< 1 Korintiyawa 1 >
1 Bulus, kirayayye daga Almsihu Yesu don zama manzo ta wurin nufin Allah, da dan'uwanmu Sastanisu,
2 zuwa ga Ikilisiyar Allah da ke korinti, zuwa ga wadanda aka kebe su cikin Almasihu Yesu, wadanda aka kira domin su zama al'umma maitsarki. Muna kuma rubuta wa dukan masu kira bisa sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu a ko'ina, wato Ubangijinsu da Ubangijinmu kuma.
3 Bari alheri da salama su zo gare ku daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Almasihu.
4 Kodayaushe ina gode wa Allahna domin ku, saboda alherin Allah da Almasihu Yesu ya yi maku.
5 Ya ba ku arziki ta kowace hanya, cikin dukkan magana da dukkan ilimi.
6 Kamar yadda shaida game da Almasihu ta tabbata gaskiya a tsakaninku.
7 Saboda haka baku rasa wata baiwa ta ruhaniya ba yayinda kuke marmarin jiran bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Almasihu.
8 Zai kuma karfafa ku zuwa karshe, saboda ku zama marasa aibi a ranar Ubangijinmu Yesu Almasihu.
9 Allah mai aminci ne shi wanda ya kira ku zuwa zumunta ta Dansa, Yesu Almasihu Ubangijimu.
10 Ina rokon ku, yan'uwa, cikin sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, ku yarda da juna, kada tsattsaguwa ta kasance tsakanin ku. Ina rokon ku ku zama da zuciya daya da kuma nufi daya.
11 Gama mutanen gidan Kulowi sun kawo kara cewa akwai tsattsaguwa a cikin ku.
12 Ina nufin: kowannen ku na cewa, “Ina bayan Bulus,” ko “Ina bayan Afollos,” ko “Ina bayan Kefas,” ko “Ina bayan Almasihu.”
13 Almasihu a rarrabe yake? An gicciye Bulus domin ku? Ko an yi maku baftisma a cikin sunan Bulus?
14 Na godewa Allah domin ban yi wa wanin ku baftisma ba, sai dai Kirisfus da Gayus.
15 Na yi wannan saboda kada wani ya ce an yi maku baftisma a cikin sunana.
16 (Na kuma yi wa iyalin gidan Sitifanas baftisma. Banda haka, ban sani ko na yi wa wani baftisma ba.)
17 Gama Almasihu bai aiko ni domin yin baftisma ba, amma domin yin wa'azin bishara. Bai aiko ni domin in yi wa'azi da kalmomin hikimar mutum ba, saboda kada giciyen Almasihu ya rasa ikonsa.
18 Gama wa'azin gicciye wauta ne ga wadanda su ke mutuwa. Amma cikin wadanda Allah ke ceto, ikon Allah ne.
19 Gama a rubuce yake, “Zan watsar da hikimar masu hikima. Zan dode fahimtar masu basira.”
20 Ina mai hikima? Ina masani? Ina mai muhawara na duniyan nan? Allah bai juya hikimar duniya zuwa wauta ba? (aiōn )
21 Tunda duniya cikin hikimarta bata san Allah ba, ya gamshi Allah ta wurin wautar wa'azi ya ceci masu bada gaskiya.
22 Gama Yahudawa suna bidar al'ajibai, Helinawa kuma suna neman hikima.
23 Amma muna wa'azin Almasihu gicciyayye, dutsen tuntube ga yahudawa da kuma wauta ga Helinawa.
24 Amma ga wadanda Allah ya kira, Yahudawa da Helinawa, muna wa'azin Almasihu a matsayin iko da kuma hikimar Allah.
25 Gama wautar Allah tafi mutane hikima, kuma rashin karfin Allah yafi mutane karfi.
26 Dubi kiranku, yan'uwa. Ba dukkan ku ke da hikima a ma'aunin mutane ba. Ba dukkan ku ke da iko ba. Ba dukkan ku ke da haifuwa ta sarauta ba.
27 Amma Allah ya zabi abubuwan da suke wofi na duniya domin ya kunyatar da masu hikima. Allah ya zabi abin da ke marar karfi a duniya domin ya kunyatar da abinda ke mai karfi.
28 Allah ya zabi abinda ke marar daraja da kuma renanne a duniya. Ya ma zabi abubuwan da ake dauka ba komai ba, domin ya wofinta abubuwan da ake dauka masu daraja.
29 Ya yi wannan ne domin kada wani ya sami dalilin fahariya a gabansa.
30 Domin abinda Allah ya yi, yanzu kuna cikin Almasihu Yesu, wanda ya zamar mana hikima daga Allah. Ya zama adalcinmu, da tsarkinmu da fansarmu.
31 A sakamakon haka, kamar yadda nassi ya ce, “Bari mai yin fahariya, ya yi fahariya cikin Ubangiji.”