< Waƙar Waƙoƙi 4 >
1 Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata! Kai, ke kyakkyawa ce! Idanunki sun yi kamar na kurciya a cikin lulluɓinki. Gashinki ya yi kamar garken awaki da suke gangarawa daga Dutsen Gileyad.
2 Haƙoranki sun yi kamar garken tumakin da ba a daɗe da yin musu sausaya ba, da suke haurawa daga inda aka yi musu wanka. Kowanne yana tare da ɗan’uwansa; babu waninsu da yake shi kaɗai.
3 Leɓunanki kamar zaren jan garura bakinki yana da kyau. Kumatunki sun yi kamar rumman da aka tsaga biyu a cikin lulluɓinki.
4 Wuyanki ya yi kamar hasumiyar Dawuda, da aka gina da daraja; a kansa an rataye garkuwoyi dubu, dukansu garkuwoyin jarumawa ne.
5 Nonanki biyu sun yi kamar bareyi biyu, kamar tagwayen barewa da suke kiwo a cikin furen bi-rana.
6 Sai gari ya waye inuwa kuma ta watse, zan je dutsen mur da kuma tudun turare.
7 Duk, ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata; babu wani lahani a cikinki.
8 Ki tare da ni daga Lebanon, amaryata, zo tare da ni daga Lebanon. Ki gangara daga ƙwanƙolin Amana, daga ƙwanƙolin Senir, ƙwanƙolin Hermon, daga ramin zaki da kuma dutsen da damisoshi suke zama.
9 Kin saci zuciyata,’yar’uwata, amaryata; kin saci zuciyata da hararar idanunki, da dutse mai daraja guda na abin wuyanki.
10 Ƙaunarki abar farin ciki ne,’yar’uwata, amaryata! Ƙaunarki ta fi ruwan inabi gamsuwa, ƙanshin turarenki kuma ya fi duk wani kayan yaji!
11 Leɓunanki suna zub da zaƙi kamar kakin zuma, amaryata; madara da zuma suna a ƙarƙashin harshenki. Ƙanshin rigunanki ya yi kamar na Lebanon.
12 Ke lambu ne da aka kulle,’yar’uwata, amaryata; ke maɓulɓula ce da aka kewaye, maɓulɓular da aka rufe.
13 Shuke-shukenki gonar rumman ne da’ya’yan itace masu kyau na lalle da nardi,
14 nardi, da asfaran, kalamus, da kirfa, da kowane irin itacen turare, da mur da aloyes da kuma dukan kayan yaji masu kyau.
15 Ke lambun maɓulɓula ne, rijiya mai ruwan da yake gudu yana gangarawa daga Lebanon.
16 Farka, iskar arewa, ki kuma zo, iskar kudu! Hura a kan lambuna, don ƙanshinsa yă bazu har waje. Bari ƙaunataccena yă zo cikin lambunsa yă ɗanɗana’ya’yan itacensa mafi kyau.