< 1 Korintiyawa 13 >

1 Koda ya zamanto ina magana da harsunan mutane, har ma da na mala'iku, amma kuma ba ni da kauna, na zama kamar kararrawa mai yawan kara, ko kuge mai amo.
εαν ταις γλωσσαις των ανθρωπων λαλω και των αγγελων αγαπην δε μη εχω γεγονα χαλκος ηχων η κυμβαλον αλαλαζον
2 Ko da ya zamanto ina da baiwar annabci kuma na fahimci dukkan boyayyar gaskiya, da dukkan ilimi, ko ina da matukar bangaskiya, har ma zan iya kawar da duwatsu. muddin ba ni da kauna, ni ba komai ba ne.
και εαν εχω προφητειαν και ειδω τα μυστηρια παντα και πασαν την γνωσιν και εαν εχω πασαν την πιστιν ωστε ορη μεθιστανειν αγαπην δε μη εχω ουδεν ειμι
3 Ko da ya zamanto na bayar da dukan mallakata domin a ciyar da matalauta, in kuma mika jikina domin a kona. Amma in ba ni da kauna, ban sami ribar komai ba. (Na bayar da jikina ne domin inyi fahariya.)
και εαν ψωμισω παντα τα υπαρχοντα μου και εαν παραδω το σωμα μου ινα καυθησομαι αγαπην δε μη εχω ουδεν ωφελουμαι
4 Kauna na da hakuri da kirki. kauna bata kishi ko fahariya. kauna ba ta girman kai
η αγαπη μακροθυμει χρηστευεται η αγαπη ου ζηλοι η αγαπη ου περπερευεται ου φυσιουται
5 ko fitsara. Bata bautar kanta. Bata saurin fushi, kuma bata ajiyar lissafin laifuffuka.
ουκ ασχημονει ου ζητει τα εαυτης ου παροξυνεται ου λογιζεται το κακον
6 Bata farin ciki da rashin adalci. A maimako, tana farin ciki da gaskiya.
ου χαιρει επι τη αδικια συγχαιρει δε τη αληθεια
7 Kauna tana jurewa cikin dukan abubuwa, tana gaskata dukan abubuwa, tana da yarda game da dukan abubuwa, tana daurewa dukan abubuwa.
παντα στεγει παντα πιστευει παντα ελπιζει παντα υπομενει
8 Kauna ba ta karewa. Idan akwai anabce anabce, zasu wuce. Idan akwai harsuna, zasu bace. Idan akwai ilimi, zaya wuce.
η αγαπη ουδεποτε εκπιπτει ειτε δε προφητειαι καταργηθησονται ειτε γλωσσαι παυσονται ειτε γνωσις καταργηθησεται
9 Domin muna da sani bisa - bisa kuma muna anabci bisa - bisa.
εκ μερους δε γινωσκομεν και εκ μερους προφητευομεν
10 Sa'adda cikakke ya zo, sai marar kammalar ya wuce.
οταν δε ελθη το τελειον τοτε το εκ μερους καταργηθησεται
11 Da nake yaro, nakan yi magana irinta kuruciya, nakan yi tunani irin na kuruciya, nakan ba da hujjojina irin na kuruciya. Da na isa mutum na bar halayen kuruciya.
οτε ημην νηπιος ως νηπιος ελαλουν ως νηπιος εφρονουν ως νηπιος ελογιζομην οτε δε γεγονα ανηρ κατηργηκα τα του νηπιου
12 Gama yanzu muna gani sama - sama kamar ta madubi, amma a ranar fuska da fuska, yanzu na sani bisa - bisa, amma a lokacin zan sami cikakken sani kamar yadda aka yi mani cikakken sani.
βλεπομεν γαρ αρτι δι εσοπτρου εν αινιγματι τοτε δε προσωπον προς προσωπον αρτι γινωσκω εκ μερους τοτε δε επιγνωσομαι καθως και επεγνωσθην
13 To, a yanzu abubuwan nan uku sun tabbata: bangaskiya, da gabagadi mai zuwa, da kuma kauna, amma duk mafi girma a cikinsu ita ce kauna.
νυνι δε μενει πιστις ελπις αγαπη τα τρια ταυτα μειζων δε τουτων η αγαπη

< 1 Korintiyawa 13 >