< 1 Tessalonikawa 5 >
1 Yanzu fa game da zancen lokatai da zamanai 'yan'uwa, ba ku da bukatar a rubuta maku wani abu.
2 Domin ku da kanku kun sani kwarai cewa ranar zuwan Ubangiji kamar barawo take da dare.
3 Da suna zancen “zaman lafiya da kwanciyar rai,” sai hallaka ta zo masu ba zato ba tsammani. Zai zama kamar nakudar haihuwa ce da ke kama mace mai ciki. Ba su kwa da wata hanyar kubuta.
4 Amma ku, 'yan'uwa, ai ba cikin duhu kuke ba har da wannan rana zata mamaye ku kamar barawo.
5 Domin dukkan ku 'ya'yan haske ne 'ya'yan rana kuwa. Mu ba 'ya'yan dare ba ne ko na duhu,
6 Don haka, kada muyi barci kamar yadda sauran ke yi. Maimakon haka, bari mu kasance muna zaman tsaro kuma muna a fadake.
7 Don masu yin barci da dare suke yin barci, haka kuma masu sha su bugu ma da dare suke yi.
8 Tunda shike mu 'ya'yan rana ne, bari mu zauna a natse. Bari musa sulke na bangaskiya da kauna, mu kuma sa kwalkwali don ceton mu dake gaba.
9 Domin Allah bai kaddara mu ga fushinsa ba, sai dai ga samun ceto ta wurin Ubangijin mu Yesu Almasihu.
10 Shi ne wanda ya mutu domin mu, don ko da muna raye ko muna mace, mu iya rayuwa tare da shi,
11 Domin haka ku ta'azantar da juna ku kuma inganta juna, kamar yadda kuke yi.
12 Muna rokon ku, 'yan'uwa, ku bada daraja ga wadanda suke aiki a tsakaninku wadanda kuma suke shugabanci a kan ku cikin Ubangiji, wadanda kuma suke horonku.
13 Muna kuma rokon ku, da ku kula dasu ku kuma kaunacesu sabili da irin ayyukansu. Ku kuma yi zaman lafiya da junan ku.
14 Muna yi maku gargadi 'yan'uwa; ku jawa marassa ji kunne, ku karfafa marassa karfin zuciya, ku taimaki gajiyayyu, kuyi zaman hakuri da kowa.
15 Ku lura kada wani ya rama mugunta da mugunta, Maimakon haka ma, Ku cigaba da abinda ke mai kyau ga juna da kowa duka.
16 Kuyi farin ciki koyaushe.
17 Kuyi addu'a ba fasawa.
18 A cikin kome kuyi godiya. Domin wannan ne nufin Allah a cikin Yesu Almasihu game daku.
19 Kada ku hana Ruhun Allah aiki a cikin ku.
20 Kada ku raina anabce anabce.
21 Ku gwada komai. Ku rike abinda ke mai kyau.
22 Ku kaucewa duk wani abinda yayi kama da mugunta.
23 Bari Allah na salama ya mai da ku cikakun tsarkaka. Bari dukkan ruhun ku, da zuciyar ku, da jikin ku su zama adanannu marassa zargi domin zuwan Ubangijin mu Yesu Almasihu.
24 Wanda ya kira ku mai aminci ne, wanda kuma zai aikata.
25 Yan'uwa, kuyi addu'a domin mu.
26 Ku gaida dukkan yan'uwa da tsattsarkar sumba.
27 Ina rokon ku saboda Ubangiji ku karanta wasikar nan ga dukkan 'yan'uwa.
28 Bari alherin Ubangijin mu Yesu Almasihu shi kasance tareda ku.