< 1 Timoti 2 >
1 Don haka da farko dai, Ina roko a yi roke-roke da addu'o'i, da yin roko domin jama, a dukka, da ba da godiya, a yi haka domin dukkan mutane,
2 domin sarakuna da dukkan masu mulki, domin mu yi zaman salama da rayuwa a natse cikin Allahntaka da daraja.
3 Wannan yana da kyau da karbuwa a gaban Allah mai cetonmu.
4 Yana so dukkan mutane su sami ceto, su kai ga sanin gaskiya.
5 Domin Allah daya ne, Matsakanci kuma daya ne, tsakanin Allah da mutum, wannan mutum Almasihu Yesu ne.
6 Ya bada kansa fansa domin kowa, domin shaida a daidaitaccen lokaci.
7 Sabo da wannan dalilin, aka sa ni kaina, na zama mai shelar bishara da manzo. Gaskiya nake fada. Ba karya nake yi ba. Ni mai koyarwa ne na al'ummai cikin gaskiya da kuma imani.
8 Saboda haka, ina so maza da ke a kowanne wuri suyi addu'a, kuma suna daga hannuwa masu tsarki a sama ba tare da fushi da gardama ba.
9 Kazalika, ina so mata su sa kayan da ya cancanta, da adon da ya dace da kamun kai. Kada su zama masu kitson gashi da zinariya da azurfa da tufafi masu tsada.
10 Ina so su sa tufafin da ya cancanci matan da ke rayuwar Allahntaka ta wurin kyawawan ayyuka.
11 Mace ta koya cikin natsuwa da saukin kai a cikin komai.
12 Ban ba da izini mace ta koyar ko ta nuna iko a kan namiji ba, amma ta zauna da natsuwa.
13 Adamu ne aka fara halitta, kafin Hauwa'u.
14 Ba Adamu ne aka yaudara ba, amma macen ce aka yaudara cikin laifi.
15 Duk da haka, zata sami ceto ta wurin haifuwar 'ya'ya, idan suka ci gaba cikin bangaskiya, da kauna da tsarki da sahihiyar zuciya.