< Zakariya 2 >
1 Sa’an nan na ɗaga kai sai na ga mutum a tsaye riƙe da ma’auni a hannunsa!
And lifting up my eyes, I saw a man with a measuring-line in his hand.
2 Sai na yi tambaya, na ce, “Ina za ka?” Ya amsa mini ya ce, “Zan je in auna Urushalima, in ga yadda fāɗinta da tsawonta suke.”
And I said to him, Where are you going? And he said to me, To take the measure of Jerusalem, to see how wide and how long it is.
3 Sai mala’ikan da yake yi mini magana ya tafi, sai wani mala’ika ya zo ya same shi
And the angel who was talking to me went out, and another angel went out, and, meeting him,
4 ya ce masa, “Yi gudu, gaya wa saurayin can cewa, ‘Urushalima za tă zama birni marar katanga domin mutane da dabbobi masu yawa ƙwarai za su kasance a cikinta.
Said to him, Go quickly and say to this young man, Jerusalem will be an unwalled town, because of the great number of men and cattle in her.
5 Ni da kaina ne zan zama katangar wuta kewaye da birnin, in kuma zama darajarta,’ in ji Ubangiji.
For I, says the Lord, will be a wall of fire round about her, and I will be the glory inside her.
6 “Zo! Zo! Ku gudu daga ƙasar arewa,” in ji Ubangiji, “gama na warwatsa ku a kusurwoyi huɗu na sama,” in ji Ubangiji.
Ho, ho! go in flight from the land of the north, says the Lord: for I have sent you far and wide to the four winds of heaven, says the Lord.
7 “Zo, ya ke Sihiyona! Ku tsere, ku masu zama a cikin Diyar Babilon!”
Ho! Zion, go in flight from danger, you who are living with the daughter of Babylon.
8 Gama ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Bayan ya ɗaukaka ni, ya kuma aiko ni ga ƙasashen da suka washe ku gama duk wanda ya taɓa ku ya taɓa ƙwayar idonsa ne.
For this is what the Lord of armies has said: In the way of glory he has sent me to the nations which have taken your goods: for anyone touching you is touching what is most dear to him.
9 Ba shakka zan tā da hannuna a kansu domin bayinsu su washe su. Sa’an nan za ku san cewa Ubangiji Maɗaukaki ne ya aiko ni.
For at the shaking of my hand over them, their goods will be taken by those who were their servants: and you will see that the Lord of armies has sent me.
10 “Ki yi sowa ki yi murna, ya ke Diyar Sihiyona. Gama ina zuwa, zan zauna a cikinki,” in ji Ubangiji.
Give songs of joy, O daughter of Zion: for I come, and I will make my resting-place among you, says the Lord.
11 “Ƙasashe da yawa za su haɗa kai da Ubangiji a ranan nan, za su kuma zama mutanena. Zan zauna a cikinku, za ku kuma san cewa Ubangiji Maɗaukaki ne ya aiko ni gare ku.
And a number of nations will be joined to the Lord in that day, and will become my people; and I will be living among you, and you will see that the Lord of armies has sent me to you.
12 Ubangiji zai gāji Yahuda a matsayin rabonsa a cikin ƙasa mai tsarki zai kuma sāke zaɓi Urushalima.
And Judah will be the Lord's heritage in the holy land, and Jerusalem will again be his.
13 Ku yi tsit a gaban Ubangiji, dukanku’yan adam, gama ya taso daga wurin zamansa mai tsarki.”
Let all flesh be quiet and make no sound before the Lord: for he is awake and has come from his holy resting-place.