< 1 Yohanna 3 >

1 Dubi irin kaunar da Allah ya bamu, har da za a kira mu 'ya'yan Allah, haka muke kuwa. Saboda wannan dalili ne duniya bata san muba, saboda bata san shi ba.
視よ、父の我らに賜ひし愛の如何に大なるかを。我ら神の子と稱へらる。既に神の子たり、世の我らを知らぬは、父を知らぬによりてなり。
2 Kaunatattu, yanzu mu 'ya'yan Allahne, kuma ba a bayyana mana yadda zamu zama ba tukuna, mun sani sa'adda Almasihu zai bayyana, zamu zama kamarsa, domin zamu ganshi kamar yadda yake.
愛する者よ、我等いま神の子たり、後いかん、未だ顯れず、主の現れたまふ時われら之に肖んことを知る。我らその眞の状を見るべければなり。
3 Dukkan wanda yake da wannan bege game da gidan gobe ya kan tsarkake kansa, kamar yadda shima yake da tsarki.
凡て主による此の希望を懷く者は、その清きがごとく己を潔くす。
4 Dukkan wanda yaci gaba da yin zunubi yana ketare shari'a kenan. Gama zunubi ketare shari'a ne.
すべて罪をおこなふ者は不法を行ふなり、罪は即ち不法なり。
5 Kun sani Almasihu ya bayyana domin ya dauke zunubai ne. Kuma a cikinsa babu zunubi.
汝らは知る、主の現れ給ひしは罪を除かん爲なるを。主には罪あることなし。
6 Ba wanda zai kasance a cikinsa da zai cigaba da yin zunubi. Ba wanda zai ci gaba da aikata zunubi da zai ce ya sanshi, ko kuma ya ganshi.
おほよそ主に居る者は罪を犯さず、おほよそ罪を犯す者は未だ主を見ず、主を知らぬなり。
7 'Ya'yana kaunatattu, kada ku bari kowa ya baudar da ku, wanda yake aikata adalci shi adali ne, kamar yadda Almasihu yake adali.
若子よ、人に惑さるな、義をおこなふ者は義人なり、即ち主の義なるがごとし。
8 Wanda yake aikata zunubi na ibilis ne, gama ibilis yayi zunubi tun daga farko. Dalilin haka ne Dan Allah ya bayyana, domin ya rushe ayyukan ibilis.
罪を行ふものは惡魔より出づ、惡魔は初より罪を犯せばなり。神の子の現れ給ひしは、惡魔の業を毀たん爲なり。
9 Duk wanda aka haife shi daga Allah ba ya yin zunubi, saboda irin Allah na cikinsa. Ba zaya iya ci gaba da yin zunubi ba domin an haife shi daga wurin Allah.
凡て神より生るる者は罪を行はず、神の種、その衷に止るに由る。彼は神より生るる故に罪を犯すこと能はず。
10 Ta haka ne ake bambanta 'ya'yan Allah da 'ya'yan ibilis. Dukkan wanda baya aikata adalci ba na Allah bane; haka kuma wanda ba ya kaunar dan'uwansa.
之に由りて神の子と惡魔の子とは明かなり。おほよそ義を行はぬ者および己が兄弟を愛せぬ者は神より出づるにあらず。
11 Domin wannan shine sakon da kuka ji tun daga farko: cewa mu kaunaci junanmu,
われら互に相 愛すべきは汝らが初より聞きし音信なり。
12 ba kamar Kayinu ba wanda yake na shaidan kuma ya kashe dan'uwansa. Me yasa ya kashe shi? Saboda ayyukansa miyagu ne, na dan'uwansa kuma masu adalci ne.
カインに效ふな、彼は惡しき者より出でて己が兄弟を殺せり。何 故ころしたるか、己が行爲は惡しく、その兄弟の行爲は正しかりしに因る。
13 Kada kuyi mamaki 'yan'uwana, idan duniya ta ki ku.
兄弟よ、世は汝らを憎むとも怪しむな。
14 Mun sani mun ratsa mutuwa zuwa cikin rai, saboda muna kaunar 'yan'uwa. Dukkan wanda ba ya yin kauna, shi matacce ne.
われら兄弟を愛するによりて、死より生命に移りしを知る、愛せぬ者は死のうちに居る。
15 Dukkan wanda yake kin dan'uwansa, mai kisan kai ne. Kun kuma sani babu rai na har abada a cikin mai kisankai. (aiōnios g166)
おほよそ兄弟を憎む者は即ち人を殺す者なり、凡そ人を殺す者の、その内に永遠の生命なきを汝らは知る。 (aiōnios g166)
16 Ta wurin haka muka san kauna, da ya ke Almasihu ya bayar da ransa saboda mu. Mu ma ya kamata mu bada ranmu saboda 'yan'uwamu.
主は我らの爲に生命を捨てたまへり、之によりて愛といふことを知りたり、我等もまた兄弟のために生命を捨つべきなり。
17 Amma duk wanda yake da kayan duniya, ya ga dan'uwansa cikin bukata, kuma bai ji tausayinsa ba, ta yaya kaunar Allah ke cikinsa?
世の財寶をもちて兄弟の窮乏を見、反つて憐憫の心を閉づる者は、いかで神の愛その衷にあらんや。
18 'Ya'yana kaunatattu, kada muyi kauna ta fatar baki kawai, amma muyi aikin kauna da gaskiya.
若子よ、われら言と舌とをもて相 愛することなく、行爲と眞實とを以てすべし。
19 Ta wurin haka mun sani mu masu gaskiya ne kuma mun tabbatar da zuciyarmu a gabansa.
之に由りて我ら眞理より出でしを知り、且われらの心われらを責むとも神の前に心を安んずべし。
20 Gama idan zuciyarmu bata kayar damu ba, Allah ya fi zuciyarmu girma, kuma yana sane da kome.
神は我らの心よりも大にして一切のことを知り給へばなり。
21 Kaunatattu, idan zuciyarmu bata kashe mu ba, muna da gabagadi a gaban Allah.
愛する者よ、我らが心みづから責むる所なくば、神に向ひて懼なし。
22 Kuma duk abin da muka nema zamu samu a wurinsa, saboda muna kiyaye dokokinsa, muna yin abubuwan da suka gamshe shi.
且すべて求むる所を神より受くべし。是その誡命を守りて御心にかなふ所を行へばなり。
23 Kuma ummurninsa kenan: mu bada gaskiya ga sunan Dansa Yesu Almasihu, mu yi kaunar juna kuma kamar yanda ya bamu wannan doka.
その誡命はこれなり、即ち我ら神の子イエス・キリストの名を信じ、その命じ給ひしごとく互に相 愛すべきことなり。
24 Duk wanda yake kiyaye umarnin Allah, yana cikinsa, Allah kuma yana cikin mutumin. Ta haka muka gane cewa yana cikinmu, Ta wurin Ruhu, wanda ya bamu.
神の誡命を守る者は神に居り、神もまた彼に居給ふ。我らその賜ふところの御靈に由りて其の我らに居給ふことを知るなり。

< 1 Yohanna 3 >