< Romawa 15 >
1 Mu da muke da ƙarfi ya kamata mu yi haƙuri da kāsawar marasa ƙarfi ba kawai mu gamshi kanmu ba.
2 Ya kamata kowannenmu yă faranta wa maƙwabcinsa rai don kyautata zamansa domin kuma yă gina shi.
3 Gama ko Kiristi ma bai gamshi kansa ba, amma kamar yadda yake a rubuce cewa, “Zage-zagen da waɗansu suka yi maka, duk sun fāɗo a kaina.”
4 Gama duk abin da aka rubuta a dā an rubuta ne domin yă koya mana, don ta wurin jimrewa da kuma ƙarfafawar Nassosi mu kasance da bege.
5 Bari Allah mai ba da haƙuri da kuma ƙarfafawa yă ba ku ruhun haɗinkai da juna yayinda kuke bin Kiristi Yesu,
6 don da zuciya ɗaya da kuma baki ɗaya kuke ɗaukaka Allah da kuma Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi.
7 Ta haka sai ku karɓi juna kamar yadda Kiristi ya karɓe ku, don a yabi Allah.
8 Ina dai gaya muku cewa Kiristi ya zama bawan Yahudawa a madadin gaskiyar Allah, don yă tabbatar da alkawaran da aka yi wa kakannin kakanninmu
9 domin Al’ummai su ɗaukaka Allah saboda jinƙansa, kamar yadda yake a rubuce, “Saboda haka zan yabe ka a cikin Al’ummai; zan rera waƙoƙi ga sunanka.”
10 Ya kuma ce, “Ku yi farin ciki, ya Al’ummai, tare da mutanensa.”
11 Da kuma, “Ku yabi Ubangiji, dukanku Al’ummai, ku kuma rera masa yabo, dukanku mutanen duniya.”
12 Kuma Ishaya ya ce, “Tushen Yesse zai tsiro, wanda zai taso yă yi mulkin al’ummai; al’ummai za su sa bege a gare shi.”
13 Bari Allah na bege yă cika ku da matuƙar farin ciki da salama yayinda kuke dogara gare shi, domin ku yalwata cikin bege ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.
14 Ni kaina na tabbata,’yan’uwana, cewa ku kanku kuna cike da kirki, cikakku cikin sani da kuma ƙwararru don yin wa juna gargaɗi.
15 Na rubuta muku gabagadi a kan waɗansu batuttuwa, don in sāke tuna muku su, saboda alherin da Allah ya ba ni
16 in zama mai hidimar Kiristi Yesu ga Al’ummai da aikin firist na yin shelar bisharar Allah, don Al’ummai su zama hadaya mai karɓuwa ga Allah, tsattsarka ta wurin Ruhu Mai Tsarki.
17 Saboda haka ina taƙama cikin Kiristi Yesu a cikin hidimata ga Allah.
18 Ba zan yi karambani in faɗi kome ba sai dai abin da Kiristi ya aikata ta wurina a jagorantar da Al’ummai su yi biyayya ga Allah ta wurin abin da na faɗa da kuma aikata
19 ta wurin ikon alamu da ayyukan banmamaki, da kuma ikon Ruhun Allah. Ta haka daga Urushalima har yă zuwa kewayen Illirikum, na yi wa’azin bisharar Kiristi.
20 Labudda, burina shi ne in yi wa’azin bishara inda ba a san Kiristi ba, don kada yă zama ina gini ne a kan tushen da wani ya kafa.
21 Sai dai kamar yadda yake a rubuce, “Waɗanda ba a faɗa musu labarinsa ba za su gani, waɗanda kuma ba su ji ba za su fahimta.”
22 Wannan ne ya sa sau da yawa aka hana ni zuwa wurinku.
23 Amma yanzu da babu sauran wurin da ya rage mini in yi aiki a waɗannan yankuna, da yake kuma shekaru masu yawa ina da marmari in gan ku,
24 ina shirin yin haka in na tafi Sifen. Ina fata in ziyarce ku yayinda nake wucewa don ku raka ni can, bayan na ji daɗin zama tare da ku na ɗan lokaci.
25 Yanzu kam, ina hanyata zuwa Urushalima don in kai gudummawa ga tsarkaka a can.
26 Gama Makidoniya da Akayya sun ji daɗin yin gudummawa domin matalautan da suke cikin tsarkakan da suke a Urushalima.
27 Sun kuwa ji daɗin yin haka, gama ya zama kamar bashi ne a gare su. Da yake Al’ummai sun sami rabo cikin albarkun ruhaniyar Yahudawa, ya zama musu kamar bashi su ma su taimaki Yahudawa da albarkunsu na kayan duniya.
28 Saboda haka in na kammala wannan aiki na kuma tabbata cewa sun karɓi wannan amfani, zan tafi Sifen in kuma ziyarce ku a hanyata.
29 Na san cewa sa’ad da na zo wurinku, zan zo ne cikin yalwar albarkar Kiristi.
30 Ina roƙonku’yan’uwa, saboda Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma saboda ƙaunar Ruhu, ku haɗa kai tare da ni cikin famata ta wurin yin addu’a ga Allah saboda ni.
31 Ku yi addu’a don in kuɓuta daga hannun marasa bi a Yahudiya don kuma gudummawar da nake kaiwa Urushalima ta zama abar karɓa ga tsarkaka a can,
32 don da yardar Allah, in iso wurinku da farin ciki in kuma wartsake tare da ku.
33 Allah na salama yă kasance tare da ku duka. Amin.