< Romawa 10 >
1 ’Yan’uwa, abin da zuciyata take so da kuma addu’ata ga Allah saboda Isra’ilawa shi ne su sami ceto.
Braćo! Želja je srca moga i molitva Bogu za njih: da se spase.
2 Gama na shaida su a kan suna da kishi bin Allah, sai dai kishinsu ba a bisa sani ba.
Svjedočim doista za njih: imaju revnosti Božje, ali ne u pravom razumijevanju.
3 Da yake ba su san adalcin da yake fitowa daga Allah ba suka kuma nemi su kafa nasu, sai suka ƙi miƙa kai ga adalcin Allah.
Ne priznajući, doista, Božje pravednosti i tražeći uspostaviti svoju, pravednosti se Božjoj ne podložiše.
4 Kiristi shi ne ƙarshen doka domin a sami adalci wa kowane mai bangaskiya.
Jer dovršetak je Zakona Krist - na opravdanje svakomu tko vjeruje.
5 Musa ya bayyana adalcin da yake ga Doka cewa, “Mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu.”
Da, Mojsije piše o onoj pravednosti iz Zakona: Tko je vrši, naći će život u njoj.
6 Amma adalcin da yake ga bangaskiya yana cewa, “Kada ka faɗa a zuciyarka, ‘Wa zai hau sama?’” (wato, don yă sauko da Kiristi),
A pravednost iz vjere ovako veli: Nemoj reći u srcu svom: Tko će se popeti na nebo - to jest Krista svesti?
7 “ko kuwa ‘Wa zai gangara can zurfin ƙasa?’” (wato, don yă hauro da Kiristi daga matattu). (Abyssos )
Ili: Tko će sići u bezdan - to jest izvesti Krista od mrtvih? (Abyssos )
8 Amma mene ne aka ce? “Maganar tana kusa da kai; tana cikin bakinka da kuma cikin zuciyarka,” wato, maganar bangaskiyan nan da muke shela.
Nego što veli? Blizu ti je Riječ, u ustima tvojim i u srcu tvome - to jest Riječ vjere koju propovijedamo.
9 Cewa in ka furta da bakinka, “Yesu Ubangiji ne,” ka kuma gaskata a zuciyarka cewa Allah ya tā da shi daga matattu, za ka sami ceto.
Jer ako ustima ispovijedaš da je Isus Gospodin, i srcem vjeruješ da ga je Bog uskrisio od mrtvih, bit ćeš spašen.
10 Gama da zuciyarka ce kakan gaskata a kuma kuɓutar da kai, da bakinka ne kuma kake furta a kuma cece ka.
Doista, srcem vjerovati opravdava, a ustima ispovijedati spasava.
11 Kamar yadda Nassi ya ce, “Duk wanda ya gaskata da shi ba zai taɓa shan kunya ba.”
Jer veli Pismo: Tko god u nj vjeruje, neće se postidjeti.
12 Gama ba bambanci tsakanin mutumin Yahuda da mutumin Al’ummai, Ubangijin nan ɗaya shi ne Ubangijin kowa yana kuma ba da albarka a yalwace ga duk masu kira gare shi,
Nema uistinu razlike između Židova i Grka jer jedan je Gospodin sviju, bogat prema svima koji ga prizivlju.
13 gama, “Duk wanda ya kira bisa sunan Ubangiji zai sami ceto.”
Jer: Tko god prizove ime Gospodnje, bit će spašen.
14 To, ta yaya za su kira ga wanda ba su gaskata ba? Ta yaya kuma za su gaskata wanda ba su taɓa ji ba? Ta yaya kuma za su ji ba tare da wani ya yi musu wa’azi ba?
Ali kako da prizovu onoga u koga ne povjerovaše? A kako da povjeruju u onoga koga nisu čuli? Kako pak da čuju bez propovjednika?
15 Kuma ta yaya za su yi wa’azi in ba an aike su ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Isowar masu kawo labari mai daɗi abu mai kyau ne ƙwarai!”
A kako propovijedati bez poslanja? Tako je pisano: Kako li su ljupke noge onih koji donose blagovijest dobra.
16 Amma ba dukan Isra’ilawa ne suka karɓi labari mai daɗin nan ba. Gama Ishaya ya ce, “Ubangiji, wa ya gaskata saƙonmu?”
Ali nisu svi poslušali blagovijesti - evanđelja! Zaista, Izaija veli: Gospodine, tko povjerova našoj poruci?
17 Saboda haka, bangaskiya takan zo ne ta wurin jin saƙo, akan ji saƙon kuma ta wurin maganar Kiristi.
Dakle: vjera po poruci, a poruka riječju Kristovom.
18 Amma ina tambaya, “Ba su ji ba ne? Tabbatacce sun ji. “Muryarsu ta tafi ko’ina a cikin duniya, kalmominsu kuma har iyakar duniya.”
Nego pitam: Zar nisu čuli? Dapače! Po svoj zemlji razliježe se jeka, riječi njihove sve do nakraj svijeta.
19 Har wa yau, ina da tambaya. Shin, Isra’ila ba su fahimta ba ne? Da farko, Musa ya ce, “Zan sa ku yi kishin waɗanda ba al’umma ba; zan sa ku yi fushin al’ummar da ba ta da fahimta.”
Onda pitam: Zar Izrael nije shvatio? Najprije Mojsije veli: Ja ću vas na ljubomor izazvati pukom ništavnim, razdražit ću vas glupim nekim narodom.
20 Ishaya kuma ya fito gabagadi ya ce, “Waɗanda ba su neme ni ba, su suka same ni; Na bayyana kaina ga waɗanda ba su ma taɓa neman sanina ba.”
Izaija pak hrabro veli: Nađoše me koji me ne tražahu, objavih se onima koji me ne pitahu.
21 Amma game da Isra’ila ya ce, “Dukan yini na miƙa hannuwana ga mutane marasa biyayya da masu taurinkai.”
A Izraelu veli: Cio dan pružah ruku narodu nepokornom i buntovnom.