< 1 Tessalonikawa 3 >
1 Saboda haka, da bamu iya jimrewa ba, sai mukayi tunanin cewa ya dace mu dakata a Atina tukunna.
C'est pourquoi ne pouvant plus soutenir [la privation de vos nouvelles] nous avons trouvé bon de demeurer seuls à Athènes.
2 Sai muka aikaTimoti, dan'uwanmu dakuma bawan Allah a bisharar Almasihu, domin karfafaku ya kuma ta'azantar daku a fannin bangaskiya.
Et nous avons envoyé Timothée, notre frère, Ministre de Dieu, et notre compagnon d'œuvre en l'Evangile de Christ, pour vous affermir, et vous exhorter touchant votre foi.
3 Mun yi haka ne saboda kada waninku ya raunana domin wadannan wahaloli. Domin ku da kanku kun sani cewa don haka aka kiraye mu.
Afin que nul ne soit troublé dans ces afflictions, puisque vous savez vous-mêmes que nous sommes destinés à cela.
4 Hakika, a lokacin da muke tare daku, mun gaya maku cewa muna daf da shan wahala, haka ya kuma kasance, kamar yadda kuka sani.
Car quand nous étions avec vous, nous vous prédisions que nous aurions à souffrir des afflictions; comme cela est aussi arrivé, et vous le savez.
5 Domin haka, da ban iya jimrewa ba, sai na aiko domin in san yadda bangaskiyar ku take. Watakila ko magafci a wata hanya ya rinjaye ku, sai ya kasance wahalarmu ta zama a banza.
C'est pourquoi, dis-je, ne pouvant plus soutenir [cette inquiétude] j'ai envoyé Timothée pour reconnaître l'état de votre foi, de peur que celui qui tente, ne vous eût tentés en quelque sorte, et que notre travail ne fût rendu inutile.
6 Amma Timoti da ya dawo daga gareku sai ya kawo mamu labari mai dadi akan bangaskiyarku da kuma kaunarku. Yako gaya mana cewa kuna kyakkyawan tunani a kanmu, kuma kuna marmarin ganinmu yadda muke marmarin ganinku.
Or Timothée étant revenu depuis peu de chez vous, il nous a apporté d'agréables nouvelles de votre foi et de votre charité, et que vous vous souvenez toujours de nous, désirant fort de nous voir, comme nous aussi nous désirons de vous voir.
7 Sabili da haka, 'yan'uwana, mun sami ta'aziyya tawurinku domin bangaskiyarku, a cikin dukkan bakin cikinmu da shan wuyamu.
C'est pourquoi, mes frères, vous nous avez été en grande consolation à cause de votre foi, dans toute notre affliction, et dans notre nécessité.
8 Yanzu a raye muke, idan kun tsaya da karfi a cikin Ubangiji.
Car maintenant nous vivons, si vous vous tenez fermes au Seigneur.
9 Gama wace irin godiya zamu ba Allah sabili da ku, domin dukan farin cikin da muke dashi a gaban Allah domin ku?
Et quelles actions de grâces n'avons-nous point à rendre à Dieu à cause de vous, pour toute la joie que nous recevons de vous, devant notre Dieu;
10 Dare da rana muke yi maku addu'a sosai domin muga fuskokinku kuma mu cika abin da kuka rasa cikin bangaskiyarku.
Le priant jour et nuit de plus en plus que nous puissions vous revoir, afin de suppléer à ce qui manque à votre foi?
11 Bari Allah da kuma Ubanmu da kansa, da Ubangijinmu Yesu, ya bida sawayen mu zuwa gareku.
Or notre Dieu [et notre] Père, et notre Seigneur Jésus-Christ, veuillent nous ouvrir le chemin pour nous rendre auprès de vous.
12 Bari Ubangiji yasa ku karu ku kuma ribambamya a kaunar 'yan'uwanku da dukan mutane, kamar yadda muke maku.
Et le Seigneur vous fasse croître et abonder de plus en plus en charité les uns envers les autres, et envers tous, comme nous abondons aussi [en charité] envers vous;
13 Bari yayi haka domin ya karfafa zukatanku marassa abin zargi a cikin tsarki a gaban Allah da Ubanmu a lokacin zuwan Ubangijinmu Yesu da dukan tsarkakansa.
Pour affermir vos cœurs sans reproche en sainteté, devant Dieu qui est notre Père, à la venue de notre Seigneur Jésus-Christ, accompagné de tous ses Saints.