< Zakariya 11 >

1 Buɗe ƙofofinki, ya Lebanon, don wuta ta cinye itatuwan al’ul naki.
Open your doors, Lebanon, so that fire may devour your cedars.
2 Yi kuka, ya itacen fir, gama itacen al’ul ya fāɗi; itatuwa masu daraja sun lalace! Ku yi kuka, ku itatuwan oak na Bashan; an sassare itatuwan babban kurmi!
Wail, pine-tree, for the cedar is fallen. Wail, oaks of Bashan, for the inaccessible forest has fallen.
3 Ku ji kukan makiyaya; an ɓata musu wuraren kiwonsu masu ciyayi! Ku ji rurin zakoki; an lalatar da jejin Urdun!
Listen to the wailing of the shepherds! Their glory is destroyed. Listen to the roaring of young lions! Blasted is the thick forest of the Jordan.
4 Ga abin da Ubangiji Allahna ya ce, “Yi kiwon garken tumakin da za a yanka.
The Lord said to me: shepherd the flock destined for slaughter,
5 Masu sayensu sun yanyanka su, suka kuwa tafi ba hukunci. Masu sayar da su sun ce, ‘Yabi Ubangiji, na yi arziki!’ Makiyayansu ma ba su ji tausayinsu ba.
whose possessors slaughter them, and hold themselves not guilty! The people who sell them say, Blessed be the Lord, for I am rich! And their own shepherds have no compassion for them.
6 Gama ba zan ƙara jin tausayin mutanen ƙasar ba,” in ji Ubangiji. “Zan ba da kowa ga maƙwabcinsa da kuma sarkinsa. Za su zalunci ƙasar, ba zan kuma cece su daga hannuwansu ba.”
I will no longer have pity on the people of this earth, says the Lord. I will turn neighbor against neighbor, and put everyone under the power of a king, and when the land is devastated I will not rescue them.
7 Saboda haka na yi kiwon garken da za a yanka, musamman garken da ake zalunta. Sai na ɗauki sanduna biyu na kira ɗaya Tagomashi, ɗaya kuma Haɗinkai, sai na yi kiwon garken.
So I shepherded the flock of slaughter for the sheep-merchants. I took two staffs: one I called Mercy and the other I called Union. So I shepherded the sheep.
8 Cikin wata guda na kawar da makiyayan nan uku. Garken suka ƙi ni, na kuwa gaji da su
I set aside three of the shepherds in one month; for I was indignant against them, and they also were displeased at me.
9 na ce, “Ba zan zama makiyayinku ba. Bari masu mutuwa su mutu, masu hallaka kuma su hallaka. Bari waɗanda suka ragu su ci naman juna.”
I said, I will not shepherd you. What is dead, let it die. What is set aside, let it be set aside. And let those who are left devour one another’s flesh.
10 Sai na ɗauki sandana mai suna Tagomashi na karya shi, na janye alkawarin da na yi da dukan al’ummai.
And I took my staff, Mercy, and broke it, so as to break my covenant which I had made with all the peoples.
11 An janye shi a ranan nan, saboda haka garken da yake cikin wahala masu kallona sun san cewa maganar Ubangiji ce.
In that day it was broken, and the sheep-merchants who watched me knew that it was the Lord’s message.
12 Na faɗa musu cewa, “In kun ga ya fi kyau, ku biya ni; in kuwa ba haka ba, ku riƙe.” Saboda haka suka biya ni azurfa talatin.
And I said to them, “If it is good in your sight, give me my wage. If not, don’t.” So they weighed out my wage, thirty pieces of silver.
13 Sai Ubangiji ya ce mini, “Jefar da shi cikin ma’aji,” Lada mai kyau da aka yi cinikina ne! Saboda haka sai na ɗauki azurfa talatin ɗin na jefa su cikin gidan Ubangiji don a sa cikin ma’aji.
And the Lord said to me, Cast it into the treasury – the precious wage that at which I was valued by them! So I took the thirty pieces of silver and cast them into the house of the Lord, into the treasury.
14 Sai na karya sandana na biyu mai suna Haɗinkai, ta haka na karya’yan’uwantakar da take tsakanin Yahuda da Isra’ila.
Then I broke my second staff called Union so as to dissolve the brotherhood between Judah and Jerusalem.
15 Sai Ubangiji ya ce mini, “Ka sāke ɗaukar kayan aiki na wawan makiyayi.
And the Lord said to me: Take again the implements of a worthless shepherd.
16 Gama zan tā da makiyayi a ƙasar wanda ba zai kula da ɓatattu, ko yă nemi ƙanana, ko yă warkar da waɗanda suka ji ciwo, ko kuma ciyar da masu lafiya ba, sai dai zai ci naman keɓaɓɓun tumaki, yă farfasa kofatonsu.
For I am about to appoint a shepherd over the land. Those who are thrust down he will not visit. Those who are scattered he will not seek out. The wounded he will not heal, the sick he will not make whole, but the flesh of the fat he will devour and even their hoofs he will tear.
17 “Kaito ga banzan makiyayin nan, wanda ya bar garken! Bari takobi yă sare hannunsa da idonsa na dama! Bari hannunsa yă shanye gaba ƙaf, idonsa na dama kuma yă makance sarai!”
Woe to my worthless shepherd, who deserts the flock! May the sword strike his arm and his right eye. May his arm completely wither. And his right eye be blinded.

< Zakariya 11 >