< Romawa 11 >

1 To, ina da tambaya. Allah ya ƙi mutanensa ne? Sam, ko kaɗan! Ni mutumin Isra’ila ne kaina, zuriyar Ibrahim kuwa, daga kabilar Benyamin.
И тъй, казвам: Отхвърлил ли е Бог Своите люде? Да не бъде! Защото и аз съм израилтянин, от Авраамовото потомство, от Вениаминовото племе.
2 Allah bai ƙi mutanensa da ya rigya sani ba. Ba ku san abin da Nassi ya faɗa game da Iliya ba, yadda ya kawo kuka ga Allah a kan Isra’ila ya ce,
Не е отхвърлил Бог людете Си, които е предузнал. Или не знаете що казва писанието за Илия? как вика към Бога против Израиля, казвайки:
3 “Ya Ubangiji, sun karkashe annabawanka suka kuma rurrushe bagadanka; ni kaɗai na ragu, suna kuma neman raina”?
"Господи, избиха пророците Ти, разкопаха олтарите Ти, и аз останах сам; но и моя живот искат да отнемат".
4 Wace amsa ce Allah ya ba shi? “Na keɓe wa kaina dubu bakwai waɗanda ba su yi wa Ba’al sujada ba.”
Но що му казва божественият отговор?
5 Haka ma, a wannan zamani akwai ragowar da aka zaɓa ta wurin alheri.
Така и в сегашно време има остатък, избран по благодат
6 In kuwa na alheri ne, ba sauran cewa ya dogara ga ayyuka ke nan. In ba haka ba, ashe, alheri ba alheri ba ne kuma.
Но, ако е по благодат, не е вече от дела, иначе благодатта не е вече благодат [а ако е от делата, не е вече благодат, иначе делото не е вече дело].
7 To, sai me? Abin da Isra’ila suka nema da himma ba su samu ba, amma zaɓaɓɓun suka samu. Sauran suka taurare,
Тогава какво? Онова, което Израил търсеше, това не получи, но избраните го получиха, а останалите се закоравиха даже до днес:
8 kamar yadda yake a rubuce cewa, “Allah ya ba su ruhun ruɗewa, idanu don su kāsa gani, da kuma kunnuwa don su kāsa ji, har yă zuwa yau.”
както е писано: "Бог им даде дух на безчуствие, очи
9 Dawuda kuma ya ce, “Bari teburin cin abincinsu yă zama musu tarko, sanadin fāɗuwa da dutsen sa tuntuɓe da kuma ramuwa a kansu.
И Давид казва:
10 Bari idanunsu su duhunta don kada su iya gani, bayansu kuma yă tanƙware har abada.”
Да се помрачат очите им, та да не виждат, И сгърби гърба им за винаги".
11 Har yanzu ina da tambaya. Sun yi tuntuɓe har ya kai ga fāɗuwar da ba za su iya tashi ba ne? Sam, ko kaɗan! A maimako, saboda laifinsu ne ceto ya zo ga Al’ummai don a sa mutanen Isra’ila su ji kishi.
Тогава казвам: Спънаха ли се, та да паднат? Да не бъде! Но чрез тяхното отклонение дойде спасението на езичниците, за да ги възбуди към ревност.
12 Amma in laifinsu yana nufin albarka ga duniya, hasararsu kuma albarka ga Al’ummai, ina misalin yalwar da albarkunsu za su kawo!
А, ако тяхното отклонение значи богатство за света и тяхното отпадане
13 Ina magana da ku ne fa Al’ummai. Tun da yake ni manzo ne ga Al’ummai, ina taƙama da aikin nan nawa,
Защото на вас, които бяхте езичници, казвам, че понеже съм апостол на езичниците, аз славя моята служба,
14 da fata zan rura kabilata a ta kowace hanya su ji kishi har ma yă sa in ceci waɗansunsu.
дано по някакъв начин възбудя към ревност тия, които са моя плът, и да спася накои от тях.
15 Gama in ƙinsu da aka yi ya zama sulhu ga duniya, me karɓarsu za tă zama in ba rai daga matattu ba?
Защото, ако тяхното отхвърляне значи примирение на света, какво ще бъде приемането им, ако не оживяване от мъртвите?
16 In sashen da aka miƙa a matsayin nunan fari tsattsarka ne, to, sauran ma tsattsarka ne; in saiwar tsattsarka ce, to, sauran rassan ma tsattsarka ne.
А ако първото от тестото е свято, то и цялото засяване е свято; и ако коренът е свят, то и клоните са свети.
17 In an sassare waɗansu rassa, kai kuwa da kake kai zaitun jeji, aka ɗauke ka aka kuma yi muku aure, a yanzu kuwa kana shan ni’imar saiwar zaitun ɗin nan tare da sauran rassan,
Но, ако някои клони са били отрязани, и ти, бидейки дива маслина, си бил присаден между тях, и си станал съучастник с тях в тлъстия корен на маслината,
18 kada ka yi taƙama cewa ka fi waɗancan rassan da aka sassare. In kuwa ka yi haka, to, ka yi la’akari da wannan. Ba kai ne kake taimakon saiwar ba, saiwar ce take taimakonka.
не се хвали между клоните; но ако се хвалиш, знай, че ти не държиш корена, а коренът тебе.
19 To, kana iya cewa, “An sassare rassan ne don a ɗaura aure da ni.”
Но ще речеш: Отрязаха се клони, за да се присадя аз.
20 Haka yake. Amma an sassare su ne saboda rashin bangaskiya, kai kuma kana tsaye ta wurin bangaskiya. Kada ka yi taƙama, sai dai ka ji tsoro.
Добре, поради неверие те се отрязаха, а ти поради вяра стоиш. Не високоумствувай, но бой се.
21 Gama in har Allah bai bar rassan nan na asali ba, kai ma ba zai bar ka ba.
Защото, ако Бог не пощади естествените клони, нито тебе ще пощади.
22 Ka lura fa da alheri da kuma tsananin Allah, tsanani ga waɗanda suka fāɗi, amma alheri a gare ka, da fata za ka ci gaba cikin alherinsa. In ba haka ba, kai ma za a sare ka.
Виж, прочее, благостта и строгостта Божии; строгост към падналите, а божествена благост към тебе, ако останеш в тая благост; иначе, и ти ще бъдеш отсечен.
23 In kuwa ba su nace cikin rashin bangaskiya ba, za a sāke ɗaura aure da su, domin Allah yana iya sāke haɗa su.
Така и те, ако не останат в неверие, ще се присадят; защото Бог може пак да ги присади.
24 Kai ma da aka saro daga zaitun ɗin da asalinsa yake na jeji, aka ɗaura aure da kai a jikin zaitun ɗin na gida, saɓanin yadda aka saba, balle waɗannan rassa na asali, da za a ɗaura aure da su a jikin zaitun ɗin nan nasu na asali?
Понеже, ако ти си бил отсечен от маслина, по естество дива, и, против естеството, си бил присаден на питомна маслина, то колко повече ония, които са естествени клони, ще се присадят на своята маслина!
25 Ba na so ku kasance cikin rashin sani game da wannan asirin’yan’uwa, domin kada ku ɗaga kai. Isra’ila sun ɗanɗana sashe na taurarewa har sai da shigowar Al’ummai masu yawa ya cika.
Защото, братя, за да не се мислите за мъдри, искам да знаете тая тайна, че частично закоравяване сполетя Израиля, само докато влезе пълното число на езичниците.
26 Ta haka kuwa za a ceci dukan Isra’ila, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Mai ceto zai zo daga Sihiyona; zai kawar da rashin bin Allah daga Yaƙub.
И така целият Израил ще се спаси, както е писано:
27 Wannan kuwa shi ne alkawarina da su sa’ad da na ɗauke musu zunubansu.”
И ето завета на Мене към тях: Когато отнема греховете им"
28 Game da zancen nan na bishara kuwa, su abokan gāba ne saboda ku; amma game da zaɓen kuwa, su ƙaunatattunsa ne, albarkacin kakannin kakanninsu,
Колкото за благовестието, те са неприятели, което е за наша полза, а колкото за избора, те са въблюбени заради бащите.
29 gama kyautar Allah da kiransa ba a sokewa.
Защото даровете и призванието от Бога са неотменими.
30 Kamar yadda a dā can ku da kuke marasa biyayya ga Allah kuka sami jinƙai yanzu ta dalilin rashin biyayyarsu,
Защото както вие някога се непокорявахте (Или: Неповярвахте
31 haka su ma suka zama marasa biyayya a yanzu domin su ma su sami jinƙai ta dalilin jinƙan da Allah ya yi muku.
също така и те сега се не покоряват.
32 Gama Allah ya daure dukan mutane ga rashin biyayya don yă nuna jinƙai ga kowa. (eleēsē g1653)
Защото Бог затвори всички в непокорство, та към всички да покаже милост. (eleēsē g1653)
33 Kai, zurfin yalwar hikima da kuma sanin Allah yana nan a yalwace! Hukunce-hukuncensa kuma su fi gaban bincike, hanyoyinsa kuwa sun wuce gaban ganewa!
О колко дълбоко е богатството на премъдростта и знанието на Бога! Колко са непостижими Неговите съдби, и неизследими пътищата Му!
34 “Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji? Ko kuwa yă ba shi shawara?”
Защото, "Кой е познал ума на Господа, Или, кой Му е бил съветник?"
35 “Wa ya taɓa ba wa Allah wani abu, da Allah zai sāka masa?”
или, "Кой от по-напред Му е дал нещо, Та да му се отплати?"
36 Gama daga gare shi, ta wurinsa, da kuma saboda shi ne dukan abubuwa suka kasance. Ɗaukaka ta tabbata a gare shi har abada! Amin. (aiōn g165)
Защото всичко е от Него, чрез Него и за Него, Нему да бъде слава до векове. Амин. (aiōn g165)

< Romawa 11 >