< Romawa 14 >
1 Ku karɓi wanda bangaskiyarsa ba tă yi ƙarfi ba, amma fa kada ku hukunta shi a kan abubuwan da ake da shakka a kai ba.
2 Bangaskiyar mutum ta yarda masa yă ci kome, amma wanda bangaskiyarsa ba tă yi ƙarfi ba, yakan ci kayan lambu ne kawai.
3 Mutumin da yake cin kowane irin abinci, kada yă rena wanda ba ya cin, wanda kuma ba ya cin kowane irin abinci, kada yă ga laifin mutumin da yake ci, domin Allah ya riga ya karɓe shi.
4 Kai wane ne har da za ka ga laifin bawan wani? Ko bawan yă yi aiki mai kyau, ko yă kāsa, ai, wannan ruwan maigidansa ne. Za a ma tsai da shi, domin Ubangiji yana da ikon tsai da shi.
5 Wani yakan ɗauki wata rana da daraja fiye da sauran ranaku; wani kuma yana ganin dukan ranakun ɗaya ne. Ya kamata kowa yă kasance da tabbaci a cikin zuciyarsa.
6 Wannan mai ɗaukan rana ɗaya da muhimmanci fiye da sauran, yana yin haka ne ga Ubangiji. Wannan mai cin nama, yana yin haka ne ga Ubangiji, gama yakan yi godiya ga Allah; wannan da ba ya ci kuwa, yana yin haka ne ga Ubangiji yana kuwa yin godiya ga Allah.
7 Gama ba waninmu da yake rayuwa wa kansa kaɗai, kuma ba waninmu da kan mutu don kansa kaɗai.
8 In muna rayuwa, muna rayuwa ne ga Ubangiji; in kuma muna mutuwa, muna mutuwa ne ga Ubangiji. Saboda haka, ko muna a raye ko muna a mace, mu na Ubangiji ne.
9 Saboda wannan ne Kiristi ya mutu, ya kuma sāke rayuwa domin yă zama Ubangiji na matattu da na masu rai.
10 Kai kuwa, don me kake ganin laifin ɗan’uwanka? Ko kuma don me kake rena ɗan’uwanka? Gama duk za mu tsaya a gaban kujerar shari’ar Allah.
11 A rubuce yake cewa, “‘Muddin ina raye,’ in ji Ubangiji, ‘kowace gwiwa za tă durƙusa a gabana; kowane harshe kuma zai furta wa Allah.’”
12 Don haka kowannenmu zai ba da lissafin kansa ga Allah.
13 Saboda haka bari mu daina ba wa juna laifi. A maimakon, sai kowa yă yi niyya ba zai sa dutsen tuntuɓe ko abin sa fāɗuwa a hanyar ɗan’uwansa ba.
14 A matsayina na mai bin Ubangiji Yesu na tabbata ƙwarai cewa babu abincin da yake marar tsabta don kansa. Amma in wani ya ɗauka wani abu marar tsabta ne, to, a gare shi marar tsabta ne.
15 In kana ɓata wa ɗan’uwanka zuciya saboda abincin da kake ci, ba halin ƙauna kake nunawa ba ke nan. Kada abincin da kake ci yă zama hanyar lalatar da ɗan’uwanka wanda Kiristi ya mutu dominsa.
16 Kada ka bar abin da ka ɗauka a matsayi kyakkyawa yă zama abin zargi ga waɗansu.
17 Gama mulkin Allah ba batun ci da sha ba ne, sai dai na adalci, salama, da kuma farin ciki cikin Ruhu Mai Tsarki,
18 duk kuwa wanda yake bauta wa Kiristi a haka yana faranta wa Allah rai ne, yardajje kuma ga mutane.
19 Saboda haka sai mu yi iya ƙoƙari mu aikata abin da zai kawo salama da kuma ingantawa ga juna.
20 Kada ku lalatar da aikin Allah saboda abinci. Dukan abinci mai tsabta ne, sai dai ba daidai ba ne mutum yă ci abin da zai sa wani yă yi tuntuɓe.
21 Ya fi kyau kada ka ci nama ko ka sha ruwan inabi ko kuma ka yi wani abin da zai sa ɗan’uwanka yă fāɗi.
22 Bari duk ra’ayin da kake da shi game da wannan sha’ani yă kasance tsakaninka da Allah. Mai albarka ne wanda zuciyarsa ba tă ba shi laifi game da abin da shi da kansa ya ɗauka cewa daidai ne ba.
23 Amma wanda yake da shakka yakan jawo wa kansa hukunci ne in ya ci, domin yana ci ne ba bisa ga bangaskiya ba; kuma duk abin da bai zo daga bangaskiya ba zunubi ne.