< Rut 2 >

1 To, fa, Na’omi tana da dangi a gefen mijinta da iyalin Elimelek, mutum mai martaba, mai suna Bowaz.
Naomi avait un parent de son mari, un homme puissant et riche, de la famille d'Elimelech, et son nom était Boaz.
2 Sai Rut mutuniyar Mowab ta ce wa Na’omi, “Bari in tafi gonaki in yi kala raguwar hatsi a bayan duk wanda na sami tagomashi daga gare shi.” Na’omi ta ce mata, “Ki je,’yata.”
Ruth, la Moabite, dit à Naomi: « Laisse-moi maintenant aller aux champs et glaner parmi les épis, après celui qui m'a fait plaisir. » Elle lui dit: « Va, ma fille. »
3 Saboda haka ta tafi ta fara kala a gonaki a bayan masu girbi. Sai ya zamana, ta sami kanta tana aiki a gonar da take ta Bowaz, wanda yake daga dangin Elimelek.
Elle partit, et vint glaner dans le champ après les moissonneurs; et elle arriva à la portion de champ appartenant à Boaz, qui était de la famille d'Elimelech.
4 Sai ga Bowaz ya iso daga Betlehem ya gai da masu girbi, “Ubangiji yă kasance tare da ku!” Sai suka amsa, “Ubangiji yă albarkace ka!”
Voici que Boaz arrive de Bethléem et dit aux moissonneurs: « Que Yahvé soit avec vous. » Ils lui répondirent: « Que Yahvé te bénisse. »
5 Sai Bowaz ya tambayi shugaban masu girbinsa, “Wace yarinya ce wannan?”
Alors Boaz dit à son serviteur qui était préposé aux moissonneurs: « A qui est cette jeune fille? »
6 Shugaban ya amsa, “Ita ce mutuniyar Mowab da ta zo daga Mowab tare da Na’omi.
Le serviteur qui était préposé aux moissonneurs répondit: « C'est la femme moabite qui est revenue avec Naomi du pays de Moab.
7 Ta ce, ‘Ina roƙo a bar ni in bi bayan masu girbin in yi kala.’ Haka ta shiga cikin gonar ta kuwa yi aiki tun da safe har zuwa yanzu, sai ɗan hutun da ta yi kaɗan.”
Elle a dit: « Laisse-moi, je te prie, glaner et ramasser les gerbes après les moissonneurs ». Elle est donc venue, et elle a continué même depuis le matin jusqu'à maintenant, sauf qu'elle s'est reposée un peu dans la maison. »
8 Saboda haka Bowaz ya ce wa Rut, “’Yata, ki saurare ni. Kada ki tafi ki yi kala a wani gona, kada kuma ki tafi daga nan. Ki tsaya nan tare da’yan matana bayi.
Boaz dit alors à Ruth: « Écoute, ma fille. Ne va pas glaner dans un autre champ, et ne pars pas d'ici, mais reste ici près de mes servantes.
9 Ki lura da gonar da mutanena suke girbi, ki bi su tare da’yan matana. Na riga na faɗa wa mazan kada su taɓa ke. Kuma duk sa’ad da kika ji ƙishirwa, ki tafi ki ɗebo ruwa daga tulunan da mazan suka cika.”
Que tes yeux soient fixés sur le champ qu'elles moissonnent, et va après elles. N'ai-je pas ordonné aux jeunes gens de ne pas vous toucher? Si vous avez soif, allez vers les vases, et buvez de ce que les jeunes gens ont tiré. »
10 Jin haka, sai ta rusuna da fuskata har ƙasa ta ce, “Me ya sa na sami irin wannan tagomashi a idanunka da har ka lura da ni, ni da nake baƙuwa?”
Alors elle tomba sur sa face et se prosterna à terre, et lui dit: « Pourquoi ai-je trouvé grâce à tes yeux, pour que tu me connaisses, puisque je suis une étrangère? »
11 Bowaz ya amsa, “An faɗa mini duka game da abin kika yi domin surukarki tun mutuwar mijinki, yadda kika bar mahaifinki da mahaifiyarki da kuma ƙasarki kika zo ki yi zama da mutanen da ba ki taɓa sani ba.
Boaz lui répondit: « On m'a raconté tout ce que tu as fait pour ta belle-mère depuis la mort de ton mari, et comment tu as quitté ton père, ta mère et le pays où tu es née, pour venir chez un peuple que tu ne connaissais pas auparavant.
12 Bari Ubangiji yă sāka maka saboda abin da ka yi. Bari Ubangiji, Allah na Isra’ila yă sāka maka a yalwace, a ƙarƙashin fikafikan da ka sami mafaka.”
Que Yahvé te rende la pareille et que tu reçoives une pleine récompense de Yahvé, le Dieu d'Israël, sous les ailes duquel tu es venue te réfugier. »
13 Ta ce, “Bari in ci gaba da samun tagomashi a idanunka ranka yă daɗe. Ka ta’azantar da ni ka kuma yi wa baranyarka magana mai alheri ko da yake ban kai matsayi ɗaya daga cikin bayinka’yan mata ba.”
Alors elle dit: « Que je trouve grâce à tes yeux, mon seigneur, parce que tu m'as consolée et que tu as parlé avec bonté à ta servante, bien que je ne sois pas comme l'un de tes serviteurs. »
14 A lokacin cin abinci Bowaz ya ce mata, “Zo nan. Ki ɗebo burodi ki tsoma cikin ruwan inabi.” Da ta zauna tare da masu girbin, sai ya ba ta gasasshe hatsi. Ta ci duk abin da take so har ta bar ragowa.
A l'heure du repas, Boaz lui dit: « Viens ici, mange du pain, et trempe ton morceau dans le vinaigre. » Elle s'assit à côté des moissonneurs, et ils lui passèrent du grain desséché. Elle mangea, fut satisfaite, et en laissa une partie.
15 Da ta tashi don tă yi kala, sai Bowaz ya yi umarni wa samarinsa cewa, “Ko ta tara daga cikin dammuna, kada ku wulaƙanta ta.
Lorsqu'elle se leva pour glaner, Boaz donna cet ordre à ses jeunes gens: « Laissez-la glaner parmi les gerbes, et ne lui faites pas de reproches.
16 Ku kuma riƙa zarar mata waɗansu daga dammunan don ta ɗauka, kada ku kwaɓe ta.”
Tirez aussi pour elle des gerbes, et laissez-les. Laissez-la glaner, et ne lui faites pas de reproches. »
17 Saboda haka Rut ta yi kala a gonar har yamma. Sa’an nan ta sussuka hatsin sha’ir da ta kalata ta sami kamar efa.
Elle glana dans le champ jusqu'au soir, et elle battit ce qu'elle avait glané: c'était environ un épha d'orge.
18 Ta ɗauka ta koma gari sai surukarta ta ga yawan abin da ta kalato. Rut kuma ta fitar da ragowar abin da ta ci bayan ta ƙoshi ta ba ta.
Elle le prit, et alla à la ville. Sa belle-mère vit ce qu'elle avait glané; elle sortit et lui donna ce qu'elle avait laissé, après s'être rassasiée.
19 Surukarta ta tambaye ta, “Ina kika yi kala a yau? Ina kika yi aiki? Albarka ta tabbata ga mutumin nan ta ya lura da ke!” Sai Rut ta faɗa wa surukarta game da wurin wanda ta yi ta aiki. Ta ce, “Sunan mutumin da na yi aiki da shi a yau Bowaz ne.”
Sa belle-mère lui dit: « Où as-tu glané aujourd'hui? Où as-tu travaillé? Béni soit celui qui t'a remarquée. » Elle dit à sa belle-mère avec qui elle avait travaillé: « Le nom de l'homme avec qui j'ai travaillé aujourd'hui est Boaz. »
20 Sai Na’omi ta ce wa surukarta, “Ubangiji yă yi masa albarka! Bai daina nuna alheri ga masu rai da matattu ba.” Ta ƙara da cewa, “Wannan mutum danginmu ne na kusa; shi ɗaya daga cikin danginmu mai fansa.”
Naomi dit à sa belle-fille: « Qu'il soit béni par Yahvé, qui n'a pas abandonné sa bonté envers les vivants et les morts. » Naomi lui dit: « Cet homme est un proche parent de nous, un de nos proches. »
21 Sa’an nan Rut mutuniyar Mowab ta ce, “Ya ma ce mini, ‘Ki riƙa bin ma’aikatana sai sun ƙare yin girbin dukan hatsina.’”
Ruth, la Moabite, répondit: « Oui, il m'a dit: « Tu resteras près de mes jeunes gens jusqu'à ce qu'ils aient fait toute ma récolte. »
22 Na’omi ta ce wa Rut surukarta, “Zai fi miki kyau,’yata ki riƙa tafiya da’yan matansa, domin a gonar wani dabam mai yiwuwa a yi miki lahani.”
Naomi dit à Ruth, sa belle-fille: « Il est bon, ma fille, que tu sortes avec ses servantes, et qu'elles ne te rencontrent pas dans un autre champ. »
23 Saboda haka Rut ta tsaya kusa da bayi mata na Bowaz don tă yi kala sai da girbin sha’ir da na alkama suka ƙare. Ta kuwa zauna tare da surukarta.
Elle resta donc près des servantes de Boaz, pour glaner jusqu'à la fin de la moisson de l'orge et de la moisson du blé, et elle vécut avec sa belle-mère.

< Rut 2 >