< Waƙar Waƙoƙi 8 >
1 Da a ce kai ɗan’uwa ne gare ni, wanda nonon mahaifiyata sun shayar! Da in na same ka a waje, na sumbace ka, babu wanda zai rena ni.
Oh that thou wert as my brother, That sucked the breasts of my mother! [When] I should find thee without, I would kiss thee; Yea, and none would despise me.
2 Da sai in bi da kai in kawo ka gidan mahaifiyata, ita da ta koyar da ni. Da na ba ka ruwan inabi gaurayayye da kayan yaji ka sha, zaƙin rumman nawa.
I would lead thee, [and] bring thee into my mother’s house, Who would instruct me; I would cause thee to drink of spiced wine, Of the juice of my pomegranate.
3 Hannunsa na hagu yana a ƙarƙashin kaina, hannunsa na dama kuma ya rungume ni.
His left hand [should be] under my head, And his right hand should embrace me.
4 ’Yan matan Urushalima, ku yi mini alkawari. Ba za ku tā da ko ku farka ƙauna ba sai haka ya zama lalle.
I adjure you, O daughters of Jerusalem, That ye stir not up, nor awake [my] love, Until he please.
5 Wace ce wannan da take haurawa daga hamada tana dogara a kan ƙaunataccenta? Ƙaunatacciya A ƙarƙashin itacen gawasa na farkar da ke, a wurin da aka haife ki, wurin da mahaifiyarki ta haife ki.
Who is this that cometh up from the wilderness, Leaning upon her beloved? Under the apple-tree I awakened thee: There thy mother was in travail with thee, There was she in travail that brought thee forth.
6 Ka sa ni kamar hatimi a zuciyarka, kamar hatimi a hannunka; gama ƙauna tana da ƙarfi kamar mutuwa, kishinta yana kamar muguntar kabari, yana ƙuna kamar wuta mai ci, kamar gagarumar wuta. (Sheol )
Set me as a seal upon thy heart, As a seal upon thine arm: For love is strong as death; Jealousy is cruel as Sheol; The flashes thereof are flashes of fire, A very flame of Jehovah. (Sheol )
7 Ruwa da yawa ba zai iya kashe ƙauna ba, koguna ba za su iya kwashe ta ba. In wani zai bayar da dukan dukiyar gidansa don ƙauna, za a yi masa dariya ne kawai.
Many waters cannot quench love, Neither can floods drown it: If a man would give all the substance of his house for love, He would utterly be contemned.
8 Muna da ƙanuwa, nonanta ba su riga sun yi girma ba. Me za mu yi da ƙanuwarmu a ranar da za a yi maganar sonta?
We have a little sister, And she hath no breasts: What shall we do for our sister In the day when she shall be spoken for?
9 Da a ce ita katanga ce, da sai mu gina hasumiyar azurfa a kanta. Da a ce ita ƙofa ce, da sai mun yi mata ƙyauren itacen al’ul.
If she be a wall, We will build upon her a turret of silver: And if she be a door, We will inclose her with boards of cedar.
10 Ni katanga ce kuma nonaina sun yi kamar hasumiya. Ta haka na zama idanunsa kamar wanda yake kawo gamsuwa.
I am a wall, and my breasts like the towers [thereof]: Then was I in his eyes as one that found peace.
11 Solomon ya kasance da gonar inabi a Ba’al-Hamon; ya ba da hayar gonar inabi ga’yan haya. Kowanne zai biya shekel dubu na azurfa don’ya’yan inabin.
Solomon had a vineyard at Baal-hamon; He let out the vineyard unto keepers; Every one for the fruit thereof was to bring a thousand [pieces] of silver.
12 Amma gonar inabina nawa ne da zan bayar; shekel dubu naka ne, ya Solomon, kuma ɗari biyu na waɗanda suke lura da’ya’yan itatuwansa ne.
My vineyard, which is mine, is before me: Thou, O Solomon, shalt have the thousand, And those that keep the fruit thereof two hundred.
13 Ke da kike zaune a cikin lambu da ƙawaye suna lura da ke, bari in ji muryarki!
Thou that dwellest in the gardens, The companions hearken for thy voice: Cause me to hear it.
14 Ka zo, ƙaunataccena, ka zama kamar barewa ko kuwa kamar’yar batsiya a kan dutsen da kayan yaji suke a shimfiɗe.
Make haste, my beloved, And be thou like to a roe or to a young hart Upon the mountains of spices.