< 1 Korintiyawa 2 >
1 Lokacin da na zo wurin ku, yan'uwa, ban zo da gwanintar magana ko hikima ba yayinda na yi shelar boyayyun bayanai game da Allah [ a yayinda na bada shaida game da Allah].
And when I came to you, brothers, I came not to proclaim God’s great secret purpose in fine language of philosophy;
2 Domin na kudura a zuciyata kada in san komai lokacin da nake tare da ku, sai dai Yesu Almasihu, gicciyayye.
for I determined to know nothing, while among you, but Jesus as Christ, and him a crucified Christ.
3 Ina tare da ku cikin kasawa, da tsoro, da fargaba mai yawa.
In weakness and fear and great trembling came I among you.
4 Kuma sakona da shelata basu tare da kalmomin hikima masu daukar hankali. Maimakon haka, sun zo da bayyanuwar Ruhu da iko,
My message and my preaching were not in the persuasive language of philosophy, but in demonstration of the Spirit and of power;
5 saboda kada bangaskiyarku ta zama cikin hikimar mutane, amma cikin ikon Allah.
in order that your faith should rest, not on human philosophy, but on the power of God.
6 Yanzu muna maganar hikima ga wadanda suka ginu, amma ba hikima ta duniyan nan ba, ko ta masu mulkin wannan zamani, wadanda suke shudewa. (aiōn )
Notwithstanding, among those who are mature I do teach philosophy; though not the philosophy of the present age, nor of its rulers who are coming to nought. (aiōn )
7 Maimakon haka, muna maganar hikimar Allah ta boyayyar gaskiya, boyayyar hikima da Allah ya kaddara kafin zamanin daukakarmu. (aiōn )
No, it is God’s wisdom that I utter, that hidden wisdom which God had decreed before the world began, unto our glory. (aiōn )
8 Babu wani mai mulki na zamanin nan da ya san wannan hikimar, domin inda sun gane ta a wancan lokacin, da basu gicciye Ubangijin daukaka ba. (aiōn )
None of the rulers of the present age understands it, for if they had, they would not have crucified the Lord of Glory. (aiōn )
9 Amma kamar yadda yake a rubuce, “Abubuwan da babu idon da ya gani, babu kunnen da ya ji, babu zuciyar da ta yi tsammanin sa, abubuwan da Allah ya shirya wa wadanda suke kaunarsa.
Nay, as it is written. Eye has not seen, Nor ear heard, Neither have entered into man’s heart The things which God has prepared For those who love him.
10 Wadannan ne abubuwan da Allah ya bayyana mana ta wurin Ruhu. Gama Ruhu yana bincika komai, har ma abubuwa masu zurfi na Allah.
Yet God has unveiled them to us by his Spirit. For the Spirit fathoms everything, even the abysmal depths of God.
11 Gama wanene ya san tunanin mutum, sai dai ko ruhun mutumin da ke cikinsa? Haka ma, babu wanda ya san abubuwa masu zurfi na Allah sai dai Ruhun Allah.
For what man knows the depths of man except the man’s own inner Spirit? Even so, also, the Spirit of God knows the deeps profound of God.
12 Ba mu karbi ruhu na duniya ba, amma Ruhun da ya zo daga wurin Allah, domin mu san abubuwan da aka bamu a sake daga wurin Allah.
But we have not received the spirit of the world, but the Spirit which comes forth from God, that we may realize the blessings freely given us by God.
13 Muna maganar wadannan abubuwa da kalmomin da hikimar da mutum baza ta iya koyarwa ba, amma wadanda Ruhu ke koyar da mu. Ruhu yana fassara kalmomi na ruhaniya da hikima ta ruhaniya.
Of these high themes we speak in words not taught by human philosophy, but by the Spirit; interpreting spiritual things to spiritual men.
14 Mutum marar ruhaniya ba ya karbar abubuwan da suke daga Ruhun Allah, gama wauta suke a gareshi. Ba zai iya sanin su ba domin Ruhu ne yake bayyana su.
The unspiritual man rejects the teachings of God’s Spirit; for him it is folly. He cannot understand it, for it is spiritually discerned,
15 Shi wanda yake mai ruhaniya yana shari'anta dukan abubuwa, amma shi baya karkashin shari'ar sauran mutane.
But the spiritual man discerns everything, yet is himself discerned by no one.
16 “Wa zai iya sanin zuciyar Ubangiji, da zai iya ba shi umarni?” Amma mu muna da lamiri irin na Almasihu.
For what man understands the mind of the Lord, that he should instruct Him?