< Rut 4 >
1 Ana cikin haka Bowaz ya haura zuwa ƙofar gari ya tafi ya zauna a can. Sa’ad da dangi mai fansan da ya yi zance ya iso, Bowaz ya ce, “Zo nan abokina ka zauna.” Saboda haka ya ratso ya zauna.
2 Bowaz kuwa ya kira dattawa guda goma na garin ya ce, “Ku zauna a nan,” suka kuwa zauna.
3 Sa’an nan ya ce wa dangin nan mai fansa, “Na’omi, wadda ta dawo daga Mowab, tana so ta sayar da filin da yake na ɗan’uwanmu Elimelek.
4 Na ga ya kamata in jawo hankalinka ga batun in kuma ba da shawara ka saye shi a gaban waɗannan da suke zazzaune a nan da kuma a gaban dattawan jama’a. In kana so ka fanshe shi, to, sai ka yi. Amma in ba za ka yi ba, sai ka faɗa mini, don in sani. Gama babu wani mai izinin yin haka sai kai, ni ne kuwa na biye.” Sai ya ce, “Zan fansa.”
5 Sa’an nan Bowaz ya ce, “A ranar da ka saya filin daga Na’omi da kuma daga Rut mutuniyar Mowab, ka sayi gwauruwar marigayin nan, domin ka riƙe sunan marigayin da kuma kayansa.”
6 Da jin haka, sai dangin nan mai fansa ya ce, “To, ba zan iya fanshe shi ba don kada in yi wa nawa mallakar rauni. Za ka iya fanshe shi wa kanka. Ni dai ba zan iya ba.”
7 (To, a kwanakin can a Isra’ila, domin a tabbatar da fansa da kuma musayar da mallaka, mutum zai cire takalminsa ya ba wa ɗayan. Wannan ita ce hanyar tabbatar da al’amarin a hukumance a cikin Isra’ila.)
8 Saboda haka dangin nan mai fansa ya ce wa Bowaz, “Saye shi wa kanka.” Sai ya cire takalminsa.
9 Sa’an nan Bowaz ya yi shela wa dattawa da kuma dukan mutane, “A yau ku ne shaidu cewa na saya daga Na’omi dukan mallakar Elimelek, Kiliyon da kuma Malon.
10 Na kuma ɗauki Rut mutuniyar Mowab, gwauruwar Malon a matsayin matata domin sunan mamaci da kuma mallakarsa yă ci gaba, domin kada sunansa yă ɓace daga cikin iyali ko daga tarihin gari. A yau ku ne shaidu!”
11 Sai dattawan da kuma dukan waɗanda suke a ƙofar suka ce, “Mu shaidu ne. Bari Ubangiji yă sa macen da take zuwa cikin gidanka ta zama kamar Rahila da Liyatu, waɗanda tare suka gina gidan Isra’ila. Bari ka sami martaba a cikin Efrata ka kuma zama sananne cikin Betlehem.
12 Ta wurin’ya’yan da Ubangiji zai ba ka ta wurin wannan mace, bari iyalinka yă zama kamar na Ferez, wanda Tamar ta haifa wa Yahuda.”
13 Sai Bowaz ya ɗauki Rut ta kuwa zama matarsa. Sa’an nan ya kwana da ita, Ubangiji kuma ya sa ta yi ciki, ta haifi ɗa.
14 Mata suka ce wa Na’omi, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda a wannan rana bai bar ki ba tare da dangi mai fansa ba. Allah yă sa yă zama sananne a dukan Isra’ila!
15 Zai sabunta rayuwarki yă adana ki a tsufanki. Gama surukarki wadda take ƙaunarki wadda kuma take mafi kyau gare ki fiye da’ya’ya maza bakwai, ta haife shi.”
16 Sai Na’omi ta ɗauki yaron, ta kwantar da shi a cinyarta ta kuma kula da shi.
17 Matan da suke zama a wurin suka ce, “Na’omi ta sami yaro.” Suka kuwa ba shi suna Obed. Shi ne ya haifi Yesse, mahaifin Dawuda.
18 Ga asalin zuriyar Ferez. Ferez shi ne mahaifin Hezron,
19 Hezron ya haifi Ram, Ram ya haifi Amminadab,
20 Amminadab ya haifi Nashon, Nashon ya haifi Salmon,
21 Salmon ya haifi Bowaz, Bowaz ya haifi Obed,
22 Obed ya haifi Yesse, Yesse kuwa ya haifi Dawuda.