< 1 Korintiyawa 6 >
1 Idan wani a cikin ku yana jayayya da wani, to sai ya tafi kotu gaban alkali marar bada gaskiya, a maimakon gaban masu bi?
2 Ko ba ku sani ba, masubi ne za su yiwa duniya shari'a? Kuma idan ku za ku yi wa duniya shari'a, sai ku kasa sasanta al'amura marasa mahimmanci?
3 Baku sani ba mu za mu yiwa mala'iku shari'a? Balle shari'ar al'amuran wannan rai?
4 Idan kuna shar'anta al'amuran yau da kullum, don me ku ke kai irin wadannan matsaloli gaban wadanda ba 'yan ikilisiya ba?
5 Na fadi wannan domin ku kunyata. Babu wani mai hikima a cikin ku ko daya da zai iya sasanta gardama a tsakanin 'yan'uwa?
6 Amma kamar yadda yake, mai bi ya na kai karar mai bi a kotu, kuma a gaban mai shari'a wanda ba mai bi ba!
7 Kasancewar rashin jituwa a tsakanin Kirista na nuna cewa kun rigaya kun gaza. Don me ba za ka shanye laifi ba? Don me ba za ka yarda a kware ka ba?
8 Amma kun yi wa wadansu laifi kun kuma cutar su, su kuwa 'yan'uwanku ne!
9 Ba ku sani ba marasa adalci ba za su gaji Mulkin Allah ba? Kada ku gaskata karya. Da fasikai, da masu bautar gumaka, da mazinata, da karuwai maza, da masu ludu,
10 da barayi, da masu zari, da mashaya, da masu zage-zage, da 'yan damfara - ba waninsu da zai gaji Mulkin Allah.
11 Kuma da haka wadansu a cikinku suke, amma an tsarkake ku, an mika ku ga Allah, an maida tsayuwar ku dai-dai a gaban Allah a cikin sunan Ubangji Yesu Almasihu, kuma ta wurin Ruhun Allahnmu.
12 Dukkan abu halal ne a gare ni”, amma ba kowanne abu ne mai amfani ba. “Dukan abu halal ne a gare ni,” amma ba zan yarda wani abu ya mallake ni ba.
13 “Abinci don ciki ne, kuma ciki don abinci ne”, amma Allah za ya kawar da su duka. Ba a yi jiki saboda fasikanci ba. Maimakon haka, jiki don Ubangiji ne, kuma Ubangiji zai yi wa jiki tanaji.
14 Allah ya tada Ubangiji, kuma za ya tashe mu ta wurin ikonsa.
15 Ba ku sani ba jikunanku gabobi ne na Almasihu? Na dauki gabobin Almasihu in hada su da karuwa? Allah ya sawwake!
16 Ko baku sani ba dukan wanda yake hade da karuwa, ya zama jiki daya da ita kenan?
17 Kamar yadda Littafi ya fadi, “Su biyun za su zama nama daya.” Amma wanda yake hade da Ubangiji ya zama ruhu daya da shi kenan.
18 Ku gujewa fasikanci! Kowane zunubi mutum yake aikatawa a waje da jikinsa yake, amma mutum mai fasikanci yana zunubi gaba da jikinsa.
19 Ba ku sani ba jikinku haikali ne na Ruhu Mai-tsarki, wanda yake zaune a cikinku, wanda ku ka samu daga wurin Allah? Ba ku sani ba cewa ku ba na kanku ba ne?
20 An saye ku da tsada. Don haka, ku daukaka Allah da jikin ku.