter al god Gerning.
11 Amma game da gwamraye masu kuruciya, kada a sa su cikin lissafi. Domin idan suka fada cikin sha'awoyin jiki da ke gaba da Almasihu, sukan so su yi aure.
Men afvis unge Enker; thi naar de i kødelig Attraa gøre Oprør imod Kristus, ville de giftes
12 Ta wannan hanya ce sun tara wa kansu tsarguwa saboda sun tada alkawarinsu na fari.
og have saa den Dom, at de have sveget deres første Tro.
13 Sun saba da halin ragwanci, suna yawo gida gida. Ba zama raggwaye kawai su ka yi ba. Amma sun zama magulmata, masu shishshigi, masu karambani. Suna fadin abin da bai dace ba.
Tilmed lære de, idet de løbe omkring i Husene, at være ørkesløse, og ikke alene ørkesløse, men ogsaa at være sladderagtige og blande sig i uvedkommende Ting, idet de tale, hvad der er utilbørligt.
14 Saboda haka ina so gwamraye masu kuruciya su yi aure, su haifi 'ya'ya, su kula da gida, domin kada a ba magabci zarafin zargin mu ga aikata mugunta.
Derfor vil jeg, at unge Enker skulle giftes, føde Børn, styre Hus, ingen Anledning give Modstanderen til slet Omtale.
15 Domin wadansu sun rigaya sun kauce zuwa ga bin shaidan.
Thi allerede have nogle vendt sig bort efter Satan.
16 Idan wata mace mai bada gaskiya tana da gwamraye, bari ta taimakesu, don kada a nawaita wa Ikilisiya, domin Ikilisiya ta iya taimakon gwamraye na gaske.
Dersom nogen troende Kvinde har Enker, da lad hende hjælpe dem, og lad ikke Menigheden bebyrdes, for at den kan hjælpe de virkelige Enker.
17 Dattawa wadanda suke mulki da kyau sun cancanci girmamawa ninki biyu, musamman wadanda suke aiki da kalma da kuma koyarwa.
De Ældste, som ere gode Forstandere, skal man holde dobbelt Ære værd, mest dem, som arbejde i Tale og Undervisning.
18 Gama nassi ya ce, “Kada a sa takunkumi a bakin takarkari lokacin da yake sussukar hatsi,” kuma “Ma'aikaci ya cancanci a biya shi hakinsa.”
Thi Skriften siger: “Du maa ikke binde Munden til paa en Okse, som tærsker”; og: “Arbejderen er sin Løn værd.”
19 Kada ka karbi zargi game da dattijo sai shaidu sun kai biyu ko uku.
Tag ikke imod noget Klagemaal imod en Ældste, uden efter to eller tre Vidner.
20 Ka tsauta wa masu zunubi gaban kowa domin sauran su ji tsoro.
Dem, som synde, irettesæt dem for alles Aasyn, for at ogsaa de andre maa have Frygt.
21 Na umarce ka a gaban Allah, da Almasihu Yesu, da zababbun mala'iku ka kiyaye ka'idodin nan ban da hassada kuma kada ka yi komai da nuna bambanci.
Jeg besværger dig for Guds og Kristi Jesu og de udvalgte Engles Aasyn, at du vogter paa dette uden Partiskhed, saa du intet gør efter Tilbøjelighed.
22 Kada ka yi garajen dibiya wa kowa hannuwa. Kada ka yi tarayya cikin zunuban wani. Ka tsare kanka da tsabta.
Vær ikke hastig til at lægge Hænder paa nogen, og gør dig ikke delagtig i andres Synder; hold dig selv ren!
23 Kada ka ci gaba da shan ruwa. Amma, maimakon haka ka sha ruwan inabi kadan saboda cikinka da yawan rashin lafiyarka.
Drik ikke længere bare Vand, men nyd lidt Vin for din Mave og dine jævnlige Svagheder.
24 Zunuban wadansu mutane a bayyane suke, sun yi gaba da su cikin hukunci. Amma wadansu zunubansu na bin baya.
Nogle Menneskers Synder ere aabenbare og gaa forud til Dom; men for nogle følge de ogsaa bagefter.
25 Haka kuma, wadansu kyawawan ayyukansu a bayyane suke, amma wadan sun ma ba su boyuwa.
Ligeledes ere ogsaa de gode Gerninger aabenbare, og de, som det forholder sig anderledes med, kunne ikke skjules.

< 1 Timoti 5 >