< Romawa 4 >
1 To, me za mu ce Ibrahim kakan kakanninmu ya gani game da wannan batu?
2 In fa da gaske ne Ibrahim ya sami kuɓuta ta wurin ayyuka, yana da abin da zai yin taƙama da shi ke nan, amma ba a gaban Allah ba.
3 Me Nassin ya ce? “Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lissafta wannan adalci ne a gare shi.”
4 To, sa’ad da mutum ya yi aiki, ba a lissafta ladan aikinsa a matsayin kyauta, sai dai a matsayin hakkinsa.
5 Amma fa, game da mutumin da ba ya aiki sai dai dogara ga Allah wanda yake kuɓutar da masu mugunta, akan lissafta bangaskiyarsa a matsayin adalci ne.
6 Dawuda ya faɗi haka sa’ad da ya yi magana game da albarkar da aka yi wa mutumin da Allah ya lissafta adalci a gare shi, ba don yă yi ayyuka ba.
7 “Masu albarka ne waɗanda aka gafarta laifofinsu, waɗanda aka kuma rufe zunubansu.
8 Mai albarka ne mutumin da Ubangiji ba zai taɓa lissafta zunubansa ba.”
9 Shin, wannan albarkar a kan masu kaciya ne kawai, ko kuwa har da marasa kaciya ma? Mun sha faɗi cewa an lissafta bangaskiyar Ibrahim adalci ne a gare shi.
10 A kan wane hali ne aka lissafta masa? Bayan da aka yi masa kaciya ne, ko kuwa kafin kaciyar? Ba bayan an yi masa kaciya ba ne, amma kafin a yi masa kaciya!
11 Ya kuma karɓi alamar kaciya, hatimin adalcin da yake da shi ta wurin bangaskiya tun yana marar kaciya. Saboda haka fa, ya zama mahaifin dukan waɗanda suka gaskata domin su ma a lasafta su masu adalci ne, ba tare da an yi musu kaciya ba.
12 Ya kuma zama mahaifin masu kaciya waɗanda ba kaciya kaɗai suke da ita ba amma har ma suna bin gurbin bangaskiyar da mahaifinmu Ibrahim yake da ita kafin aka yi masa kaciya.
13 Ba ta wurin doka ce Ibrahim da zuriyarsa suka sami alkawarin cewa zai zama magājin duniya ba, amma sai dai ta wurin adalcin da yake zuwa ta wurin bangaskiya.
14 Gama da a ce masu kiyaye doka ne magāda, ai, da bangaskiya ba ta da amfani, alkawarin kuma ya zama banza,
15 domin doka tana jawo fushi ne. Kuma inda babu doka babu keta umarni ke nan.
16 Saboda haka, alkawari yakan zo ta wurin bangaskiya ne, domin yă zama ta wurin alheri, don a tabbatar wa dukan zuriyar Ibrahim ba kawai ga waɗanda suke na doka ba amma har ma ga waɗanda suke na bangaskiyar Ibrahim. Shi ne kuwa mahaifinmu duka.
17 Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Na mai da kai uban al’ummai masu yawa.” Shi ubanmu ne a gaban Allah, wanda a cikinsa ya gaskata, Allahn da yake ba da rai ga matattu, yake kuma kiran abubuwan da ba su kasance ba su zama kamar sun kasance.
18 Saɓanin dukan bege, Ibrahim cikin bege ya gaskata, haka kuwa ya zama uban al’ummai masu yawa, kamar yadda aka riga aka faɗa masa cewa, “Haka zuriyarka za tă zama.”
19 Ba tare da ya bar bangaskiyarsa ta yi rauni ba, ya fuskanci gaskiyan nan mai cewa jikinsa mai tsufa matacce ne, da yake yana da shekara wajen ɗari, mahaifar Saratu kuma matacciya ce.
20 Duk da haka bai yi shakka ta wurin rashin bangaskiya game da alkawarin Allah ba, sai ma ya ƙara ƙarfafa ga bangaskiyarsa, ya kuma ɗaukaka Allah,
21 yana kuma da cikakken tabbaci cewa Allah yana da iko yă cika abin da ya yi alkawari.
22 Shi ya sa, “aka lissafta adalci a gare shi.”
23 Kalmomin nan, “aka lissafta a gare shi” ba a rubuta su saboda shi kaɗai ba ne,
24 amma saboda mu ma, mu da Allah zai lissafta adalci, mu da muka ba da gaskiya gare shi da ya tashe Yesu Ubangijinmu daga matattu.
25 An miƙa shi ga mutuwa saboda zunubanmu, aka kuma tashe shi zuwa rai saboda Allah zai same mu marasa laifi.