< Zakariya 13 >

1 “A ranan nan za a buɗe maɓulɓulan ruwa zuwa gidan Dawuda da mazaunan Urushalima, don a tsarkake su daga zunubi da rashin tsabta.
In that day there shall be a fountain opened To the house of David, and to the inhabitants of Jerusalem, For sin and for uncleanness.
2 “A ranan nan, zan kawar da sunayen gumaka daga ƙasar, ba kuwa za a ƙara tunawa da su ba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan kawar da annabawa da kuma ruhu marar tsabta daga ƙasar.
And it shall come to pass in that day, Saith Jehovah of hosts, That I will cut off the names of the idols out of the land, And they shall no more be remembered; And the prophets also, and the impure spirit, Will I cause to pass out of the land.
3 In kuma wani ya yi annabci, sai mahaifinsa da mahaifiyarsa su ce masa, ‘Ba za ka rayu ba, gama kana faɗar ƙarya da sunan Ubangiji.’ Sa’ad da yake yin annabci, iyayensa za su soke shi da takobi.
And it shall come to pass, when any one shall yet prophesy, That his father and mother shall say to him, Even they that begat him, “Thou shalt not live; For thou hast spoken falsehood in the name of Jehovah.” And his father and mother that begat him shall pierce him through when he prophesieth.
4 “A ranan nan kowane annabi zai ji kunyar annabcin wahayinsa. Ba zai sa rigar annabci mai gashi ba don yă yi ruɗu.
And it shall come to pass in that day, that the prophet shall be ashamed Every one of his vision when he prophesieth; Neither shall they wear a garment of hair, to deceive.
5 Zai ce, ‘Ni ba annabi ba ne. Ni manomi ne; ƙasa ce nake samun abin zaman gari tun ina matashi.’
But each shall say, “I am no prophet; I am a man that tilleth the ground; For a man hath purchased me from my youth.”
6 In wani ya tambaye shi, ‘Waɗanne miyaku ne haka a jikinka?’ Zai amsa yă ce, ‘Miyakun da aka yi mini a gidan abokaina ne.’
And when one shall say to him, “What are these wounds in thy hands?” He shall answer, “Those with which I was wounded in the house of my friends.”
7 “Tashi, ya takobi, gāba da makiyayina, mutumin da yake kusa da ni sosai!” In ji Ubangiji Maɗaukaki. “Kashe makiyayin, sai tumakin su watse, in kuma tayar wa ƙananan.
Awake, O sword, against my shepherd, Even against the man who is my fellow, saith Jehovah of hosts! Smite the shepherd, and let the sheep be scattered! I will also turn my hand against the lambs.
8 A cikin ƙasar duka,” in ji Ubangiji, “kashi biyu bisa uku za a buge su su hallaka; duk da haka za a bar kashi ɗaya bisa uku a cikinta.
And it shall come to pass in all the land, saith Jehovah, That two parts therein shall be cut off and die; But the third part shall be left therein.
9 Wannan kashi ɗaya bisa ukun zan kawo in sa a cikin wuta; zan tace su kamar azurfa in gwada su kamar zinariya. Za su kira bisa sunana zan kuwa amsa musu; zan ce, ‘Su mutanena ne,’ za su kuma ce, ‘Ubangiji ne Allahnmu.’”
And I will bring the third part through the fire, And will refine them, as silver is refined, And will try them, as gold is tried; They shall call upon me, and I will hear them; I will say, “It is my people.” And they shall say, “Jehovah is our God.”

< Zakariya 13 >