< Romawa 3 >
1 To, mece ce ribar zama mutumin Yahuda, ko kuwa mene ne amfanin kaciya?
2 Akwai riba ƙwarai ta kowace hanya! Da farko dai, su ne aka danƙa wa kalmomin nan na Allah.
3 Amma a ce waɗansu ba su da bangaskiya fa? Rashin bangaskiyarsu nan zai shafe amincin Allah?
4 Ko kaɗan! Bari Allah yă zama mai gaskiya, kowane mutum kuma yă zama maƙaryaci. Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Gama a tabbatar kana da gaskiya, sa’ad da ka yi magana, ka kuma yi nasara sa’ad da ka yi shari’a.”
5 Amma in rashin adalcinmu ya bayyana adalcin Allah a fili, me za mu ce ke nan? Za mu ce Allah ya yi rashin adalci ke nan da ya saukar da fushinsa a kanmu? (Ina magana kamar yadda mutum zai yi ne.)
6 Sam, ko kusa! Da a ce haka ne, ta yaya Allah zai shari’anta duniya?
7 Wani zai iya ce, “In a dalilin ƙaryata, gaskiyar Allah ta ƙara bayyana, har aka ƙara ɗaukaka shi, to, ta yaya zan zama mai zunubi, in ƙaryata tana kawo ɗaukaka ga Allah?”
8 In haka ne, “Ba sai mu yi ta yin mugunta don yă zama hanyar samun nagarta ba”? Kamar yadda masu baƙar magana game da mu suna cewa wai haka muke faɗa. Tabbatacce za a hukunta irin waɗannan da hukuncin da ya dace da su.
9 To, me za mu ce ke nan? Mun fi su ke nan? Ina, ko kaɗan! Mun riga mun zartar cewa da Yahudawa da Al’ummai duk suna a ƙarƙarshin zunubi.
10 Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Babu wani mai adalci, babu ko ɗaya;
11 babu wani mai fahimta, babu wani mai neman Allah.
12 Duk sun kauce gaba ɗaya, sun zama marasa amfani; babu wani mai aikata nagarta, babu ko ɗaya.”
13 “Maƙogwaronsu kamar buɗaɗɗun kaburbura ne, harsunansu suna yin ƙarya.” “Dafin mugun maciji yana a leɓunansu.”
14 “Bakunansu sun cike da la’ana da ɗacin rai.”
15 “Ƙafafunsu suna saurin kai su zuwa ga zub da jini;
16 hallaka da baƙin ciki suna ko’ina a hanyoyinsu,
17 ba su kuma san hanyar salama ba.”
18 “Babu tsoron Allah a idanunsu.”
19 Yanzu mun san cewa dukan abin da doka ta ce, tana magana ne ga waɗanda suke ƙarƙarshin doka, saboda a rufe kowane baki; dukan duniya kuma ta ba da lissafin kanta a gaban Allah.
20 Saboda haka babu wanda Allah zai ce da shi mai adalci ta wurin kiyaye doka kawai; a maimako, ta wurin doka ne muke sane da zunubi.
21 Amma yanzu an bayyana wani adalci daga Allah, wannan adalcin bai danganta ga doka ba, Doka da Annabawa suna ba da shaida game da wannan adalci.
22 Wannan adalcin Allah yana zuwa ta wurin bangaskiya a cikin Yesu Kiristi ga dukan waɗanda suka ba da gaskiya ne. Ba bambanci,
23 gama duka sun yi zunubi suka kuma kāsa ga ɗaukakar Allah,
24 an kuma kuɓutar da su kyauta ta wurin alherinsa bisa ga aikin fansar da ya zo ta wurin Yesu Kiristi.
25 Allah ya miƙa Yesu Kiristi a matsayin hadayar kafara, ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya yi haka domin yă nuna adalcinsa, domin a cikin haƙurinsa bai hukunta zunuban da aka aikata a dā ba
26 ya yi haka domin yă nuna adalcinsa a wannan lokaci, saboda yă zama mai adalci da mai kuɓutar da waɗanda suke ba da gaskiya a cikin Yesu.
27 To, me za mu yi taƙama a kai? Babu wani abin da zamu yi taƙama a kai. A kan wace ƙa’ida ce za mu yi taƙama? Ta hanyar bin doka ne? A’a, sai dai ta wurin bangaskiya.
28 Gama mun tsaya a kan cewa ta wurin bangaskiya ne ake kuɓutar da mutum, ba ta wurin kiyaye doka ba.
29 Allah ɗin, Allahn Yahudawa ne kaɗai? Shi ba Allahn Al’ummai ba ne? I, shi Allahn Al’ummai ne ma,
30 da yake Allah ɗaya ne kaɗai, shi kuma zai kuɓutar da masu kaciya bisa ga bangaskiya da kuma marasa kaciya ta wurin wannan bangaskiya ɗin.
31 To, za mu soke dokar saboda wannan bangaskiyar ne? Ko kaɗan! A maimako, sai ma tabbatar da ita muke yi.