< Romawa 8 >
1 Saboda haka, yanzu babu hukunci don waɗanda suke cikin Kiristi Yesu,
There is now, therefore, no condemnation to those who are in Christ Jesus.
2 gama ta wurin Kiristi Yesu dokar Ruhu mai ba da rai ta’yantar da ni daga Dokar Musa.
For the law of the spirit of life in Christ Jesus has freed me from the law of sin, and of death.
3 Gama abin da dokar ba tă iya yi saboda kāsawar mutuntaka ba, Allah ya yi shi sa’ad da ya aiko da Ɗansa a kamannin mutum mai zunubi, don yă zama hadaya ta zunubi. Ta haka, ya hukunta zunubi a cikin mutum mai zunubi.
For what the law could not do, because it was weak through the flesh, God has done, who, sending his own son in the likeness of sinful flesh, and for a sin-offering, condemned sin in the flesh,
4 Ya yi haka domin yă cika bukatun adalcin doka a cikinmu, mu da ba ma rayuwa bisa ga mutuntaka, sai dai bisa ga Ruhu.
that the righteousness of the law might be fulfilled in us, who walk not according to the flesh, but according to the Spirit.
5 Waɗanda suke rayuwa bisa ga mutuntaka sun kafa hankulansu a kan sha’awace-shawa’acen jiki; amma waɗanda suke rayuwa bisa ga Ruhu sun kafa hankulansu a kan abubuwan da Ruhu yake so.
For those who are according to the flesh, mind the things of the flesh; but those who are according to the Spirit, the things of the Spirit.
6 Ƙwallafa rai ga al’amuran halin mutuntaka ƙarshensa mutuwa ne, ƙwallafa rai ga al’amuran Ruhu kuwa rai ne da salama;
For the mind of the flesh is death; but the mind of the Spirit is life and peace.
7 hankalin mai zunubi na gāba da Allah. Ba ya biyayya da dokar Allah, ba kuwa zai iya yin haka ba.
Because the mind of the flesh is enmity against God; for it is not subject to the law of God, nor indeed can it be.
8 Waɗanda mutuntaka yake mulkinsu ba za su iya su gamshi Allah ba.
Those, then, who are in the flesh, can not please God.
9 Ku kam, ana mulkinku ba ta wurin mutuntaka ba, sai dai ta wurin Ruhu, in Ruhun Allah yana zaune a cikinku. In kuma wani ba shi da Ruhun Kiristi, shi ba na Kiristi ba ne.
But you are not in the flesh, but in the Spirit, if indeed the Spirit of God dwells in you. Now, if any one has not the Spirit of Christ, he is not his.
10 Amma in Kiristi yana a cikinku, jikinku matacce ne saboda zunubi, duk da haka ruhunku yana a raye saboda adalci.
But if Christ is in you, the body is dead, on account of sin, but the Spirit is life, on account of righteousness.
11 In kuwa Ruhu wannan da ya tā da Yesu daga matattu yana zama a cikinku, shi wanda ya tā da Kiristi daga matattu zai ba da rai ga jikunanku masu mutuwa ta wurin Ruhunsa, wanda yake zama a cikinku.
And if the Spirit of him who raised Jesus from the dead dwells in you, he that raised the Christ from the dead will give life to your mortal bodies, because of his Spirit that dwells in you.
12 Saboda haka’yan’uwa, muna da hakki, amma ba na wanda za mu yi rayuwar mutuntaka da yake so ba.
Therefore, brethren, we are debtors, not to the flesh, to live according to the flesh;
13 Gama in kuna rayuwa bisa ga mutuntaka, za ku mutu; amma in ta wurin Ruhu kuka kashe ayyukan jikin nan, za ku rayu.
for if you live according to the flesh, you shall die: but if, through the Spirit, you put to death the deeds of the body, you shall live.
14 Domin waɗanda Ruhun Allah yake bi da su ne’ya’yan Allah.
For as many as are led by the Spirit of God, they are the sons of God.
15 Gama ba ku karɓi ruhun da ya mai da ku bayi da za ku sāke jin tsoro ba ne, sai dai kun karɓi Ruhun zaman ɗa. Ta wurinsa kuwa muke kira, “Abba, Uba.”
For you have not again received the spirit of bondage, that you may fear; but you have received the spirit of adoption, by which we cry, Abba, Father.
16 Ruhu kansa yana ba da shaida tare da ruhunmu cewa mu’ya’yan Allah ne.
The Spirit itself testifies with our spirit, that we are the children of God;
17 In kuwa mu’ya’ya ne, to, mu magāda ne, magādan Allah da kuma abokan gādo tare da Kiristi, in kuwa muna tarayya a cikin shan wuyarsa to, za mu yi tarayya a cikin ɗaukakarsa.
and, if children, then heirs; heirs of God, and joint-heirs with Christ, if indeed we suffer with him, that we may also be glorified together.
18 A ganina, wuyar da muke sha a wannan lokaci ba su isa a kwatanta da ɗaukakar da za a bayyana a cikinmu ba.
For I consider the sufferings of the present time not worthy to be compared with the glory that shall be revealed for us.
19 Halitta tana jira da marmari ta ƙosa ta ga bayyanuwar’ya’yan Allah.
For the earnest expectation of the creature waits for the revelation of the sons of God.
20 Gama an sa halitta a cikin wulaƙanci, ba da son ta ba, sai dai ta wurin nufin wannan da ya mai da ita haka, da bege
For the creature was subject to frailty, (not by its own will, but for his sake who subjected it, )
21 cewa za a’yantar da halitta kanta daga bautarta ga ruɓewa a kuma kawo ta cikin’yancin ɗaukakar’ya’yan Allah.
in hope, that even the creature itself shall be made free from the bondage of corruption, and introduced into the glorious liberty of the children of God.
22 Mun san cewa dukan halitta tana nishi sai ka ce mace mai naƙuda har yă zuwa wannan lokaci.
For we know that every creature groans, and is in pain together, till now:
23 Ba haka kaɗai ba ma, mu kanmu da muke da nunan fari na Ruhu, muna nishi a ciki-cikinmu yayinda muke jira da marmari a maishe mu’ya’yan riƙo na Allah, fansar jikunanmu.
and not only they, but ourselves also, who have the first fruits of the Spirit, even we ourselves groan within ourselves, waiting for the adoption, the redemption of our body.
24 Gama a wannan begen ne muka sami ceto. Amma begen da ake gani ba bege ba ne sam. Wa yake begen abin da ya riga ya samu?
For we are saved by this hope; but hope that is seen is not hope; for, what any one sees, why does he also hope for it?
25 Amma in muna begen abin da ba mu riga mun samu tukuna ba, mukan jira da haƙuri.
But if we hope for that which we see not we wait for it with patience.
26 Haka nan ma, Ruhu yana taimakonmu cikin rashin ƙarfinmu. Ba mu san abin da ya kamata mu roƙa cikin addu’a ba, amma Ruhu kansa yana roƙo a madadinmu da nishe-nishen da kalmomi ba sa iya bayyanawa.
In like manner, also, the Spirit helps our infirmities; for we know not what we should pray for as we ought, but the Spirit itself intercedes for us, with groanings unutterable.
27 Shi kuma wanda yake binciken zukatanmu ya san halin Ruhu, domin Ruhu yana roƙo a madadin tsarkaka bisa ga nufin Allah.
And he that searches the hearts knows what is the mind of the Spirit, that he intercedes for the saints according to the will of God.
28 Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa.
And we know that all things work together for good, to those who love God, to those who are called according to his purpose.
29 Gama waɗanda Allah ya rigyasani ya kuma ƙaddara su dace da kamannin Ɗansa, don yă zama ɗan fari cikin’yan’uwa masu yawa.
For those whom he foreknew, he predestinated to be conformed to the image of his Son, that he might be the first-born among many brethren:
30 Waɗanda kuwa ya ƙaddara, su ne ya kira; waɗanda ya kira kuwa, su ne ya kuɓutar; waɗanda ya kuɓutar kuwa, su ne ya ɗaukaka.
and those whom he predestinated he also called, and those whom he called he also justified, and those whom he justified he also glorified.
31 Me za mu ce ke nan game da wannan abu? In Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu?
What, then, shall we say to these things? If God be for us, who can be against us?
32 Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka, ashe, ba zai kuma ba mu, tare da shi, dukan abubuwa cikin alherinsa ba?
He that spared not his own Son, but delivered him up for us all, how will he not with him also freely give us all things?
33 Wa zai kawo wani zargi a kan waɗanda Allah ya zaɓa? Allah ne mai kuɓutarwa.
Who shall lay any thing to the charge of God’s elect? It is God that justifies.
34 Wa zai yi hukunci? Yesu Kiristi ne, wanda ya mutu, fiye da haka ma, shi da aka tā da zuwa rai, yana zaune a hannun dama na Allah yana kuma yin roƙo a madadinmu.
Who is he that condemns? It is Christ that died: rather, indeed, that has risen, who is at the right hand of God, who also intercedes for us.
35 Wane ne zai raba mu da ƙaunar Kiristi? Masifa ce ko wahala ko tsanani ko yunwa ko tsiraici ko hatsari ko takobi?
Who shall separate us from the love of the Christ? Shall affliction, or distress, or persecution, or famine, or nakedness, or danger, or the sword?
36 Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Saboda kai ne muke fuskantar mutuwa dukan yini; an ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.”
As it is written: For thy sake, we are killed all the day long; we are counted as sheep for the slaughter.
37 A’a, cikin dukan waɗannan abubuwa mun ma fi masu nasara ta wurin shi wanda ya ƙaunace mu.
Yet, in all these things, we are more than conquerors, through him that loved us.
38 Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki,
For I am persuaded that neither death, nor life, nor angels, nor principalities, nor powers, nor things present, nor things to come,
39 ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.
nor hight, nor depth, nor any other creature, will be able to separate us from the love of God which is in Christ Jesus our Lord.