< Zefaniya 2 >
1 Ku tattaru, ku tattaru, Ya ku al’umma marar kunya,
2 kafin ƙayyadadden lokacin nan yă zo ranan nan kuma ta share ku kamar ƙaiƙayi kuma kafin fushi mai tsanani na Ubangiji yă auko muku, kafin ranar fushin Ubangiji ta auko muku.
3 Ku nemi Ubangiji, dukanku ƙasashe masu tawali’u, ku da kuke yin abin da ya umarta. Ku nemi adalci da tawali’u; mai yiwuwa ku sami mafaka a ranar fushin Ubangiji.
4 Za a yashe Gaza a kuma bar Ashkelon kango. Da tsakar rana Ashdod za tă zama babu kowa a kuma tumɓuke Ekron.
5 Taku ta ƙare ku da kuke zama a bakin teku, Ya ku mutanen Keretawa; maganar Ubangiji tana gāba da ke, Ya ke Kan’ana, ƙasar Filistiyawa. “Zan hallaka ki kuma babu abin da zai rage.”
6 Ƙasar da take a bakin teku, inda Keretawa suke zaune, za tă zama wurin da makiyaya da ta garken tumaki.
7 Za tă zama mallakar raguwar gidan Yahuda; a can za su sami wurin kiwo. Da yamma za su kwanta a gidajen Ashkelon. Ubangiji Allahnsu zai lura da su; zai maido musu da martabarsu.
8 “Na ji irin zagin da Mowab take yi, da kuma ba’ar Ammonawa, waɗanda suka zagi mutanena suna kuma yi barazana a kan ƙasarsu.
9 Saboda haka, muddin ina raye,” in ji Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, “tabbatacce Mowab za tă zama kamar Sodom, Ammonawa kuma kamar Gomorra, ƙasa mai ciyayi da rammukan gishiri, ƙasa marar amfani har abada. Raguwar mutanena za su washe su; waɗanda suka rage na al’ummata za su gāda ƙasarsu.”
10 Wannan ne zai zama sakamakon girmankansu, saboda zagi da kuma ba’ar da suka yi wa mutanen Ubangiji Maɗaukaki.
11 Ubangiji zai zama abin tsoro a gare su sa’ad da ya hallaka allolin ƙasar. Al’ummai a kowane bakin teku za su yi masa sujada, kowa a ƙasarsa.
12 “Ku ma, ya Kushawa, za a kashe ku da takobina.”
13 Zai kuma miƙa hannunsa gāba da arewa yă kuma hallaka Assuriya, zai mai da Ninebe kango gaba ɗaya ta kuma zama busasshiya kamar hamada.
14 Garkuna za su kwanta a can, da kowace irin halitta, Mujiyar hamada da bushiya za su zauna a kan ginshiƙanta. Kukansu za tă ratsa tagogi, ɓuraguzai za su tare ƙofofin shiga, za a kware ginshiƙan al’ul.
15 Birnin da yake harka ke nan da take zaune lafiya. Ta ce wa kanta, “Ni ce, kuma babu kamata.” Dubi irin kangon da ta zama mana, mazaunin namun jeji! Duk wanda ya wuce ta sai ya yi mata tsaki yana kaɗa kai.