< Romawa 9 >
1 Ina faɗin gaskiya a cikin Kiristi ba ƙarya nake yi ba, lamirina ya tabbatar da wannan a cikin Ruhu Mai Tsarki.
我在基督里说真话,并不谎言,有我良心被圣灵感动,给我作见证:
2 Ina da baƙin ciki mai yawa da kuma rashin kwanciyar rai marar ƙarewa a zuciyata.
我是大有忧愁,心里时常伤痛;
3 Gama da so na ne, sai a la’anta ni a kuma raba ni da Kiristi saboda’yan’uwana, waɗannan na kabilata,
为我弟兄,我骨肉之亲,就是自己被咒诅,与基督分离,我也愿意。
4 mutanen Isra’ila. Su ne Allah ya mai da su’ya’yansa, ya bayyana musu ɗaukakarsa, ya ba su alkawarinsa da Dokarsa, ya nuna musu hanyar sujada ta gaske, ya kuma ba su sauran alkawura.
他们是以色列人;那儿子的名分、荣耀、诸约、律法、礼仪、应许都是他们的。
5 Kakannin-kakannin nan kuma nasu ne, Kiristi kuma, ta wurin zamansa mutum, na kabilarsu ne. Yabo ya tabbata ga Allah har abada, shi da yake bisa kome! Amin. (aiōn )
列祖就是他们的祖宗;按肉体说,基督也是从他们出来的。他是在万有之上,永远可称颂的 神。阿们! (aiōn )
6 Ba cewa maganar Allah ta kāsa ba ne. Gama ba duk waɗanda suke zuriyar Isra’ila ne suke Isra’ila na gaske ba.
这不是说 神的话落了空。因为从以色列生的不都是以色列人,
7 Ba kuwa don su zuriyarsa ne dukansu suka zama’ya’yan Ibrahim ba. A maimako, “Ta wurin Ishaku ne za a lissafta zuriyarka.”
也不因为是亚伯拉罕的后裔就都作他的儿女;惟独“从以撒生的才要称为你的后裔。”
8 Ana iya cewa zaman zuriyar Ibrahim, ba shi ne zama’ya’yan Allah ba, a’a, zuriya ta alkawarin nan su ne ake lasaftawa zuriyar Ibrahim.
这就是说,肉身所生的儿女不是 神的儿女,惟独那应许的儿女才算是后裔。
9 Ga yadda aka yi alkawarin nan, “A ƙayyadadden lokaci zan dawo, Saratu kuma za tă haifi ɗa.”
因为所应许的话是这样说:“到明年这时候我要来,撒拉必生一个儿子。”
10 Ba ma haka kaɗai ba,’ya’yan Rifkatu suna da mahaifi guda ne, wato, mahaifinmu Ishaku.
不但如此,还有利百加,既从一个人,就是从我们的祖宗以撒怀了孕,(
11 Duk da haka, tun ba a haifi tagwayen nan ba, balle su yi wani abu mai kyau ko marar kyau don nufin Allah bisa ga zaɓensa ya tabbata, ba ga aikin lada ba, sai dai ga kiransa,
双子还没有生下来,善恶还没有做出来,只因要显明 神拣选人的旨意,不在乎人的行为,乃在乎召人的主。)
12 ba ta wurin ayyuka ba sai dai ta wurin shi wanda ya kira, aka faɗa mata cewa, “Babban zai bauta wa ƙaramin.”
神就对利百加说:“将来,大的要服事小的。”
13 Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yaƙub ne na so, amma Isuwa ne na ƙi.”
正如经上所记:雅各是我所爱的;以扫是我所恶的。
14 Me za mu ce ke nan? Allah marar adalci ne? Sam, ko kaɗan!
这样,我们可说什么呢?难道 神有什么不公平吗?断乎没有!
15 Gama ya ce wa Musa, “Zan nuna jinƙai ga wanda zan nuna jinƙai, zan kuma ji tausayin wanda zan ji tausayi.”
因他对摩西说: 我要怜悯谁就怜悯谁, 要恩待谁就恩待谁。
16 Saboda haka, bai danganta ga sha’awar mutum ko ƙoƙarinsa ba, sai dai ga jinƙan Allah.
据此看来,这不在乎那定意的,也不在乎那奔跑的,只在乎发怜悯的 神。
17 Gama Nassi ya ce wa Fir’auna, “Na ɗaga ka saboda wannan manufa, saboda in nuna ikona a cikinka domin kuma a shaida sunana a duniya duka.”
因为经上有话向法老说:“我将你兴起来,特要在你身上彰显我的权能,并要使我的名传遍天下。”
18 Saboda haka Allah yana nuna jinƙai ga wanda yake so, yana kuma taurara zuciyar wanda yake so.
如此看来, 神要怜悯谁就怜悯谁,要叫谁刚硬就叫谁刚硬。
19 Waninku zai iya ce mini, “To, don me har yanzu Allah yake ganin laifinmu? Gama wa zai iya tsayayya da nufinsa?”
这样,你必对我说:“他为什么还指责人呢?有谁抗拒他的旨意呢?”
20 Amma wane ne kai, ya mutum, da za ka mayar wa Allah magana? “Ashe, abin da aka gina zai iya ce wa wanda ya gina shi, ‘Don me ka gina ni haka?’”
你这个人哪,你是谁,竟敢向 神强嘴呢?受造之物岂能对造他的说:“你为什么这样造我呢?”
21 Ashe, mai ginin tukwane ba shi da iko yin amfani da yumɓu guda yă gina tukunya domin ayyuka masu daraja da kuma waɗansu don ayyuka marasa daraja?
窑匠难道没有权柄从一团泥里拿一块做成贵重的器皿,又拿一块做成卑贱的器皿吗?
22 Haka ma aikin Allah yake. Ya so yă nuna fushinsa yă kuma sanar da ikonsa, ya yi haka cikin haƙuri ƙwarai ga waɗanda suka cancanci fushinsa, waɗanda aka shirya domin hallaka?
倘若 神要显明他的忿怒,彰显他的权能,就多多忍耐宽容那可怒、预备遭毁灭的器皿,
23 Haka kuma ya so yă sanar da wadatar ɗaukakarsa ga waɗanda suka cancanci jinƙansa, waɗanda ya shirya tun kafin lokaci don ɗaukaka
又要将他丰盛的荣耀彰显在那蒙怜悯、早预备得荣耀的器皿上。
24 har da mu ma, mu da ya kira, ba daga cikin Yahudawa kaɗai ba amma har ma daga cikin Al’ummai?
这器皿就是我们被 神所召的,不但是从犹太人中,也是从外邦人中。这有什么不可呢?
25 Kamar yadda ya faɗa a Hosiya. “Zan kira su ‘mutanena,’ su da ba mutanena ba; zan kuma kira ta ‘ƙaunatacciyata,’ ita da ba ƙaunatacciyata ba,”
就像 神在何西阿书上说: 那本来不是我子民的, 我要称为“我的子民”; 本来不是蒙爱的, 我要称为“蒙爱的”。
26 kuma, “Zai zama cewa a daidai inda aka ce musu, ‘Ku ba mutanena ba,’ za a ce da su, ‘’ya’yan Allah mai rai.’”
从前在什么地方对他们说: 你们不是我的子民, 将来就在那里称他们为“永生 神的儿子”。
27 Ishaya ya ɗaga murya game da Isra’ila ya ce, “Ko da yake yawan Isra’ilawa yana kama da yashi a bakin teku, ragowa ce kaɗai za su sami ceto.
以赛亚指着以色列人喊着说:“以色列人虽多如海沙,得救的不过是剩下的余数;
28 Gama Ubangiji zai zartar da hukuncinsa a bisan duniya da sauri kuma ba da ɓata lokaci ba.”
因为主要在世上施行他的话,叫他的话都成全,速速地完结。”
29 Yana nan kamar yadda Ishaya ya riga ya faɗa. “Da ba don Ubangiji Maɗaukaki ya bar mana zuriya ba, da mun zama kamar Sodom, da mun kuma zama kamar Gomorra.”
又如以赛亚先前说过: 若不是万军之主给我们存留余种, 我们早已像所多玛、蛾摩拉的样子了。
30 Me za mu ce ke nan? Ai, Al’ummai da ba su nemi adalci ba, sun same shi, adalcin da yake ta wurin bangaskiya;
这样,我们可说什么呢?那本来不追求义的外邦人反得了义,就是因信而得的义。
31 amma Isra’ila da suka yi ƙwazo wajen bin Dokar adalci, ba su same shi ba.
但以色列人追求律法的义,反得不着律法的义。
32 Don me? Domin sun yi ƙwazo wajen binta ba ta wurin bangaskiya ba sai dai ta wurin ayyuka. Sun yi tuntuɓe a kan “dutsen sa tuntuɓe.”
这是什么缘故呢?是因为他们不凭着信心求,只凭着行为求;他们正跌在那绊脚石上。
33 Kamar yadda yake a rubuce, “Ga shi, na sa dutse a Sihiyona da yake sa mutane yin tuntuɓe da kuma dutsen da yake sa su fāɗi wanda kuwa ya dogara gare shi ba zai taɓa shan kunya ba.”
就如经上所记: 我在锡安放一块绊脚的石头,跌人的磐石; 信靠他的人必不至于羞愧。