< 1 Bitrus 3 >
1 Haka ku kuma da kuke matan aure, kuyi biyayya da na ku mazajen, domin in har wadansunsu basa biyayya da maganar Allah, halin matansu ya shawo kansu ba tare da magana ba,
Ligesaa, I Hustruer! underordner eder under eders egne Mænd, for at, selv om nogle ere genstridige imod Ordet, de kunne vindes uden Ord ved Hustruernes Vandel,
2 Domin sun ga tsattsakan halinku da ladabinku.
naar de iagttage eders kyske Vandel i Frygt.
3 Haka ma adonku kar ya zama na kwalliyar waje kitson kai, kayan zinariya ko tufafi masu kawa.
Eders Prydelse skal ikke være den udvortes med Haarfletning og paahængte Guldsmykker eller Klædedragt,
4 Amma bari adon ya zama na mutum na cikin zuciya, kuma adon ya zama kyan nan marar dushewa, na kamun kai da natsatsen ruhu, wanda yake da daraja a gaban Allah.
men Hjertets skjulte Menneske med den sagtmodige og stille Aands uforkrænkelige Prydelse, hvilket er meget kosteligt for Gud.
5 Haka tsarkakan mata su ka yi ado kamar haka. Suka dogara ga Allah suka yi biyayya ga mazajensu.
Thi saaledes var det ogsaa, at fordum de hellige Kvinder, som haabede paa Gud, prydede sig, idet de underordnede sig under deres egne Mænd,
6 Ta haka Saratu ta yi biyayya ga Ibrahim ta kira shi “ubangiji”. Yanzu ku 'ya'yantane in dai kun yi aiki nagari, idan kuma ba ku ji tsoron wahala ba.
som Sara var Abraham lydig, hun kaldte ham Herre, hun, hvis Børn I ere blevne, naar I gøre det gode og ikke frygte nogen Rædsel.
7 Kamar yadda na fada wa matan aure haka ma mazaje, ku zauna da mata da sanin su raunana ne abokan tarayya ne na karbar baiwar rayuwa. Ku dinga yin haka domin a rika jin addu'oinku.
Ligesaa I Mænd! lever med Forstand sammen med eders Hustruer som med et svagere Kar, og beviser dem Ære som dem, der ogsaa ere Medarvinger til Livets Naadegave, for at eders Bønner ikke skulle hindres.
8 Daga karshe, dukanku ku hada hankulanku, ku zama masu juyayi, masu kauna kamar 'yan'uwa, masu taushin zuciya, masu tawali'u.
Og til Slutning værer alle enssindede, medlidende, kærlige imod Brødrene, barmhjertige, ydmyge;
9 Kada ku rama mugunta da mugunta ko zagi da zagi. A maimakon haka ku cigaba da sa albarka, gama sabili da haka ne musamman aka kiraye ku, domin ku gaji albarka.
betaler ikke ondt med ondt, eller Skældsord med Skældsord, men tværtimod velsigner, thi dertil bleve I kaldede, at I skulle arve Velsignelse.
10 “Wanda duk yake so ya more a rayuwarsa ya kuma ga kwanaki masu alheri, to fa, ya kame harshen sa daga mugunta da lebensa daga maganganun yaudara.
Thi „den, som vil elske Livet og se gode Dage, skal holde sin Tunge fra ondt og sine Læber fra at tale Svig;
11 Ya rabu da mugunta ya aikata abin da ke nagari. Bari ya nemi zaman salama ya kuma dimanceta.
han vende sig fra ondt og gøre godt; han søge Fred og jage efter den!
12 Idanun Ubangiji suna duban adalai, kunnuwansa kuma suna sauraron roke rokensu. Amma fuskar Ubangiji tana gaba da masu aikata mugunta.”
Thi Herrens Øjne ere over de retfærdige, og hans Øren til deres Bøn; men Herrens Ansigt er over dem, som gøre ondt.”
13 Wanene ya isa ya cuce ku idan kun himmatu ga yin abin da ke nagari?
Og hvem er der, som kan volde eder ondt, dersom I ere nidkære for det gode?
14 Amma idan kuna shan wuya saboda adalci, ku masu albarka ne. Kada ku ji tsoron abin da su ke tsoro. Kada ku damu.
Men om I ogsaa maatte lide for Retfærdigheds Skyld, ere I salige. Nærer ingen Frygt for dem, og forfærdes ikke;
15 Maimakon haka, ku kebe Ubangiji a cikin zukatanku cewa shi mai tsarki ne. Kullum ku zauna da shiri domin ku amsa wa mai tambayar ku dalilin sa begenku ga Allah. Amma fa kuyi haka tare da tawali'u da bangirma.
men helliger den Herre Kristus i eders Hjerter, altid rede til at forsvare eder over for enhver, som kræver eder til Regnskab for det Haab, der er i eder, men med Sagtmodighed og Frygt,
16 Ku zama da tsatsakan lamiri domin mutanen da ke zargin rayuwarku mai kyau cikin Almasihu, su ji kunya domin suna maganar gaba da ku kamar ku mugaye ne.
idet I have en god Samvittighed, for at de, der laste eders gode Vandel i Kristus, maa blive til Skamme, naar de bagtale eder som Ugerningsmænd.
17 Ya fi kyau, a sha wuya akan aiki nagari, idan nufin Allah ne, da a sha wuya sabili da mugun aiki.
Thi det er bedre, om det saa er Guds Villie, at lide, naar man gør godt, end naar man gør ondt.
18 Almasihu ya sha wahala sau daya tak sabili da zunubai. Shi da ya ke mai adalci ya sha wahala domin mu marasa adalci, domin ya kawo mu ga Allah. Aka kashe shi cikin jiki, amma aka rayar da shi cikin Ruhu.
Thi ogsaa Kristus led een Gang for Synder, en retfærdig for uretfærdige, for at han kunde føre os hen til Gud, han, som led Døden i Kødet, men blev levendegjort i Aanden,
19 A Ruhu ne, ya je ya yi wa'azi ga ruhohin da ke a yanzu cikin kurkuku.
i hvilken han ogsaa gik hen og prædikede for Aanderne, som vare i Forvaring,
20 Sun yi rashin biyayya ne sa'adda hakurin Allah yake jiransu a lokacin Nuhu a zamanin sassaka jirgin ruwa, sai Allah ya tsirar da mutane kalilan wato rayuka takwas daga cikin ruwa.
som fordum vare genstridige, dengang Guds Langmodighed ventede i Noas Dage, medens Arken byggedes, i hvilken faa, nemlig otte, Sjæle bleve frelste igennem Vand,
21 Wannan kwatancin baftismar da take cetonmu yanzu ne, ba kamar ta wanke Dauda daga jiki ba, sai dai ta rokon Allah da lamiri mai kyau ta wurin tashin Yesu Almasihu daga matattu.
hvilket nu ogsaa frelser eder i sit Modbillede som Daab, der ikke er Fjernelse af Kødets Urenhed, men en god Samvittigheds Pagt med Gud ved Jesu Kristi Opstandelse,
22 Ya hau sama. Yana dama ga Allah. Mala'iku, da mulkoki da masu iko dole su yi masa biyayya.
han, som er faren til Himmelen og er ved Guds højre Haand, efter at Engle og Myndigheder og Kræfter ere ham underlagte.