< Waƙar Waƙoƙi 6 >
1 Ina ƙaunataccenki ya tafi, yake mafiya kyau cikin mata? Wace hanya ce ƙaunataccenki ya bi, don mu taimake ki nemansa.
2 Ƙaunataccena ya gangara zuwa lambunsa, zuwa inda fangulan kayan yaji suke, don yă yi kiwo a cikin lambun don kuma yă tattara furen bi-rana.
3 Ni na ƙaunataccena ce, ƙaunataccena kuma nawa ne; yana kiwo a cikin furen bi-rana.
4 Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata, kamar Tirza, kyakkyawa kuma kamar Urushalima, mai daraja kamar mayaƙa da tutoti.
5 Ki kau da idanu daga gare ni; gama suna rinjayata. Gashinki yana kama da garken awakin da suke gangarawa daga Gileyad.
6 Haƙoranki suna kama da garken tumakin da suke haurawa daga inda aka yi musu wanka. Kowanne yana tare da ɗan’uwansa; babu waninsu da yake shi kaɗai.
7 Kumatunki sun yi kamar rumman da aka tsaga biyu a cikin lulluɓinki.
8 Sarauniyoyi sittin za su iya kasance a can, da ƙwarƙwarai tamanin da kuma budurwai da suka wuce ƙirge;
9 amma kurciyata, cikakkiyata, dabam take, tilo kuwa ga mahaifiyarta,’yar lele ga wadda ta haife ta.’Yan mata sun gan ta suka ce da ita mai albarka; sarauniyoyi da ƙwarƙwarai sun yabe ta.
10 Wace ce wannan da ta bayyana sai ka ce ketowar alfijir? Kyakkyawa kamar wata, mai haske kamar rana, mai daraja kamar taurari a jere?
11 Na gangara zuwa cikin itatuwan almon don in ga ƙananan itatuwan da suke girma a kwari, don in ga ko inabi sun yi’ya’ya ko rumman suna fid da furanni.
12 Kafin in san wani abu, sha’awarta ta sa ni a cikin keken yaƙin sarkin mutanena.
13 Ki dawo, ki dawo, ya Bashulammiya; ki dawo, ki dawo, don mu dube ki! Ƙaunatacce Don me kuke duban Bashulammiya sai ka ce rawar Mahanayim?