< 1 Bitrus 5 >

1 Ina yiwa dattawan da ke cikinku gargadi, ni da nike dan'uwanku dattijo, mashaidin shan wuyar Almasihu, ni kuma mai samun rabo ne daga cikin daukakar daza a bayyana.
Πρεσβυτέρους ⸀οὖνἐν ὑμῖν παρακαλῶ ὁ συμπρεσβύτερος καὶ μάρτυς τῶν τοῦ Χριστοῦ παθημάτων, ὁ καὶ τῆς μελλούσης ἀποκαλύπτεσθαι δόξης κοινωνός,
2 Saboda haka na gargade ku dattawa, kuyi kiwon garken Allah dake tare da ku. Ku kula da su, ba a kan dole ba, amma domin kuna son yin haka, bisa ga yin Allah. Ku kula da su, ba don cin ribar banza ba amma sabo da yardar rai.
ποιμάνατε τὸ ἐν ὑμῖν ποίμνιον τοῦ θεοῦ, ⸀ἐπισκοποῦντεςμὴ ἀναγκαστῶς ἀλλὰ ἑκουσίως ⸂κατὰ θεόν, μηδὲ αἰσχροκερδῶς ἀλλὰ προθύμως,
3 Kada ku zama kamar masu iko akan mutanen dake hannunku, amma ku zama abin koyi ga garken.
μηδʼ ὡς κατακυριεύοντες τῶν κλήρων ἀλλὰ τύποι γινόμενοι τοῦ ποιμνίου·
4 Sa'adda za a bayyana Sarkin Makiyaya zaku karbi rawanin da darajarsa bata dushewa.
καὶ φανερωθέντος τοῦ ἀρχιποίμενος κομιεῖσθε τὸν ἀμαράντινον τῆς δόξης στέφανον.
5 Hakannan, ku kuma samari kuyi biyayya ga dattawa. Dukanku kuyi damara da tawali'u, kuna bauta wa juna, domin Allah ya na tsayayya da mai girman kai, amma yana yiwa masu tawali'u alheri.
ὁμοίως, νεώτεροι, ὑποτάγητε πρεσβυτέροις. πάντες δὲ ⸀ἀλλήλοιςτὴν ταπεινοφροσύνην ἐγκομβώσασθε, ὅτι Ὁ θεὸς ὑπερηφάνοις ἀντιτάσσεται ταπεινοῖς δὲ δίδωσιν χάριν.
6 Saboda haka ku kaskantar da kanku karkashin hannuwan Allah mai iko duka domin ya daukaka ku a madaidecin lokaci.
Ταπεινώθητε οὖν ὑπὸ τὴν κραταιὰν χεῖρα τοῦ θεοῦ, ἵνα ὑμᾶς ὑψώσῃ ἐν καιρῷ,
7 Ku jibga masa duk taraddadin zuciyarku, domin yana kula da ku.
πᾶσαν τὴν μέριμναν ὑμῶν ἐπιρίψαντες ἐπʼ αὐτόν, ὅτι αὐτῷ μέλει περὶ ὑμῶν.
8 Ku natsu, ku zauna a fadake. Magabcinku, ibilis, kamar zaki mai ruri yana zazzagawa, yana neman wanda zai cinye.
νήψατε, γρηγορήσατε. ὁ ἀντίδικος ὑμῶν διάβολος ὡς λέων ὠρυόμενος περιπατεῖ ζητῶν ⸀τινα⸀καταπιεῖν
9 Ku yi tsayayyiyar gaba da shi. Ku yi karfi cikin bangaskiyarku. Ku sani fa abokan tarayyarku da suke cikin duniya suna jimrewa da shan wuyan nan irin taku.
ᾧ ἀντίστητε στερεοὶ τῇ πίστει, εἰδότες τὰ αὐτὰ τῶν παθημάτων τῇ ἐν ⸀τῷκόσμῳ ὑμῶν ἀδελφότητι ἐπιτελεῖσθαι.
10 Bayan shan wuyarku na dan lokaci kadan, Allah mai alheri mara iyaka, wanda ya kiraye ku zuwa ga madawwamiyar daukakarsa cikin Almasihu, zai kammalaku, ya kafa ku, ya kuma karfafa ku. (aiōnios g166)
ὁ δὲ θεὸς πάσης χάριτος, ὁ καλέσας ὑμᾶς εἰς τὴν αἰώνιον αὐτοῦ δόξαν ἐν ⸀Χριστῷ ὀλίγον παθόντας αὐτὸς ⸀καταρτίσει στηρίξει, σθενώσει, ⸀θεμελιώσει (aiōnios g166)
11 Mulki ya tabbata a gare shi har abada abadin. Amin. (aiōn g165)
⸀αὐτῷτὸ κράτος εἰς τοὺς αἰῶνας ⸂τῶν αἰώνων· ἀμήν. (aiōn g165)
12 Na amince da Sila amintaccen dan'uwa ne, kuma na rubuto maku a takaice ta hannunsa. Ina yi maku gargadi ina kuma shaida maku cewa abin da na rubuto alherin Allah ne na hakika. Ku kafu a cikinsa.
Διὰ Σιλουανοῦ ὑμῖν τοῦ πιστοῦ ἀδελφοῦ, ὡς λογίζομαι, διʼ ὀλίγων ἔγραψα, παρακαλῶν καὶ ἐπιμαρτυρῶν ταύτην εἶναι ἀληθῆ χάριν τοῦ θεοῦ· εἰς ἣν ⸀στῆτε
13 Ita matar da ta ke a Babila zababbiya tare da ku, ta na gaisheku, da Markus, dana, yana gaisheku.
ἀσπάζεται ὑμᾶς ἡ ἐν Βαβυλῶνι συνεκλεκτὴ καὶ Μᾶρκος ὁ υἱός μου.
14 Ku gai da juna da sumbar kauna. Salama ta tabbata a gare ku dukanku da ke cikin Almasihu.
ἀσπάσασθε ἀλλήλους ἐν φιλήματι ἀγάπης. εἰρήνη ὑμῖν πᾶσιν τοῖς ἐν ⸀Χριστῷ

< 1 Bitrus 5 >