< Waƙar Waƙoƙi 1 >

1 Waƙar Waƙoƙin Solomon.
שיר השירים אשר לשלמה
2 Bari yă sumbace ni da sumbar bakinsa, gama ƙaunarka ta fi ruwan inabi zaƙi.
ישקני מנשיקות פיהו כי טובים דדיך מיין
3 Ƙanshin turarenka mai daɗi ne; sunanka kuwa kamar turaren da aka tsiyaye ne. Shi ya sa mata suke ƙaunarka!
לריח שמניך טובים שמן תורק שמך על כן עלמות אהבוך
4 Ka ɗauke ni mu gudu, mu yi sauri! Bari sarki yă kai ni gidansa. Ƙawaye Muna farin ciki muna kuma murna tare da kai, za mu yabi ƙaunarka fiye da ruwan inabi. Ƙaunatacciya Daidai ne su girmama ka!
משכני אחריך נרוצה הביאני המלך חדריו נגילה ונשמחה בך--נזכירה דדיך מיין מישרים אהבוך
5 Ni baƙa ce, duk da haka kyakkyawa. Ya ku’yan matan Urushalima, ni baƙa ce kamar tentunan Kedar, kamar labulen tentin Solomon.
שחורה אני ונאוה בנות ירושלם כאהלי קדר כיריעות שלמה
6 Kada ku harare ni domin ni baƙa ce, gama rana ta dafa ni na yi baƙa.’Ya’yan mahaifiyata maza sun yi fushi da ni suka sa ni aiki a gonakin inabi; na ƙyale gonar inabi na kaina.
אל תראוני שאני שחרחרת ששזפתני השמש בני אמי נחרו בי שמני נטרה את הכרמים--כרמי שלי לא נטרתי
7 Faɗa mini, kai da nake ƙauna, ina kake kiwon garkenka kuma ina kake kai tumakinka su huta da tsakar rana. Me ya sa zan kasance kamar macen da aka lulluɓe kusa da garkunan abokanka?
הגידה לי שאהבה נפשי איכה תרעה איכה תרביץ בצהרים שלמה אהיה כעטיה על עדרי חבריך
8 Ke mafiya kyau a cikin mata, in ba ki sani ba, to, ki dai bi labin da tumaki suke bi ki yi kiwon’yan awakinki kusa da tentunan makiyaya.
אם לא תדעי לך היפה בנשים צאי לך בעקבי הצאן ורעי את גדיתיך על משכנות הרעים
9 Ina kwatanta ke ƙaunatacciyata, da goɗiya mai jan keken yaƙin kayan Fir’auna.
לססתי ברכבי פרעה דמיתיך רעיתי
10 ’Yan kunne sun ƙara wa kumatunki kyau, wuyanki yana da jerin kayan wuya masu daraja.
נאוו לחייך בתרים צוארך בחרוזים
11 Za mu yi’yan kunnenki na zinariya, da adon azurfa.
תורי זהב נעשה לך עם נקדות הכסף
12 Yayinda sarki yake a teburinsa, turarena ya bazu da ƙanshi.
עד שהמלך במסבו נרדי נתן ריחו
13 Ƙaunataccena yana kamar ƙanshin mur a gare ni, kwance a tsakanin ƙirjina.
צרור המר דודי לי בין שדי ילין
14 Ƙaunataccena kamar tarin furanni jeji ne gare ni daga gonakin inabin En Gedi.
אשכל הכפר דודי לי בכרמי עין גדי
15 Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata! Kai, ke kyakkyawa ce! Idanunki kamar na kurciya ne.
הנך יפה רעיתי הנך יפה עיניך יונים
16 Kai kyakkyawa ne, ƙaunataccena! Kai, kana ɗaukan hankali! Gadonmu koriyar ciyawa ce.
הנך יפה דודי אף נעים אף ערשנו רעננה
17 Al’ul su ne ginshiƙan gidanmu; fir su ne katakan rufin gidanmu.
קרות בתינו ארזים רחיטנו (רהיטנו) ברותים

< Waƙar Waƙoƙi 1 >