< 1 Tessalonikawa 4 >
1 A karshe, 'yan'uwa, muna karfafa ku kuma muna yi maku gargadi cikin Ubangiji Yesu. Yadda kuka karbi umarni a garemu game da yadda dole za kuyi tafiya kuma ku gamshi Allah, kuma a cikin wannan hanya ku tafi, ku kuma wuce haka.
2 Domin kun san umarnin da muka baku cikin Ubangiji Yesu.
3 Gama wannan ne nufin Allah: kebewar ku - cewa ku kauce wa zina da fasikanci,
4 Cewa kowannenku ya san yadda zai rike mata tasa cikin tsarki da girmamawa.
5 Kada kayi mata cikin zautuwar sha'awa ( kamar al'ummai wadanda basu san Allah ba).
6 Kada wani ya kuskura yaci amanar dan'uwansa akan wannan al'amari. Gama Ubangiji mai ramuwa ne akan dukkan wadannan al'amura, Kamar yadda a baya muka yi maku kashedi kuma muka shaida.
7 Gama Allah bai kira mu ga rashin tsarki ba, amma ga rayuwar tsarki.
8 Domin haka, duk wanda yaki wannan ba mutane yaki ba, amma Allah, wanda ya bada Ruhunsa Mai Tsarki a gareku.
9 Game da kaunar 'yan'uwa, baku bukatar wani ya sake rubuta maku, gama ku da kanku Allah ya koyar da ku kaunar 'yan'uwa.
10 Ba shakka, kunayin haka ga dukkan 'yan'uwa wadanda ke cikin dukkan Makidoniya. Amma muna gargadin ku 'yan'uwa, kuyi haka bugu da kari.
11 Kuma muna gargadin ku 'yan'uwa kuyi kokari ku zauna a natse, ku kula da al'amuranku, kuyi aiki da hannuwanku, Yadda muka umarceku a baya.
12 Kuyi haka domin tafiyar ku ta zama dai dai a gaban wadanda basu bada gaskiya ba, kuma ya zama baku cikin bukatar komai.
13 Bamu so ku zama da rashin fahimta ba, 'yan'uwa, game da wadanda sukayi barci, domin kada kuyi bacin rai kamar sauran wadanda basu da tabbacin abinda ke gaba.
14 Domin idan mun bada gaskiya Yesu ya mutu kuma ya tashi, haka kuma tare da Yesu Allah zai maido da duk wadanda suka yi barci a cikinsa.
15 Gama muna fada maku wannan daga maganar Ubangiji, cewa mu da muke a raye, da aka bari har zuwan Ubangiji, babu shakka ba za mu riga wadanda suka yi barci ba.
16 Gama Ubangiji da kan sa zai sauko daga sama. Zai zo da muryar babban mala'ika, da karar kahon Allah, sai matattu cikin Almasihu su fara tashi.
17 Sai mu da muke a raye, wadanda aka bari, tare dasu za'a fyauce mu zuwa cikin gizagizai, mu hadu da Ubangiji cikin sararin sama. Haka zamu cigaba da kasancewa da Ubangiji.
18 Domin haka ku ta'azantar da juna da wadannan maganganu.