< Romawa 7 >

1 Ba ku sani ba,’yan’uwa, ina magana ne fa da mutanen da suka san doka, cewa dokar tana da iko a kan mutum muddin yana a raye ne kawai.
η αγνοειτε αδελφοι γινωσκουσιν γαρ νομον λαλω οτι ο νομοσ κυριευει του ανθρωπου εφ οσον χρονον ζη
2 Misali, bisa ga doka mace mai aure tana daure ga mijinta muddin mijin yana da rai, amma in mijinta ya mutu, an sake ta ke nan daga dokar aure.
η γαρ υπανδροσ γυνη τω ζωντι ανδρι δεδεται νομω εαν δε αποθανη ο ανηρ κατηργηται απο του νομου του ανδροσ
3 Saboda haka fa, in ta auri wani yayinda mijinta yana raye, za a ce da ita mazinaciya. Amma in mijinta ya mutu, an sake ta ke nan daga wannan doka, ita kuwa ba mazinaciya ba ce, ko da yake ta auri wani.
αρα ουν ζωντοσ του ανδροσ μοιχαλισ χρηματισει εαν γενηται ανδρι ετερω εαν δε αποθανη ο ανηρ ελευθερα εστιν απο του νομου του μη ειναι αυτην μοιχαλιδα γενομενην ανδρι ετερω
4 Saboda haka’yan’uwana, ku ma kun mutu ga dokar ta wurin jikin Kiristi, domin ku zama na wani, gare shi wanda aka tashe shi daga matattu, don mu ba da amfani ga Allah.
ωστε αδελφοι μου και υμεισ εθανατωθητε τω νομω δια του σωματοσ του χριστου εισ το γενεσθαι υμασ ετερω τω εκ νεκρων εγερθεντι ινα καρποφορησωμεν τω θεω
5 Gama sa’ad da halin mutuntaka yake mulkinmu, sha’awace-sha’awacen zunubi waɗanda dokar ta zuga sun yi ta aiki a jikunanmu, don mu ba da amfani wa mutuwa.
οτε γαρ ημεν εν τη σαρκι τα παθηματα των αμαρτιων τα δια του νομου ενηργειτο εν τοισ μελεσιν ημων εισ το καρποφορησαι τω θανατω
6 Amma yanzu, ta wurin mutuwa ga abin da dā ya daure mu, an sake mu daga dokar saboda mu yi hidima a sabuwar hanyar Ruhu, ba a tsohuwar hanyar rubutaccen ƙa’ida ba.
νυνι δε κατηργηθημεν απο του νομου αποθανοντεσ εν ω κατειχομεθα ωστε δουλευειν ημασ εν καινοτητι πνευματοσ και ου παλαιοτητι γραμματοσ
7 Me za mu ce ke nan? Dokar zunubi ce? Sam, ko kaɗan! Tabbatacce ai, da ban san mene ne zunubi ba in ba ta wurin doka ba. Gama da ban san mene ne ƙyashi yake ba tabbatacce in ba don doka ta ce, “Kada ka yi ƙyashi ba.”
τι ουν ερουμεν ο νομοσ αμαρτια μη γενοιτο αλλα την αμαρτιαν ουκ εγνων ει μη δια νομου την τε γαρ επιθυμιαν ουκ ηδειν ει μη ο νομοσ ελεγεν ουκ επιθυμησεισ
8 Amma zunubi, da ya sami dama ta wurin umarnin nan, ya haifar a cikina kowane halin ƙyashi iri-iri. Gama in babu doka, zunubi matacce ne.
αφορμην δε λαβουσα η αμαρτια δια τησ εντολησ κατειργασατο εν εμοι πασαν επιθυμιαν χωρισ γαρ νομου αμαρτια νεκρα
9 Dā kam ina da rai sa’ad da ban san doka ba; amma da umarni ya zo, sai zunubi ya zaburo da rai na kuma mutu.
εγω δε εζων χωρισ νομου ποτε ελθουσησ δε τησ εντολησ η αμαρτια ανεζησεν εγω δε απεθανον
10 Na gane cewa wannan umarnin da aka nufa ya kawo rai, a gaskiya ya jawo mutuwa ce.
και ευρεθη μοι η εντολη η εισ ζωην αυτη εισ θανατον
11 Gama zunubi, da ya sami dama ta wurin umarni, sai ya ruɗe ni, kuma ta wurin umarnin kuwa ya kashe ni.
η γαρ αμαρτια αφορμην λαβουσα δια τησ εντολησ εξηπατησεν με και δι αυτησ απεκτεινεν
12 Saboda haka fa, dokar tana da tsarki, umarnin kuma yana da tsarki, su duka suna da adalci da kuma kyau.
ωστε ο μεν νομοσ αγιοσ και η εντολη αγια και δικαια και αγαθη
13 Abin nan da yana mai kyau, zai kawo mini mutuwa? Ko kaɗan! Amma domin zunubi ya bayyana kansa a matsayin zunubi, sai ya haifar da mutuwa a cikina ta wurin abin da yake mai kyau, domin ta wurin umarnin nan zunubi ya fito da matuƙar muninsa.
το ουν αγαθον εμοι γεγονεν θανατοσ μη γενοιτο αλλα η αμαρτια ινα φανη αμαρτια δια του αγαθου μοι κατεργαζομενη θανατον ινα γενηται καθ υπερβολην αμαρτωλοσ η αμαρτια δια τησ εντολησ
14 Mun san cewa doka aba ce ta ruhu; amma ni ba na ruhu ba ne, an sayar da ni a matsayin bawa ga zunubi.
οιδαμεν γαρ οτι ο νομοσ πνευματικοσ εστιν εγω δε σαρκικοσ ειμι πεπραμενοσ υπο την αμαρτιαν
15 Ban gane abin da nake yi ba. Don abin da nakan so yi, ba shi nakan yi ba, sai dai abin da nake ƙi, shi nake yi.
ο γαρ κατεργαζομαι ου γινωσκω ου γαρ ο θελω τουτο πρασσω αλλ ο μισω τουτο ποιω
16 In kuma na yi abin da ba na son yi, na yarda da cewa dokar aba ce mai kyau.
ει δε ο ου θελω τουτο ποιω συμφημι τω νομω οτι καλοσ
17 Kamar dai yadda yake, ba ni kaina nake yinsa ba, sai dai zunubin da yake zaune a cikina ne.
νυνι δε ουκετι εγω κατεργαζομαι αυτο αλλ η οικουσα εν εμοι αμαρτια
18 Gama na san cewa babu wani abin kirkin da yake zaune a cikina, wato, a mutuntakata. Gama sha’awar yin abu mai kyau kam ina da ita, sai dai ikon yin ne fa babu.
οιδα γαρ οτι ουκ οικει εν εμοι τουτ εστιν εν τη σαρκι μου αγαθον το γαρ θελειν παρακειται μοι το δε κατεργαζεσθαι το καλον ουχ ευρισκω
19 Gama abin da nake yi ba shi ne abu mai kyau da nake so in yi ba; a’a, mugun da ba na so in yi, shi ne nake ci gaba da yi.
ου γαρ ο θελω ποιω αγαθον αλλ ο ου θελω κακον τουτο πρασσω
20 To, in na yi abin da ba na so in yi, ba ni ba ne nake yinsa, sai dai zunubin nan da yake zaune a cikina.
ει δε ο ου θελω εγω τουτο ποιω ουκετι εγω κατεργαζομαι αυτο αλλ η οικουσα εν εμοι αμαρτια
21 Saboda haka na gane wannan ƙa’ida ce take aiki a cikina. Sa’ad da nake so in yi abu mai kyau, sai in ga cewa mugun nan ne nake yi.
ευρισκω αρα τον νομον τω θελοντι εμοι ποιειν το καλον οτι εμοι το κακον παρακειται
22 Gama a ciki-cikina ina farin cikin da dokar Allah;
συνηδομαι γαρ τω νομω του θεου κατα τον εσω ανθρωπον
23 amma ina ganin wata doka tana aiki a gaɓoɓin jikina, tana yaƙi da dokar hankalina, tana kuma sa in zama ɗaurarren dokar zunubin da take aiki a gaɓoɓin jikina.
βλεπω δε ετερον νομον εν τοισ μελεσιν μου αντιστρατευομενον τω νομω του νοοσ μου και αιχμαλωτιζοντα με τω νομω τησ αμαρτιασ τω οντι εν τοισ μελεσιν μου
24 Kaitona! Wane ne zai cece ni daga wannan jiki mai mutuwa?
ταλαιπωροσ εγω ανθρωποσ τισ με ρυσεται εκ του σωματοσ του θανατου τουτου
25 Godiya ga Allah ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu! Saboda haka fa, ni kaina a cikin hankalina, ni bawa ne ga dokar Allah, amma a mutuntaka, ni bawa ne ga dokar zunubi.
ευχαριστω τω θεω δια ιησου χριστου του κυριου ημων αρα ουν αυτοσ εγω τω μεν νοι δουλευω νομω θεου τη δε σαρκι νομω αμαρτιασ

< Romawa 7 >