< 1 Bitrus 1 >
1 Bitrus, manzon Yesu Almasihu, zuwa ga zababbu wadanda suke baki, a warwatse cikin Buntus, Galatiya, kappadokiya, Asiya, da Bitiniya.
Петр, апостол Ісуса Христа, вибраним захожанам розсїяння по Понту, Галатиї, Кападокиї, Азиї і Витиниї,
2 Bisa ga rigasanin Allah Uba, Ta wurin tsarkakewar Ruhu, zuwa biyayya da yayyafar jinin Yesu Almasihu. Alheri da salama su yawaita a gareku.
по провидінню Бога Отця, через осьвяченнє Духа, на послуханнє і кропленнє крові Ісус-Христової: Благодать вам і мир нехай намножить ся.
3 Albarka ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Almasihu. Ta wurin jinkansa mai girma, ya maya haihuwarmu zuwa bege mai rai ta wurin tashin Yesu Almasihu daga matattu.
Благословен Бог і Отець Господа нашого Ісуса Христа, що, по великій своїй милости, знов породив нас на впованнє живе воскресеннєм Ісус-Христовим із мертвих,
4 Zuwa gado marar lalacewa, marar baci, ba kuma zai kode ba. Wanda aka kebe a sama dominku.
до наслїддя нетлїнного і непорочного, що не зовяне, сховане на небесах про вас,
5 Ku da ikon Allah ya kiyaye ta wurin bangaskiya domin ceto wanda za'a bayyana a karshen zamanai.
котрі силою Божою стережені пробуваєте через віру, на спасеннє, готове явитись останнього часу.
6 Cikin wannan kuna murna da yawa, duk da ya ke ya zama wajibi gare ku yanzu ku yi bakin ciki, a cikin jarabobi iri iri.
Сим радуйте ся, мало нині (коли треба), смуткуючи у всяких напастях,
7 Wannan kuwa da nufin a iske aunawar bangaskiyarku ne, bangaskiyar da tafi zinariya daraja, wadda takan lalace ko da an gwada ta da wuta. Wannan ya faru domin bangaskiyan nan taku ta jawo maku yabo da girma da daukaka a bayyanuwar Yesu Almasihu.
щоб випробувана віра ваша, геть дорожча золота пропадущого, хоч і огнем випробуваного, знайшлась на похвалу і честь і славу в одкриттю Ісус-Христовому.
8 Wanda kuke kauna, ko da yake baku ganshi ba. Ko da yake baku ganinsa yanzu, duk da haka kun bada gaskiya gare shi murnar da ku ke yi kwarai da farin ciki wanda tafi gaban a fadi cike da daukaka.
Котрого не бачивши любите, і на котрого нині не дивлячись, а віруючи, радуєтесь радістю невимовною і преславною,
9 Kuna karbar sakamakon bangaskiyarku, ceton rayukanku.
приймаючи конець віри вашої, спасеннє душам.
10 Annabawan da su ka yi annabcin ceton da ya zama naku su ka yi bidassa suka bincike kuma da himma.
Про се ж то спасеннє розвідували і допитувались пророки, що про вашу благодать пророкували,
11 Sun nemi su san ko wanene da kuma kowanne lokaci ne Ruhun Almasihu da ke cikinsu yake bayyana ma su. Wannan ya faru ne sa'adda yake gaya ma su tun da wuri game da shan wahalar Almasihu da kuma daukakar da zata biyo baya.
дознаючись, якого або котрого часу являв у них Дух Христов, поперед сьвідкуючи про Христові страстї і про славу, що після них;
12 An kuwa bayyana wa annabawan cewa ba kansu suke hidimtawa ba, amma ku suke yi wa hidima. Wannan shine abin da suke yi game da abin da aka rigaya aka gaya maku, ta wurin wadanda da Ruhu mai Tsarki ya bishe su. Wanda aka aiko daga sama. Wadannan sune abubuwan da mala'iku ma suka yi marmarin a bayyana masu.
котрим відкрито, що не самим собі, а нам служили вони (тим), що нині звістили вам ті, котрі благовіствували вам Духом сьвятим, посланим із неба, (і) на що бажають ангели дивитись.
13 Domin wannan fa ku natsu. Ku yi dammara a hankalinku. Ku kafa begenku sarai akan alherin da za'a kawo maku a lokacin bayyanuwar Yesu Almasihu.
Тим то, підперезавши поясницї думок ваших, будьте тверезі, і звершено вповайте на благодать, що приносить ся вам в одкриттю Ісуса Христа.
14 Kamar 'ya'ya masu biyyaya, kada ku biyewa sha'awoyinku na da a zamanin jahilcinku.
Яко діти слухняні, не водячи себе по давнім хотїнням вашим, що в незнанню,
15 Amma yadda shi wanda ya kira ku mai tsarki ne, kuma ku zama da tsarki cikin dukkan al'amuranku.
а, яко Покликавший вас сьвятий, і. ви самі сьвяті у всьому життю будьте:
16 Domin a rubuce yake, “Ku zama da tsarki, gama ni mai tsarki ne.”
бо написано: "Будьте сьвяті, бо я сьвят."
17 Idan ku na kira bisa gare shi “Uba” shi wanda yake hukuntawa ba da tara ba, amma gwar-gwadon aikin kowane mutum, sai kuyi zaman bakuncinku da tsoro da bangirma.
І коли Отцем зовете Того, що, не вважаючи на лице, судить кожного по ділу, то Зo страхом провожайте час вашого домування,
18 Kun san cewa ba da azurfa ko zinariya mai lalacewa aka fanshe ku ba, daga halinn wauta da kuka gada daga wurin iyayenku.
знаючи, що не тлінним сріблом або золотом викупились од марного життя вашого, від отців переданого,
19 Maimakon haka an fanshe ku da jinin Almasihu mai daraja, marar aibu kamar na dan rago.
но дорогоцінною кровю Христа, як непорочного і чистого агнця,
20 An zabi Almasihu tun kafin kafawar duniya, amma a karshen zamanu ya bayyanu a gare ku.
призначеного перш настання сьвіта, обявленого в останнї часи задля вас,
21 Ku da kuka bada gaskiya ga Allah ta wurinsa, wanda ya tashe shi daga matattu ya kuma bashi daukaka domin bangaskiyarku da begenku su kasance cikin Allah.
що через Його віруєте в Бога, котрий воскресив Його з мертвих і дав Йому славу, щоб віра ваша і надія була на Бога.
22 Da shike kun tsarkake rayukanku cikin biyayyar ku ga gaskiya zuwa ga sahihiyar kauna ta 'yan'uwa, sai ku kaunaci junanku da zuciya mai gaskiya.
Душі ваші очистивши, в послусї правди Духом, на братню любов нелицемірну, із чистого серця любіте один одного щиро,
23 da shike an sake hai'huwarku ba daga iri mai lalacewa ba amma daga iri marar rubewa, ta wurin maganar Allah wadda take rayuwa ta kuma dawwama. (aiōn )
як народжені не з тлінного сїмя а з нетлїнного, через слово Бога живого і пробуваючого по вік. (aiōn )
24 Gama “dukkan jiki kamar ciyawa yake, dukkan darajarsa kuwa kamar furen ciyawa take. Ciyawa takan yi yaushi, furenta ya kan yankwane ya fadi,
Бо "всяке тіло, як трава, і всяка слава чоловіча, як цьвіт на траві: Зісохла трава і цьвіт її упав;
25 amma maganar Ubangiji tabbatacciya ce har abada. “Wannan ita ce maganar bishara wadda akayi maku wa'azinta.” (aiōn )
а слово Господнє пробував по вік." Се ж слово - благовіствововане між вами. (aiōn )