< Zakariya 9 >

1 Annabci. Maganar Ubangiji tana gāba da ƙasar Hadrak za tă kuma sauko a kan Damaskus, gama idanun dukan mutane da na kabilan Isra’ila suna a kan Ubangiji,
משא דבר יהוה בארץ חדרך ודמשק מנחתו כי ליהוה עין אדם וכל שבטי ישראל
2 da kuma a kan Hamat ita ma, wadda ta yi iyaka da ita, da kuma a kan Taya da Sidon, ko da yake suna da hikima ƙwarai.
וגם חמת תגבל בה צר וצידון כי חכמה מאד
3 Taya ta gina wa kanta mafaka mai ƙarfi; ta tara azurfa kamar ƙasa, zinariya kuma kamar tarin shara a tituna.
ותבן צר מצור לה ותצבר כסף כעפר וחרוץ כטיט חוצות
4 Amma Ubangiji zai karɓe mallakarta, zai hallaka ikonta da take da shi a kan teku, wuta kuma za tă cinye ta.
הנה אדני יורשנה והכה בים חילה והיא באש תאכל
5 Ashkelon za tă ga haka ta ji tsoro; Gaza za tă yi birgima cikin azaba, haka Ekron ma, gama za tă fid da zuciya. Gaza za tă rasa sarkinta za a kuma gudu a bar Ashkelon.
תרא אשקלון ותירא ועזה ותחיל מאד ועקרון כי הביש מבטה ואבד מלך מעזה ואשקלון לא תשב
6 Baƙi za su mallaki Ashdod, kuma zan kawar da girman kan Filistiyawa.
וישב ממזר באשדוד והכרתי גאון פלשתים
7 Zan kawar da jini daga bakinsu, zan kuma cire abincin da aka haramta daga tsakanin haƙoransu. Waɗanda za a bari za su zama na Allahnmu, su kuma zama shugabanni a Yahuda, Ekron kuma za tă zama kamar Yebusiyawa.
והסרתי דמיו מפיו ושקציו מבין שניו ונשאר גם הוא לאלהינו והיה כאלף ביהודה ועקרון כיבוסי
8 Amma zan kāre gidana daga sojoji masu kai da kawowa. Azzalumi ba zai ƙara cin mutanena da yaƙi ba, gama yanzu ina tsaro.
וחניתי לביתי מצבה מעבר ומשב ולא יעבר עליהם עוד נגש כי עתה ראיתי בעיני
9 Ki yi murna ƙwarai, ya Diyar Urushalima! Ki yi sowa, Diyar Urushalima! Duba, ga sarkinki yana zuwa wurinki, mai adalci yana kuma da ceto, mai tawali’u yana kuma hawan jaki, yana a kan ɗan aholaki, a kan’yar jaka.
גילי מאד בת ציון הריעי בת ירושלם הנה מלכך יבוא לך צדיק ונושע הוא עני ורכב על חמור ועל עיר בן אתנות
10 Zan ƙwace kekunan yaƙi daga Efraim, da kuma dawakan yaƙi daga Urushalima, za a kuma karya bakan yaƙi. Zai yi shelar salama ga al’ummai. Mulkinsa zai yaɗu daga teku zuwa teku, daga Kogi kuma zuwa ƙarshen duniya.
והכרתי רכב מאפרים וסוס מירושלם ונכרתה קשת מלחמה ודבר שלום לגוים ומשלו מים עד ים ומנהר עד אפסי ארץ
11 Ke kuma, saboda jinin alkawarina da ke, zan’yantar da’yan kurkukunki daga rami marar ruwa.
גם את בדם בריתך שלחתי אסיריך מבור אין מים בו
12 Ku koma maɓuya, ya ku’yan kurkuku masu sa zuciya; ko yanzu ma na sanar cewa zan mayar muku ninki biyu.
שובו לבצרון אסירי התקוה גם היום מגיד משנה אשיב לך
13 Zan lanƙwasa Yahuda yadda nake lanƙwasa bakana, in kuma cika ta da Efraim kamar kibiya. Zan tā da’ya’yanki maza, ya Sihiyona, gāba da’ya’yanki, ya Girka, in kuma mai da ke kamar takobin jarumin yaƙi.
כי דרכתי לי יהודה קשת מלאתי אפרים ועוררתי בניך ציון על בניך יון ושמתיך כחרב גבור
14 Sa’an nan Ubangiji zai bayyana a bisansu; kibiyarsa za tă wulga kamar walƙiya. Ubangiji Mai Iko Duka zai busa ƙaho; zai taho ta cikin guguwa daga kudu,
ויהוה עליהם יראה ויצא כברק חצו ואדני יהוה בשופר יתקע והלך בסערות תימן
15 Ubangiji Maɗaukaki kuma zai tsare su. Za su hallakar su kuma yi nasara da duwatsun majajjawa. Za su sha su yi kururuwa kamar sun sha ruwan inabi; za su cika kamar kwanon da ake amfani don a yayyafa jini a kusurwoyin bagade.
יהוה צבאות יגן עליהם ואכלו וכבשו אבני קלע ושתו המו כמו יין ומלאו כמזרק--כזויות מזבח
16 Ubangiji Allahnsu zai cece su a wannan rana gama su mutanensa ne da kuma garkensa. Za su haska a cikin ƙasarsa kamar lu’ulu’u a rawani.
והושיעם יהוה אלהיהם ביום ההוא--כצאן עמו כי אבני נזר מתנוססות על אדמתו
17 Za su yi kyan gani da kuma bansha’awa! Hatsi zai sa samari su yi murna, sabon ruwan inabi kuma zai sa’yan mata su yi farin ciki.
כי מה טובו ומה יפיו--דגן בחורים ותירוש ינובב בתלות

< Zakariya 9 >