< 1 Timoti 3 >
1 Wannan magana tabattaciya ce: Idan wani na da marmari ya zama shugaban Ikilisiya, ya na marmarin aiki mai kyau.
This is a faithful saying: someone who seeks to be an overseer desires a good work.
2 Don haka, wajibi ne shugaban Ikilisiya ya zama mara abin zargi. Ya zama mai mace daya. Wajibi ne ya zama mai kamewa, mai hankali, mai natsuwa mai karbar baki. Wajibi ne ya iya koyarwa.
The overseer therefore must be without reproach, the husband of one wife, temperate, sensible, modest, hospitable, good at teaching;
3 Kada ya zama mashayin giya, da mai tankiya. A maimakon haka ya zama da natsuwa, mai salama. Ba mai son kudi ba.
not a drinker, not violent, not greedy for money, but gentle, not quarrelsome, not covetous;
4 Wajibi ne ya iya lura da gidansa da kyau, 'ya'yansa su zama masu yi masa biyayya da dukkan bangirma.
one who rules his own house well, having children in subjection with all reverence;
5 Gama idan mutum bai iya sarrafa gidansa ba, ta yaya zai iya lura da Ikkilisiyar Allah?
(for how could someone who does not know how to rule his own house take care of God’s assembly?)
6 Bai kamata ya zama sabon tuba ba, domin kada ya kumbura da girman kai, kada ya fadi cikin irin hukunci da aka yi wa Ibilis.
not a new convert, lest being puffed up he fall into the same condemnation as the devil.
7 Wajibi ne kuma ya kasance mai kyakyawar shaida a cikin wadanda ba masubi ba, domin kada ya fadi cikin kunya da kuma tarkon Ibilis.
Moreover he must have good testimony from those who are outside, to avoid falling into reproach and the snare of the devil.
8 Hakanan kuma Dikinoni su kasance da halin mutunci, ba masu magana biyu ba. Bai kamata su zama mashayan giya ko masu hadama ba.
Servants, in the same way, must be reverent, not double-tongued, not addicted to much wine, not greedy for money,
9 Su zama masu rikon bayyananniyar gaskiyar bangaskiya da lamiri mai tsabta.
holding the mystery of the faith in a pure conscience.
10 Daidai ne kuma a fara tabbatar da su, daga nan su fara hidima domin basu da abin zargi.
Let them also first be tested; then let them serve if they are blameless.
11 Hakanan ma mata su zama masu mutunci. Bai kamata su zama magulmanta ba, amma masu kamewa da aminci cikin komai.
Their wives in the same way must be reverent, not slanderers, temperate, and faithful in all things.
12 Tilas Dikinoni su zama masu mata daya daya. Su iya kulawa da 'ya'yansu da gidajensu.
Let servants be husbands of one wife, ruling their children and their own houses well.
13 Gama wadanda suka yi hidima da kyau sun sami tsayawa mai kyau da gabagadi cikin bangaskiyar da ke cikin Almasihu Yesu.
For those who have served well gain for themselves a good standing and great boldness in the faith which is in Christ Jesus.
14 Ina rubuta maka wadannan abubuwa, da sa zuciya zan zo wurin ka ba da jimawa ba.
These things I write to you, hoping to come to you shortly,
15 Amma idan na yi jinkiri, ina rubuta maka ne domin ka san yadda za ka gudanar da al'amuranka a cikin gidan Allah, wato Ikklisiyar Allah rayyayiya, ginshiki da kuma mai tallafar gaskiya.
but if I wait long, that you may know how men ought to behave themselves in God’s house, which is the assembly of the living God, the pillar and ground of the truth.
16 Babu musu an bayyana cewa ibadarmu ta gaskiya da girma take: “Ya bayyana kansa cikin jiki, Ruhu ya baratar da shi, mala'iku suka gan shi, aka yi shelarsa a cikin al'ummai, aka gaskanta shi a duniya, sa'an nan aka dauke shi sama cikin daukaka.
Without controversy, the mystery of godliness is great: God was revealed in the flesh, justified in the spirit, seen by angels, preached among the nations, believed on in the world, and received up in glory.