< 1 Korintiyawa 12 >
1 Game da baye bayen Ruhu Mai Tsarki 'yan'uwa, bana so ku zama da jahilci.
de spiritalibus autem nolo vos ignorare fratres
2 Kun san cewa lokacin da ku ke al'ummai, an rude ku da alloli marasa magana ta hanyoyi dabam dabam marasa kan gado.
scitis quoniam cum gentes essetis ad simulacra muta prout ducebamini euntes
3 Saboda haka ina so ku sani babu wanda ya ke magana da Ruhun Allah da zai ce, “Yesu la'ananne ne.” Babu kuma wanda zaya ce, “Yesu Ubangili ne,” sai dai ta Ruhu Mai Tsarki.
ideo notum vobis facio quod nemo in Spiritu Dei loquens dicit anathema Iesu et nemo potest dicere Dominus Iesus nisi in Spiritu Sancto
4 Akwai bay bye iri iri, amma Ruhu daya ne.
divisiones vero gratiarum sunt idem autem Spiritus
5 Akwai hidimomi iri iri, amma Ubangiji daya ne.
et divisiones ministrationum sunt idem autem Dominus
6 Akwai aikace aikace iri iri, amma Allah daya ke bayyanawa kowane mutum yadda zai aiwatar da su.
et divisiones operationum sunt idem vero Deus qui operatur omnia in omnibus
7 To ga kowanne an bayar da ikon nuna ayyukan Ruhu a fili domin amfanin kowa.
unicuique autem datur manifestatio Spiritus ad utilitatem
8 Ga wani ta wurin Ruhu an bayar da baiwar hikima, kuma ga wani kalmar sani ta wurin Ruhu daya.
alii quidem per Spiritum datur sermo sapientiae alii autem sermo scientiae secundum eundem Spiritum
9 Ga wani an ba shi baiwar bangaskiya ta wurin Ruhun nan, ga wani kuwa an ba shi baiwar warkarwa ta wurin wannan Ruhun.
alteri fides in eodem Spiritu alii gratia sanitatum in uno Spiritu
10 Ga wani yin ayyukan iko, ga wani kuwa annabci. Ga wani kuwa an ba shi baiwar bambance ruhohi, ga wani harsuna daban daban, kuma ga wani fassarar harsuna.
alii operatio virtutum alii prophetatio alii discretio spirituum alii genera linguarum alii interpretatio sermonum
11 Dukan wadannan Ruhu daya ne ya ke iza su, ya kuma rarraba baye bayen ga kowannen su yadda ya nufa.
haec autem omnia operatur unus atque idem Spiritus dividens singulis prout vult
12 Kamar yadda jiki daya ne amma da gabobi da yawa kuma duk gabobin na jiki daya ne, haka nan Almasihu yake.
sicut enim corpus unum est et membra habet multa omnia autem membra corporis cum sint multa unum corpus sunt ita et Christus
13 Gama ta Ruhu daya aka yi wa kowa baftisma cikin jiki daya, ko Yahudawa ko al'ummai, ko bayi ko 'ya'ya, dukan mu kuwa an shayar da mu Ruhu daya.
etenim in uno Spiritu omnes nos in unum corpus baptizati sumus sive Iudaei sive gentiles sive servi sive liberi et omnes unum Spiritum potati sumus
14 Gama jiki ba daya ba ne sungun, amma gabobi ne da yawa.
nam et corpus non est unum membrum sed multa
15 Idan kafa ta ce, “tun da dai ni ba hannu ba ne to ni ba fannin jikin bane,” wannan baya rage masa matsayin sa a jikin ba.
si dixerit pes quoniam non sum manus non sum de corpore non ideo non est de corpore
16 Kuma da kunne zaya ce, '''Da yake ni ba ido ba ne, ai, ni ba gabar jiki ba ne,'' fadar haka ba za ta raba shi da zama gabar jikin ba.
et si dixerit auris quia non sum oculus non sum de corpore non ideo non est de corpore
17 Idan dukan jikin ya kasance ido ne da me za a ji? Da dukan jikin kunne ne, da me za a sunsuna?
si totum corpus oculus ubi auditus si totum auditus ubi odoratus
18 Amma Allah ya shirya gabobin jiki bisa ga tsarin sa.
nunc autem posuit Deus membra unumquodque eorum in corpore sicut voluit
19 Amma da duk jiki gaba daya ce, da ina jikin zai kasance?
quod si essent omnia unum membrum ubi corpus
20 Ga shi akwai gabobi da yawa, kuma jiki daya ne.
nunc autem multa quidem membra unum autem corpus
21 Ba da ma ido ya fadawa hannu, ''Bana bukatar ka,'' ko kuma kai ya fadawa kafafu, ''Ba na bukatar ku.''
non potest dicere oculus manui opera tua non indigeo aut iterum caput pedibus non estis mihi necessarii
22 Amma, sai ma gabobin da ake gani kamar raunannu su ne masu humimmanci, gabobin jiki kuwa da ake gani kamar sun kasa sauran daraja, mu kan fi ba su martaba.
sed multo magis quae videntur membra corporis infirmiora esse necessariora sunt
23 Ta haka gabobinmu marasa kyan gani, akan kara kyautata ganinsu. Gabobin mu masu kyan kuma ba sai an yi masu ado ba.
et quae putamus ignobiliora membra esse corporis his honorem abundantiorem circumdamus et quae inhonesta sunt nostra abundantiorem honestatem habent
24 Amma Allah ne da kansa ya hada jiki, yana bada mafificiyar martaba ga kaskantacciyar gaba.
honesta autem nostra nullius egent sed Deus temperavit corpus ei cui deerat abundantiorem tribuendo honorem
25 Yayi haka ne domin kada a sami tsattsaguwa a cikn jikin, amma domin gabobin su kula da juna da matsananciyar lura.
ut non sit scisma in corpore sed id ipsum pro invicem sollicita sint membra
26 Kuma idan gaba daya na wahala, dukan gabobin suna wahala tare. ko kuma idan an girmama gaba daya, dukan gabobin na farin ciki tare.
et si quid patitur unum membrum conpatiuntur omnia membra sive gloriatur unum membrum congaudent omnia membra
27 Yanzu ku jikin Almasihu ne, saboda haka kuma kowannen ku gabarsa ne.
vos autem estis corpus Christi et membra de membro
28 A cikin ikilisiya, Allah ya sa wasu su zama, na farko manzanni, na biyu annabawa, na uku masu koyarwa, sa'an nan sai masu yin ayyukan iko, sai masu aikin warkarwa, da masu bayar da taimako, da masu aikin tafiyar da al'amura, da masu harsuna daban daban.
et quosdam quidem posuit Deus in ecclesia primum apostolos secundo prophetas tertio doctores deinde virtutes exin gratias curationum opitulationes gubernationes genera linguarum
29 To kowa manzo ne? ko kuwa duka annabawa ne? ko kuma duka masu koyarwa ne? Kowa ne ke yin manyan ayyukan iko?
numquid omnes apostoli numquid omnes prophetae numquid omnes doctores
30 Ko kuwa dukan su ne suke da baiwar warkarwa? Dukan su ne ke magana da harsuna? ko kuma dukan su ne ke fassara harsuna?
numquid omnes virtutes numquid omnes gratiam habent curationum numquid omnes linguis loquuntur numquid omnes interpretantur
31 Amma bari ku himmantu ga neman baiwa mafi girma. Kuma zan nuna maku wata hanya mafificiya.
aemulamini autem charismata maiora et adhuc excellentiorem viam vobis demonstro