< Romawa 2 >

1 Saboda haka, kai da kake ba wa wani laifi, ba ka da wata hujja, gama a duk lokacin da kake ba wa wani laifi, kana hukunta kanka ne, domin kai da kake ba wa wani laifi kai ma kana aikata waɗannan abubuwa.
THEREFORE thou art inexcusable, O man, even every one that judgeth: for in the very thing wherein thou judgest another, thou condemnest thyself; for thou that judgest art living in the practices of the same things.
2 Yanzu mun san cewa hukuncin Allah a kan masu aikata waɗannan abubuwa daidai ne.
But we know that the judgment of God is according to truth, against those who practise such things.
3 Saboda haka sa’ad da kai mutum kurum, kana ba su laifi, duk da haka kana aikata abubuwan nan, kana tsammani za ka tsere wa hukuncin Allah ne?
For thinkest thou this, O man, that judgest those who do such things, and doest the same, that thou shalt escape the judgment of God?
4 Ko kuma kana rena wadatar alherinsa, haƙurinsa, da kuma jimrewarsa ne ba tare da sanin cewa alherin Allah yana kai ka ga tuba ba ne?
Or despisest thou the riches of his kindness and patience and long-suffering, ignorant that this goodness of God is leading thee to repentance?
5 Amma saboda taurinkanka da zuciyarka marar tuba, kana tara wa kanka fushi a ranar fushin Allah, sa’ad da za a bayyana hukuncinsa mai adalci.
But after thy obdurate and impenitent heart treasurest up for thyself wrath at the day of wrath and revelation of the righteous judgment of God,
6 Allah, “Zai sāka wa kowane mutum gwargwadon aikin da ya yi.”
who will recompense to every man according to his works;
7 Ga waɗanda ta wurin naciya suna yin nagarta suna neman ɗaukaka, girma da rashin mutuwa, su za a ba su rai madawwami. (aiōnios g166)
to those who, in the patient practice of good works, seek glory and honour and immortality―eternal life. (aiōnios g166)
8 Amma ga waɗanda suke sonkai waɗanda suke ƙin gaskiya suke kuma bin mugunta, akwai fushi da haushi dominsu.
But to those who are of a contentious spirit, and do not obey the truth, but obey unrighteousness, indignation, and wrath;
9 Akwai wahala da baƙin ciki ga duk mutumin da yake aikata mugunta, da farko Yahudawa, sa’an nan Al’ummai,
tribulation and anguish upon every soul of man that doeth wickedness, of the Jew first, and also of the Greek.
10 amma akwai ɗaukaka, girma da salama ga duk mutumin da yake aikata alheri, da farko Yahudawa, sa’an nan Al’ummai.
But glory and honour and peace be to every man who doeth that which is good, to the Jew first and also to the Greek:
11 Gama Allah ba ya nuna bambanci.
for there is no acceptance of persons with God.
12 Duk waɗanda suka yi zunubi a rashi sanin doka, a rashin doka za su hallaka, waɗanda kuma suka yi zunubi ƙarƙashin doka, a ƙarƙashin doka za a hukunta su.
For as many as have sinned without the law, shall perish also without the law: and as many as have sinned under the law shall be judged by the law;
13 Gama ba masu jin dokar ne suke da adalci a gaban Allah ba, amma waɗanda suke yin biyayya da dokar, su za a ce da su masu adalci.
for the hearers of the law are not righteous before God, but the doers of the law shall be counted righteous;
14 Tabbatacce, sa’ad da Al’ummai, waɗanda ba su da dokar, suka aikata abubuwan da dokar take bukata, abubuwan sun zama doka ke nan gare su, ko da yake ba su da dokar.
(for when the Gentiles, who have not the law naturally, do the things of the law, these, though not having the law, are a law unto themselves:
15 To, da yake sun nuna cewa abubuwan da dokar take bukata suna a rubuce a zukatansu, lamirinsu yana kuma ba da shaida, tunaninsu kuwa yanzu yana zarginsu ko kuma yana kāre su.
which exhibit the practice of the law written on their hearts, their conscience also bearing its testimony, and their mutual reasonings at intervals bringing accusations or forming excuses; )
16 Wannan zai faru a ranar da Allah ta wurin Yesu Kiristi zai shari’anta ɓoyayyun abubuwan da mutane suka yi, yadda bisharata ta furta.
in the day when God shall judge the hidden things of men, according to my gospel by Jesus Christ.
17 To, kai, da kake kiran kanka mutumin Yahuda; in kana dogara ga doka kana kuma taƙama da dangantakarka da Allah;
Lo! thou art named a Jew, and restest on the law, and boastest in God,
18 in ka san nufinsa ka kuma amince da abin da yake mafifici domin an koyar da kai bisa ga doka;
and knowest the will of God, and bringest to the test the things that are different, being instructed out of the law;
19 in ka tabbata cewa kai jagora ne ga makafi, haske ga waɗanda suke cikin duhu,
and hast confidence that thou thyself art a leader of the blind, a light of those who are in darkness,
20 mai koyar da masu wauta, malamin jarirai, domin a cikin dokar ce akwai sani da gaskiya
an instructor of the uninformed, a teacher of babes, holding the form of knowledge and of truth in the law.
21 to, kai mai koya wa waɗansu, ba kanka kake koya wa ba? Kai da kake wa’azi kada a yi sata, kana sata?
Thou therefore who teachest another, dost thou not teach thyself? thou that proclaimest aloud that a man should not steal, dost thou steal?
22 Kai da kake cewa wa mutane kada su yi zina, kana yin zina? Kai da kake ƙyamar gumaka, kana wa haikali fashi?
thou that sayest, Do not commit adultery, dost thou commit adultery? thou that holdest idols in abomination, dost thou commit sacrilege?
23 Kai da kake taƙama da doka, kana nuna rashin bangirma ga Allah ta wurin karya dokar?
thou who gloriest in the law, dishonourest thou God by the transgression of the law?
24 Kamar yadda yake a rubuce, “Ana saɓon sunan Allah a cikin Al’ummai saboda ku.”
for the name of God is blasphemed through you among the heathen, as it is written.
25 Kaciya tana da amfani in kana kiyaye dokar, amma in kana karya dokar, ka zama kamar ba a yi maka kaciya ba.
For circumcision indeed is advantageous, if thou practise the law: but if thou art a transgressor of the law, thy circumcision becomes uncircumcision,
26 In marasa kaciya suna kiyaye dokar, ashe, ba za a ɗauke su kamar an yi musu kaciya ba?
If then the uncircumcision observe the righteous judgments of the law, shall not his uncircumcision be accounted for circumcision?
27 Wanda ba shi da kaciya ta jiki duk da haka yana biyayya da dokar zai iya hukunta ka, kai da kake karya dokar, ko da yake kana da rubutaccen tsarin dokar an kuma yi maka kaciya.
And the uncircumcision by nature which fulfilleth the law shall condemn thee, who through the letter and circumcision art a transgressor of the law.
28 Mutum ba mutumin Yahuda ba ne in shi mutumin Yahuda ne kawai a jiki, haka kuma kaciya ba a waje ko a jiki kawai ba.
For not he who is outwardly such, is the Jew; neither is that which is outward in the flesh, circumcision.
29 A’a, mutum mutumin Yahuda ne in shi mutumin Yahuda ne a zuci; kuma kaciya ita ce kaciya ta zuci, ta wurin Ruhu, ba ta wurin rubutaccen doka ba. Irin wannan mutum yana samun yabo daga Allah ne, ba ɗan adam ba.
But he is a Jew who is such inwardly; and circumcision is of the heart, in spirit, not in letter; whose praise is not from men, but from God.

< Romawa 2 >