< 1 Korintiyawa 11 >
1 Ku yi koyi da ni, kamar yadda nake koyi da Almasihu.
Be imitators of me, in so far as I in turn am an imitator of Christ.
2 Yanzu ina yaba maku ne, don kuna tunawa da ni cikin abu duka. Ina kuma yaba maku wajen bin al'adun da na ba ku daidai yadda na ba ku.
Now I commend you for remembering me in everything, and because you hold fast truths and practices precisely as I have taught them to you.
3 Amma fa ina son ku fahimta da cewa, shugaban kowane mutum Almasihu ne, shugaban kowace mace mutumin ne, shugaban Almasihu Allah ne.
I would have you know, however, that of every man, Christ is the Head, that of a woman her husband is the Head, and that God is Christ's Head.
4 Kuma duk mutumin da ya yi addu'a ko annabci kansa a rufe, ya wulakanta shugabansa.
A man who wears a veil when praying or prophesying dishonors his Head;
5 Amma duk macen da ta yi addu'a ko annabci kanta a bude, ta wulakanta shugabanta. Gama yayi dai dai da idan tayi aski.
but a woman who prays or prophesies with her head uncovered dishonors her Head, for it is exactly the same as if she had her hair cut short.
6 Gama idan mace ba zata rufe kanta ba, to ta yanke gashinta ya zama gajere. Idan abin kunya ne mace ta yanke gashinta ko ta aske kanta, bari ta rufe kanta.
If a woman will not wear a veil, let her also cut off her hair. But since it is a dishonor to a woman to have her hair cut off or her head shaved, let her wear a veil.
7 Bai kamata na miji ya rufe kansa ba, tun da yake shi siffa ne da daukakar Allah. Amma mace daukakar namiji ce.
For a man ought not to have a veil on his head, since he is the image and glory of God; while woman is the glory of man.
8 Don kuwa namiji ba daga jikin mace yake ba. A maimako, matar daga jikin namiji take.
Man does not take his origin from woman, but woman takes hers from man.
9 Ba a kuma halicci namiji don mace ba. A maimako, an halicci mace don namiji.
For man was not created for woman's sake, but woman for man's.
10 Shi ya sa mace za ta kasance da alamar iko a kanta, saboda mala'iku.
That is why a woman ought to have on her head a symbol of subjection, because of the angels.
11 Duk da haka, a cikin Ubangiji, mace ba a rabe take da namiji ba, haka kuma namiji ba a rabe yake da mace ba.
Yet, in the Lord, woman is not independent of man nor man independent of woman.
12 Kamar yadda mace take daga namiji, haka ma namiji kuma haihuwar mace ne. Amma dukkan abubuwa daga Allah suke.
For just as woman originates from man, so also man comes into existence through woman, but everything springs originally from God.
13 Ku hukunta da kanku: Daidai ne mace ta yi addu'a ga Allah kanta a bude?
Judge of this for your own selves: is it seemly for a woman to pray to God when she is unveiled?
14 Ashe, ko dabi'a bata nuna maku cewa abin kunya ne namiji, ya kasance da dogon gashi ba?
Does not Nature itself teach you that if a man has long hair it is a dishonor to him,
15 Ba dabi'a ta koya maku cewa idan mace tana da dogon gashi, daukakar ta ne ba? Gama domin rufewa aka yi mata baiwar gashin.
but that if a woman has long hair it is her glory, because her hair was given her for a covering?
16 To idan wani yana da niyyaryin gardama game da wannan, mu dai bamu da wata al'adar, ikilisiyoyin Allah kuma haka.
But if any one is inclined to be contentious on the point, we have no such custom, nor have the Churches of God.
17 Amma game da umarnin dake biye, ban yaba maku ba, taruwarku ba ta kirki ba ce, ta rashin gaskiya ce.
But while giving you these instructions, there is one thing I cannot praise--your meeting together, with bad rather than good results.
18 Farko dai sa'adda kuke, taron ikklisiya, na ji har akwai rarrabuwa tsakaninku, har na fara amincewa da maganar.
for, in the first place, when you meet as a Church, there are divisions among you. This is what I am told, and I believe that there is some truth in it.
19 Dole ne a sami tsattsaguwa a tsakaninku, don a iya gane wadanda suke amintattu a cikinku.
For there must of necessity be differences of opinion among you, in order that it may be plainly seen who are the men of sterling worth among you.
20 Domin, in kun taru a wuri daya, ba jibin Ubangiji kuke ci ba!
When, however, you meet in one place, there is no eating the Supper of the Lord;
21 Ya yin da kuke ci, kowa na cin abincinsa ne kamin sauran Wani yana jin yunwa, wani kuma ya zarin ci, har ya bugu.
for it is his own supper of which each of you is in a hurry to partake, and one eats like a hungry man, while another has already drunk to excess.
22 Baku da gidajen da zaku ci ku sha, kuna raina ikkilisiyar Allah, kuna kuma wulakanta wa wadanda basu da komai? To, me zan ce maku? Yaba maku zan yi? Ba zan yaba maku ba akan wannan.
Why, have you no homes in which to eat and drink? Or do you wish to show your contempt for the Church of God and make those who have no homes feel ashamed? What shall I say to you? Shall I praise you? In this matter I certainly do not praise you.
23 Amma abin da na karba a gun Ubangiji shi nake baku cewa Ubangiji Yesu, a daren da aka bashe shi ya dauki gurasa.
For it was from the Lord that I received the facts which, in turn, I handed on to you; how that the Lord Jesus, on the night He was to be betrayed, took some bread,
24 Bayan ya yi godiya, sai ya kakkarya ya ce, “wanna shi ne jikina wanda yake saboda ku, ku yi domin tunawa da ni.”
and after giving thanks He broke it and said, "This is my body which is about to be broken for you. Do this in memory of me."
25 Ta wannan hanya kuma, sai ya dauki kokon, ya ce, “kokon nan na sabon alkawari ne, da aka tabbatar da shi da cikin jinina. Ku yi haka kuna sha don tunawa da ni.”
In the same way, when the meal was over, He also took the cup. "This cup," He said, "is the new Covenant of which my blood is the pledge. Do this, every time that you drink it, in memory of me."
26 Duk sa'adda kuke cin gurasar nan, kuna kuma sha cikin kokon nan, kuna bayyana mutuwar Ubangiji ke nan, har sai ya dawo.
For every time that you eat this bread and drink from the cup, you are proclaiming the Lord's death--until He returns.
27 Saboda haka duk wanda ya ci gurasar nan, ko ya sha a cikin kokon nan, na Ubangiji da rashin cancanta, ya yi laifin wulakanta jikin Ubangiji da jininsa.
Whoever, therefore, in an unworthy manner, eats the bread or drinks from the cup of the Lord sins against the body and blood of the Lord.
28 Sai kowa ya fara auna kansa, kafin ya ci gurasar, ya kuma sha a cikin kokon nan.
But let a man examine himself, and, having done that, then let him eat the bread and drink from the cup.
29 In kowa ya ci, ya sha ba tare da rarrabewa da jikin Ubangiji ba, lalle ya jawowa kansa hukunci, ta wurin ci da sha da ya yi.
For any one who eats and drinks, eats and drinks judgement to himself, if he fails to estimate the body aright.
30 Shi ya sa da yawa a cikin ku suke raunana, kuma suna fama da rashin lafiya, har ma wasun ku da dama suka yi barci.
That is why many among you are sickly and out of health, and why not a few die.
31 Amma, in mun auna kanmu, ba a za a hukunta mu ba.
If, however, we estimated ourselves aright, we should not be judged.
32 In kuwa Ubangiji ne ya ke hukunta mu, To, muna horuwa ke nan, don kada a kayar damu tare da duniya.
But when we are judged by the Lord, chastisement follows, to save us from being condemned along with the world.
33 Saboda haka, ya ku 'yan'uwana, idan kuka tattaru don cin abinci, sai ku jira juna.
Therefore, brethren, when you come together for this meal, wait for one another.
34 Idan kuwa wani yana jin yunwa, ya ci a gida, kada ya zama taronku ya jawo maku hukunci. Batun sauran abubuwan da kuka rubuta kuwa, zan ba da umarni a kai sa'ad da na zo.
If any one is hungry, let him eat at home; so that your coming together may not lead to judgement. The other matters I will deal with whenever I come.