< 1 Bitrus 2 >

1 Saboda haka sai ku tube dukkan keta, rikici, da riya, kishi, da dukkan mugun zance.
Putting away therefore all wickedness, all deceit, hypocrisies, envies, and all evil speaking,
2 Kammar jarirai, sababbin haihuwa, ku yi marmarin madara mai ruhaniya wadda take sahihiya, domin ta wurinta kuyi girma zuwa ceto,
as newborn babies, long for the pure spiritual milk, that with it you may grow,
3 idan kun dandana Ubangiji mai-alheri ne.
if indeed you have tasted that the Lord is gracious.
4 Kuzo gareshi rayayyen dutse wanda mutane suka ki, amma zababbe ne mai-daraja wurin Allah.
Come to him, a living stone, rejected indeed by men, but chosen by God, precious.
5 Ku kuma kamar rayayyun duwatsu ana gina ku gida mai ruhaniya, domin ku zama tsarka-kan fristoci, domin ku mika hadayu masu ruhaniya abin karba ga Allah ta wurin Yesu Almasihu.
You also as living stones are built up as a spiritual house, to be a holy priesthood, to offer up spiritual sacrifices, acceptable to God through Jesus Christ.
6 Gama nassi ya ce, “Ga shi na sanya dutse na kan kusurwa, zababe, mai daraja a cikin Sihiyona. Duk wanda ya bada gaskiya gareshi ba zaya kunyata ba.”
Because it is contained in Scripture, “Behold, I lay in Zion a chief cornerstone, chosen and precious. He who believes in him will not be disappointed.”
7 Daraja a gareku take ku da kun bada gaskiya. Amma, ga wadanda suka ki bada gaskiya, “Dutsen da magina suka ki shine aka mai she shi kan kusurwa”.
For you who believe therefore is the honour, but for those who are disobedient, “The stone which the builders rejected has become the chief cornerstone,”
8 kuma, “Dutsen sa tuntube da fa na sa tuntube. “Sun yi tuntube, da shike sun ki biyayya da maganar, an kuwa kaddara su ga wannan.
and, “a stumbling stone and a rock of offence.” For they stumble at the word, being disobedient, to which also they were appointed.
9 Amma ku zababben jinsi ne, kungiyar fristoci ba-sarauci, al'umma mai-tsarki, jama'ar mallakar Allah, domin ku sanar da mafifitan al'amuran wanda ya kiraye ku daga chikin duhu zuwa cikin haskensa mai'ban al'ajibi.
But you are a chosen race, a royal priesthood, a holy nation, a people for God’s own possession, that you may proclaim the excellence of him who called you out of darkness into his marvellous light.
10 Ku da ba jama'a ba ne a da, amma yanzu jama'ar Allah ne. Da baku sami jinkai ba, amma yanzu kun sami jinkai.
In the past, you were not a people, but now are God’s people, who had not obtained mercy, but now have obtained mercy.
11 Kaunatattu, ina rokon ku misalin baki da masu-tafiya kuma, ku guje wa sha'awoyin jiki wadanda ke yaki da rai.
Beloved, I beg you as foreigners and pilgrims to abstain from fleshly lusts which war against the soul,
12 Ku kasance da kyakkyawan hali a cikin al'ummai, domin, sa'adda suke kushen ku kamar masu aikata mugunta, sai su lura da nagargarun ayyukanku su kuma daukaka Allah a ranar zuwansa.
having good behaviour amongst the nations, so in that of which they speak against you as evildoers, they may see your good works and glorify God in the day of visitation.
13 Kuyi biyayya ga kowacce hukuma ta mutane sabili da Ubangiji, ko ga sarki domin shi ne shugaba.
Therefore subject yourselves to every ordinance of man for the Lord’s sake: whether to the king, as supreme,
14 Ko kuwa ga masu mulki aikakkunsa ne domin su hori masu aikata mugunta da yabawa masu aikata nagarta.
or to governors, as sent by him for vengeance on evildoers and for praise to those who do well.
15 Gama wannan nufin Allah ne, ta wurin aikin kirki ku, kwabi jahilcin mutane marassa hikima.
For this is the will of God, that by well-doing you should put to silence the ignorance of foolish men.
16 Kamar 'yan'tattu kada ku mori 'yan'cinku kamar mayafin mugunta, amma ku zama kamar bayin Allah.
Live as free people, yet not using your freedom for a cloak of wickedness, but as bondservants of God.
17 Ku girmama dukkan mutane. Ku kaunaci 'yan'uwa, kuji tsoron Allah. Ku girmama sarki.
Honour all men. Love the brotherhood. Fear God. Honour the king.
18 Ku barori, kuyi biyayya ga iyayen gidanku da dukkan bangirma, ba ga nagargaru da masu saukin kai ba, amma har ga miskilai.
Servants, be in subjection to your masters with all respect, not only to the good and gentle, but also to the wicked.
19 Gama abin yaba wa ne idan sabili da lamiri zuwa ga Allah in wani ya jimre da shan zalunci.
For it is commendable if someone endures pain, suffering unjustly, because of conscience towards God.
20 Gama wacce riba ke nan idan kun yi zunubi ana horonku kuna jimrewa da hukuncin? amma idan kunyi aikin kirki kuka sha wuya a kansa kuka yi hakuri, wannan abin karba ne wurin Allah.
For what glory is it if, when you sin, you patiently endure beating? But if when you do well, you patiently endure suffering, this is commendable with God.
21 Gama akan haka aka kiraye ku, gama Almasihu ma yasha azaba saboda ku, ya bar maku gurbi kubi sawunsa.
For you were called to this, because Christ also suffered for us, leaving you an example, that you should follow his steps,
22 Bai taba yin zunubi ba, ba'a taba jin yaudara a bakinsa ba.
who didn’t sin, “neither was deceit found in his mouth.”
23 Da'a ka zage shi bai mai da zagi ba. Da ya sha azaba, bai yi kashedi ba, amma ya mika kansa ga wanda yake yin shari'ar adalci.
When he was cursed, he didn’t curse back. When he suffered, he didn’t threaten, but committed himself to him who judges righteously.
24 Shi da kansa ya dauki zunubanmu a cikin jiki nasa ya kai su bisa itace, domin kada a iske mu cikin zunubi, amma muyi rayuwa ga adalci. Ta wurin raunukansa ne kuka warke.
He himself bore our sins in his body on the tree, that we, having died to sins, might live to righteousness. You were healed by his wounds.
25 Dukkanku da kun bata kuna yawo kamar batattun tumaki, amma yanzu kun dawo wurin makiyayi da mai tsaron rayukanku.
For you were going astray like sheep; but now you have returned to the Shepherd and Overseer of your souls.

< 1 Bitrus 2 >